BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 24
Bangaren yaa malam kuwa ana sauke shi a kofar gidan sa baiyi wata wata ba ya nufi cikin gidansan ayanayin bacin rai da tsananin fushi wanda tsaban munin sa aransa yasa hatta kwayar idanunsa sanda suka sauya kala sukayi jaajaxur kamar anhura garwashin wuta,tafiya yakeyi gaf gaf gaf kamar wani Doki,yana haki yana huci yana kuma sauri tamkar wanda zai kifu akasa ya ci da bakin sa haka yake jefa kafafun sa,idon sa a rufe take,bai biya dakinsa ba ya wuce direct zauren rubuce rubucen sa na lakanin qur'ani daya sabayi,yana hankade kofar zauren ya fada karkashin gado ya soma fidda wasu Alluna,ruwan tawada na musammn da Wani jimmamen buzu..
Kara lekawa karkashin gadon yayi ya fidda wani abu a lullube da farin kyalle Duk kura da datti ya hau kanta,baidamu ba ya shiga kakkabewa sanda kuran ya ragu sannan ya ajiyeta agabansa,cike da nitsuwa ya yaye kyallen,wata yar madaidaiciyar akwatin gongoro ne ta bayyana agaban sa wanda aka rufe ta kirif da makullin tokos silver colour,key dinta ya dauko ya budeta atake Daga Nan Bai bata lokaci ba ya shiga barbaje abubuwan dake ciki Wani irin qur'ani ne wanda yake brownish_red in colour,anjerasu a falle falle daga Ganin sa kasan jimammen ajiyane wanda bada fasalin hafs akayi rubutun sa ba,an zayyana ayoyin ne da asalin fasalin rubutun warash,Asalin irin rubutun nan na ta da can can wayanda suka matikar kwarewa..
Daukar qur'anin yayi ya ajeshi a gefe sannan ya Kara jefa hannun sa cikin akwatin yana lalube Jim kadan ya fidda Wani sihirtaccen turare,turaren baida wani yawa Dan kwata kwata bazaifi yayi cikin kwalban fiya fiya ba,budewar sa keda wuya Wani azaban qamshi mai ratsa jini da jijiya ruhi da kwakwalwa ta mamaye wajen hartana neman bugar dashi,a kusa da qur'anin ya ajiye turaren ya Kara lalubar akwatin ya fito da Wani ferarren alkalami mai Dan uban kaifi da tsini,gefe yay dasu duka sannan ya rufe akwatin.
Acikin allunan daya fitar yasaka hannu ya dauki na karfen cikinsu wanda yake tamkar takobi,sau daya ma ya taba amfani da Ita arayuwarsa tsaban qarfin sirrinta da muhibbanta a idanun sa, itakanta tawadar ma saida ya zaba daga nan bai bata lokaci ba ya hadata da ruwan Wani magani ya Kuma jefa wancan alkalamin aciki Nan danan ta jike aciki sosai
Miqewa yay ya nufi can sashensa ya bude kofar dakinsa ya shiga ya dauko kwarya da sauran abubuwan bukata kamar ruwa da buta da wasu lakani wanda bansan su ba...
Bai dawo zauren ba sanda ya shiga bayi ya doro sabuwar alwala yanayi yana wasu irin maganganu tamkar zararre da alaman har yanzu wutar dake cin zuciyarsa bata matso kusa da mutuwa baShigarsa zauren keda wuya ya shimfida wata farar buzu ya haukai ya zaune kafafunsa a dungulme,sann ya dauki qur'anin ya shiga bubbudewa daidai Inda yakeso ya jera su falle falle, shafukan da zasuyi mai amfani kaf ya ajiyesu agaban sa
Zaman dirshan yay akan buzun Nan tare da nade hannun garensa yana wasu irin tofin da bansan kansu ba daga Nan Bai kara bata lokaci ba ya dau allon karfen nan da tawadar ya dorata akan cinyarsa ya hau rubuce rubuce Wanda Ako Wani iyakar rubutun dayakeyi saiya shaka dafin tawadar ta numfashinsa wanda yake tayashi jefa sirrin lakanin sa aciki,yanayi yanai ma wasu ayoyin wasali wasu kuma baya saka musu wasali,wasu yakan daure wasu yakan jaaa,ahakn sanda yaci kusan awa hudu yana abu daya.Kafin ya gama Gabadaya jikin sa yayi tsami ga gajiya ga azaban yunwa ga tsananin fushi da bacin rai daya wuni da shi saidai dukkan wayannan basu hanasa aikata komi ba...
Ana daf za'a kira fajr ya miqe cikin sauri ya Kara komawa bayan gidan sa alwala ya Dora sann ya dawo,rubutun dayayi a allon ya shiga wankewa yana tsilalo ruwan a Dan madaidaicin kwarya,kusan cika kwaryan yay da ruwan rubutu sannan ya ajiyeta Agefe ya nade buzun sa tsaf ya dauko dayan jimammen buxun mai brownish red colour ya shimfida ta ya haura Kai ya tsaya a tsaye kyam kamar tsohon soja tare da kwaryan a hannun sa,daf setin bakin sa ya kawo kwaryan tamkar wanda yake shirin tofa Bismillah sai ya shaisha,,lumshe idanunsa yay ya shiga ambatar wasu irin tawaludun sumbatun karatu wanda ba agane komi sai sunan zaidu daya ke tofawa harda numfashin sa acikin kwarya....
![](https://img.wattpad.com/cover/276957352-288-k381677.jpg)
ESTÁS LEYENDO
SHADE OF RUFAIDAH
Espiritual"Na rasa ni wata irin baqar mujiyace,Duk wanda yake tare Dani saiyayi Gamo da baqinciki acikin zuciyarsa. Na rasa ni wata irin mace ce da bani da albarka Sam Sam saidai ayita kuka Dani".. "life is full of negative and positive numbers but Not once h...