chapter 34

731 112 10
                                        


Part1:chapter 34

Wayannan tambayoyin su suka Dade suna rikita ma umma kwakwala suna aikin dagula mata yanayin tunanin ta shiyasa ma a kullum cikin yanayin damuwa da fargaba zaka tsince ta ko kaga ta rafka tagumi cikin Nisan tunani mai cike da kunci.

Ayanzu haka gaba daya ta rasa ta yadda zata fara tunkarar matsala guda daya acikin matsalolinta musamman ma Wanda yafi kunnowa mata kai na tsananin fushin da yaa malam ya dauka da ita., hargagin gulma da titsiyar mutane Sam bai dara ta harcan can ba,dan bata taba kai zantukan su har cikin zuciyarta ba,sumtimes in aka fada mata baqar maganan saidai ya mata zafi hartayi hawayen kunci amma daga zarar ta kwantar da Hanklinta sai taji komi ma ya wuce mata,she believe ita kadai tasan gaskiyar lamarin yarta ba mutane ba so why worry?saidai abun na mata wuyar dauka wani bin cin fuska da rainin wayo yakan shiga ciki,dan akan lamarin rufaida sosai tagane fuskokin makiyanta, saida ta kara fahimtar yanayin mutanen anguwar bana wasa ba.

Wato wasu kana zaune da su ne ana dariya ana raha amma dagata cikin zuciyarsu banda tsananin tsana da kiyayya da dumbin hassada babu abunda suke maka, arayuwa jira suke kawai suji faduwarka ransu yay sanyi da dadi,harga Allah jira suke ace musu ka mutu ace baka duniyar gaba daya sai hanklinsu ya kwanta.

Wasu sukan Iya boye tsana da hassada agabanka sununa tamakr basu tsanekan ba amma abayan idonka sune kan gaba wajen gaftare ka,duk wata kofar cigabanka suna yaqi dashi,duk wata kofar musiban daa shafeka suna murna dash, amma wasu tsantsar jahilci ke gindaya musu hakan,a gajeren tunanin su muddin qaddara yasame bawa toh gani suke kamar shiyaga dama hakan ta faru dashi.

Saidai duk da haka in qaddarar ta same su sukanfi kowa nuna son ayi musu uzuri..ko sukama dalilin da zasu lakama alhaki.

Umma duk saida ta fahimce wayannan halayyar acikin kwana biyun nan dama shi halin mutum sai Allah baka isa ka Iya ma Dan Adam ba.

Bisa dogon nazarin datayi kwkwaktan baya bata kakkarfan zugi akan aikata komi face ta  gyarota tsakaninta da yaa malam,koma yaya ne su dawo daidai dan tana matukar bukatan samun hadin kansu awannan yanayi na yaqin kubutar da rayuwar rufaida daga mummumn baki da fassarar mutanen anguwa.

Kwana biyun nan haka ta Dora dammaran tunkarar sa akan maganan
Saidai as usual bata ji ta da dadi ba,cewa yake babu ruwansa d maganan rufaida yrda ta bijire masa ta rabasa da mahaifiyar sa,babu kalar baqar maganan da umma bata amsa ba amma hakan dai tayi shiru,saida ya kammala ta nemi alfarman sa akan a sati zata na fita sau daya zuwa gidan yakumbo tana duba lpyar yarta,ahakan ma dakyar ya amince shikansa cike yake da damuwar yanayin jkin rufaida Wanda a duk sanda ya rufe idanun sa cikin nitsuwa toh sai ya hango rama da kwamusher da yarsa tayi.

Babu kalar tsine ma alai bature da bayayi a zuciyarsa amma bai taba Barin hakan ya fito karara a fili ba.

Sosai ya Tara masifa aransa yanata jiran ranan da alhj okene zai fito,already yanada labarin cewa tub ranar da aka kamasa ya gudu ya bar matayensa
,yanzu haka ita kanta suhan wahala kawai take sha dan survival of the fittest akeyo agidansa sakamakon labarin da sukajji nacewa hukuma suna farautar mijinsu akan laifin kisan kai da rufaida ta aikata.

Akan haka aka sako suhan din ita agaba da gore gore,kusan kullum sai matan alhaj okene sun sauke takaicin su akanta na cewa shegen maitar kwadayin ubanta ya jawo musu dukan ukubar da suka tsinci Kansu aciki

Ita kuwa suhan haushin yar uwanta rufaida ta somaji a xuciyarta tun abu na wasa wasa har ya soma rikida yana dawowa tsana da takaici
A duk sanda aka muzanta bata ganin laifin kowa saina rufaida,fisabillah da rufaida ta hakura kamar yadda su suka hakura suka zauna agidajen mazajensu Aida duk wayanann abubuwan basu faru ba gashi ta jawo musu abun magana badama su fito cikin mutane sai an yaba musu baqaqen maganganu.

SHADE OF RUFAIDAHWhere stories live. Discover now