chapter 50

1.8K 115 7
                                    

SHADE OF RUFAIDAH

Page 50:
Karshen Part 1.

#Barister fareesa zayd matazu residence.

Har ila yau, Rayuwa sosai ta sauyin bazata wa rufaida. wanda ya santa a satikai uku da suka shude bazai taba yarda da cewa ita din bace yanzu cikin sauki dan kuwa jinyar da akayi mata anan ya bala'in amsar tsarin garkuwan jikinta ya saka mata nitsuwa da kwanciyar hankali,ko fatar jikinta ma daya so ya yamushe dayaji isashhen kulawa, hutu,da ingantaccun Abinci tuni jikinta ya warware ya dau wani irin haske da kyalli kibane kawai batayi ba tukuna amma tun ba aje koina ba rufaida ta fara wankuwa sosai

Wani irin tsabar kyaunta na tun usuli shiya soma hargowan fallasa kansa a fili kamar wanda dama a matse yake daya fito sarari,ba aufi rufaida ta soma dawo cikin cikakkiyar  hanklinta .Dadin karawa da yanzu ta cire tunanin komi da kowa aranta ta kuma dora dammaran kai rayuwarta gaba,bayan tallafawar su anty fareesa da mijinta kai harma da yaransu,karatun novels din da sukeyi kullum shima ya balai'n taka rawa sosai wajen cire ma zuciyarta tsoron tunkarar rayuwarta na nan gaba.

Labarin novels baicika zamtowa labarin gaskiya ba, amma tabbas yana kkri wajen taimakawa phsychologyn dan adam ta hanyar uplifting din mental awareness dinsa, da consiousness dinsa game da wani rudaddiyar matsalar dake addabarsa koma na wani daban na kusa dashi,yau Hatta anty farisa saida ta komo baya tana shan mamakin irin tarin ilimin rufaida,yarinyar a mugun nitse take,kuma tana kkrin perceving knowledge dinta in a very sensible and matured manner sam sam batada ragon azanci,wanda za'a iya alakanta yiyuwar hakan,a sababin challenges din da tacikaro dasu masu nauyi da ciwo  arayuwa,bahaushe yace bazaka taba fahimtar azaban zafin kunan wuta da tukunyar girkinka yake daukawa ajikinsa ba,har sai ranan da kai kanka kafada acikin wutar ko shi tukunyar ya hantsalo ya fado ajikinka.

Tabbas Wanda yasan zafin ciwo,shiyake ma wa mai ciwo sannu..

Har iyau rufaida Bata tunanin da akwai wani mahalukin mutum a duniya wanda zai iya fitowa ya buga kirjinsa yace ya fahimce asalin abunda taji zak zak acikin zuciyarta da arayuwarta akwanakin baya.

Buts she is all putting them behind now,ynxu harji take tamkar bazata kara ta'buwa kojin wani rauni a zuciyarta ba.

Ganin alaman hakan ayanyinta shi ya karawa anty farisa karfin gwiwar cigaba da taimaka mata,tamkar ciki daya suka fito haka take daukar lamarin rufaida,aynzu duk wani rayuwa mai kyau shitake ta kkrin taga ta dorata akai, saidai duk abunda takeyi har ilayau da dar dar aranta domin kuwa tasan basu sanar da iyayensu cewa rufaida tana wajensu ba,hala yaa sheik bazai zame musu matsala in yaji hakan,da akwai harsashen cewa hj mama zata iya ta sha bakinsu, amma yaa malam fa?a kullum inta tunashi sai taji mummunan fargaba da faduwar gaba,ita kanta tasan da akwai hatsari a zaman su tare da rufaida.

G.R.A
kano state.nigeria
**
Hajiya fulani ce zaune acikin wani katafaren falonta daya hakimtu da kayan alatu yana fidda wani azaban qamshin turaren wuta na yan sudan mai dan karan qamshi da sanyi,wayarta dark maroon colour kirar iphone ta ajin karshe shine a sakale a kunnenta dayaji dan kunnen saudi gold bamai tsayi sosai ba kamar dai manne

hadadden fuskarta ta kwabe kamar karamin yarinya,tana da kyaunta na usuli dan itama asalin bafulatana ce wayayyaiya,duk da girma da tsahon shekaru fuskar nan nata a tattale yake tsaf da hadadiyar kwaliyya irinta zamani mai balain kyau da tsari,a hnkli take sake sautin muryanta wanda yake fidda amonsa kasa kasa cikin kasaitaccen yanayi tana famar narkewa dan cikinta IMAD acikin yanayin salon shagwaba da lallami yanayinta kamar bataja wani shekaru ba..

Dagata dayan bangaren kuwa shine a kwance  mashak yasha farar jallabiya yana famar wutsila kafafunshi da sukaji sabuwa fill din canvas na lanvin akan fankaccen royal bed dinshi a kasar saudi arabia.

SHADE OF RUFAIDAHWhere stories live. Discover now