chapter 18

842 179 34
                                        


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 18
Case1:she is ours

Nannauyan Ajiyar zuciya yaa sheik ya sauke tare da baje babban garen sa ayayin da yake nemawa kansa wajen zama,cikin babban cushion din dake falon ya nitse tare da jingina kansa a hnkli wani lumshe Idanun sa yay tsamm sannan ya Kara Bude su cikin maida wata sihirtacen numfashi.

Gani yay mufrad yanata daddana wayar sa da alamar layin imad din yake nema,tare da sake yar gyaran murya ya kalle sa muryan sa sounding soo unhappy yace"
.."Kabar neman layin sa, dannima har yanzu bamuyi magana dashi ba, dama nafada hakn agabansu ne Dan kawai hanklin su ya kwanta,yanzu haka kaine zaka kula da gidan Nan mufrad,nikam inaga i must have to go to Vegas yau yau insha Allahu cikin sauri mufrad ya juyo ya dube sa..
yace "pls Abbu,
kabari nizanje nariga na tura sako ma pilot dina within 10 min ma ya shirya cikin dakatar dashi yaa sheik Yace No,Lamarin Daya shafi dan uwana bana son Kuna tsoma kanku aciki For God sake da tuntuni yana Jin shawara da bazai aurar da yarsa ma
Irin wayannan muguyen mutanen ba,Yanzu wannan lamari da maiyayi kama?ace mutum shikadan sa yabi ya tayyyara rayuwar mutane harda yar da na yaya cikin sa? kasa cewa komi mufrad yay ganin yadda mahaifinsan yay maganan cikin kunan rai da tsantsar takaicin halin dan uwan san

Daga Nan Sallamar hjy jasmine ya tun karosu shigowa tayi jikinta a sanyaye ta karasa kusa da yaa sheik ta zauna cikin yanayin tagumi

Vibe dayan wayar mufrad ya somayi ya ciro a aljihun sa yana ganin sunan dayake kai sai ya Danna silent cikin sauri baice musu uffan ba ya sabule jikinshi daga wajen yayi waje, Sauke Ajiyan zuciya yaa sheik yy yana mai dubar matarsa yace Hajiya Ni zan wuce
Ta juyo cikin sauri tana kallon sa Tace "bangane zaka wuce ba ?Yace jasmine dole na inje can din,abune wanda ya shafemu gaba daya,sun tashi sun Dora imad akan case din da zai iya dawo masa matsala Nan gaba a daya bangaren kuma Dan uwana ne da yarsa victims,inaga zuwana can shizaifi min alfanu,so In akwai Wani abu da kike bukata ga dai mufrad zan barki dashi..kekanki kinsan inba an sasanta wannn lamarin ba bazan iya tunkarar mama  ayanzu ba Wani Ajiyan zuciya ta sauke tayi shiru, can cikin sanyin yanayi tace Toh shikenan,,, Allah ya baka sa'a Allah ya kare min Kai,..pls in Babu matsala kacewa imad din yanemi Ina son magana dashi mama tun jiya ta daga hanklinta akansa,kasan jiya an report din Wani aircrash mama kwana tayi fa tana kuka,kanshi ya girgiza Yace a'a ki kirata ki kwantar mata da hanklinta sannan kibar maganan magana da imad ayanzu,ku dakata mai shi zai kiraku dakansa,doc Mehra ya gaya min case din nan is very delicate,har kotu za aje dasu,so kinga kuwa dole imad sai yayi takatsantsan da irin wayoyin da zaina yi,we are talking Abt power here,bamu San ya gwamantin kasar Bulgaria zasu dauki case din ba, so u can imagine why aka nemesa tunma Kan anemo iyayen yarinya,inaga US basa son arufe case din ne Hala,so In har na isa lpya dai zakuji komi,Dan Allah a kula da ita hadizar Hjy jasmine tace ok,toh babu matsala Allah ya tsare,yace Ameen ya miqe zai wuce ta dakatar dashi cikin sauri.."tace yaa sheik dama dazu hjy goggo take magana akan wai zasu wuce abuja da yara kuma already har mufrad ya basu go ahead da mamaki a fuskan sa ya juyo yace abuja kuma?tace eh..yace hmm gaggawan me sukeyi haka,batace mai uffan ba,Dan Tsaki yay yace toh Allah ya kyauta ai sai suje din, tunda everything is set inyaso mu zamuzo daga baya,cikin sassauto da muryan ta kadan tace Toh Amma dai zaka mata bayani ko?Kasan dai hjy mama da nikaina bazamu iya tafiya acikin wannan yanayi ba Kuma kasn hjy goggo sarai da iya mita yanzu saita dau abun nan da zafi,hmm kawai yace "kiyi abunda ya dace kawai jasmine,insha Allah zan nemesu ma kafin na wuce yau kwata kwata bamu hadu ba..tace eh Aikuwa hajiya tayita mita,baka saba fita baka gaya mata ba,murmushin kawai yay baice uffan ba,a hankli tace Allah dai ya kareka muje in taka maka..Yace A'a na yafe,Ina shi mufrad din?tace Kamar waje naga yayi,Yace ok to ke saiki koma ciki kisamesu I Wil meet him on my way out Tace ok Allah ya tsare Murmushin sa mai taushi kawai ya mata sannan ya saka kansa ya fita,fitar san keda wuya yaga ko ina shiru Babu alaman mufrad a waje sai daidaikun masu aiki da masu ban ruwa can saiga driver ya leqo ta bayan mota bai tsaya amsa gaisuwar sa bama yace mufrad yay Ina?yace shugaba ban San Inda yayi ba,kallon agogon hannun sa yay agaggauce yace duba min shi yanzun nan yana gama fadan haka driver ya juya,shima  dialing number sa yashiga yi jin ance masa user busy Yasan Hala yana kusa, Bude masa motar akayi ya shiga ya zauna yay shiru a Gidan baya cikin yanayin nazari time to time yana dialing number mufrad da har yanzu ba adena cemai user busy ba,
Jikinshi ne ya basa Hala da imad din yake waya Duk dama bawai ya yarda bane cancan dan ko da sukayi waya da doc Mehra daxu bai samu ya hadasu ba

Ata bayan gidan Inda katoton swimming pool dinsu yake ya tsaya daf da bakin ruwan
Hannun sa daya na cikin aljihun sa daya na riqe da wayar dake makale a kunnen sa tun tuni bayani yakeyi.

SHADE OF RUFAIDAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora