BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 14
Lord's perfect plan.Kano state
Anguwan gangare.Ana kiraye kirayen salla ta shigo gidansu da sallama babu kowa a tsakar gidan, hijabin ta tacire ta daura kan igiya tadau butan datagani agaban wata tsohuwar rijiya tai hanyar bayi sanin tsohuwar nata Hala tana salla yasa bata kira sunanta ba ta shiga bayin tayi tsarki bata jimaba tafito ta tsugunna tai alwala tadau hijabin da Dan ledarta tayii sallama a kofa ta shiga dakinsun da babu abunda yake tashi aciki sai warin tsufa da tsamin tsamin talauci..
Agefen tsohuwar dake salla taje ta tsaya ta tada nata sallan bayan ta Sallame zama tayi tadaura kanta kan kafadar tsohuwar da ake cewa yakumbo data idar da sallanta tuntuni tana zaune,a mugun gajiye tace "wayyo Allah na yakumbo nagaji wlh, yunwa nakeji akwai abinci agidanga kuwa? dagota yakumbon tayi tace "sannu hadiza sannu kinji,fatan kin samo cikakken labari akan yayan naki?shin yaya suke ciki kinji labarin rufaidar kuwa?..atake yanayin umma hadiza ya sauya idanunta suka cikko ruwa da alaman bata ma San me zata fara cewa ba,ganin alamar data bayar yasa yakumbo tayi saurin kawar da maganan tace ke da kikejin yunwa, toh kiy maza ki tashi mana, nasaka ruwan zafi akan murhu ki dau kofi ki dama kunu ki dumama cikinki, wanka zakifarayi kokuma abincin zaki ciki?,riko hannunta umma hadiza tayi tace A'a yakumbo zandai sha kunun Amma bazan iya kara bata Wani lokaci a gidan nan ba kema kinsan halinsa ai,kuma tunda nayi masa karyan baki da lpya zanzo dubaki hklina yakasa kwanciya yanzu haka Hala yasan Inda naje karma inje gidan ne ya harxuka ya fatattako ni,...
Cikin tabe baki Yakumbo tace hadiza ba gwamma ya korokin da irin wannan zalunci ba,ace miji ya rabaka da yayanka sannan yahanaka yin magana akansu?yo Allah na tuba inbadan bashin maganin shi danaci ba har shi ya isa inbashi aurenki ne? Ai har abada malam bukar bazaici darajar samun mace kamar ki ba hadiza saidai a qaddara jahilin banza jahilin wofi
Ke Jeki ki debo kunun inkinsha saiki bani labarin yadda ake ciki da batun yara shi zaifi min,Mikewa umma hadiza tayi babu musu ta wuce waje cikin Dan karamin kitchen din falange dake tsakiyar gidan ta kutsa kai garin kunun geron su ta kamfata ta dama shi da dan kauri tasa musu zuma ta taho musu dashi daki Adan kokoSamu tayi har yakumbo ta gama kimtsa Inda sukayi sallan tana zaune abakin gadonta na Tum Tum tana kan jiranta Zama tayi ta zuzzuba musu a kofuna bayan ta kammala ta miqa ma yakumbo nata sannan itama ta xauna ta fara shan nata a hnkli wani kuuuuuru ru cikin yake bada sauti alaman abu mai dumi yana ratsa hanjin cikinta yau tun safe rabonta da abinci banda yawon neman cikakken labari akan yayanta Babu abunda takeyi
Saidai Alhamdullahi hankalinta yadan kwanta yanzu data ta jijjiyo wasu labaran saidai kokadan yanayin labarin data juyo game da zaman kangin da sukeyi din bai mata dadi ba...Musammn ma na yarta suhan da akace sau biyu mijinta yana lakada mata shegen dukka irin na kawo wuka,murja da rukkya km ma bbu magana dan labarin auren sun Sam babu Wani dadi aciki, aika ta musu a boye Dan karma akai gulman ta wajen mahaifinsu ya dawo musu bala'i dukkansu awajen sa ko ya tsine musu.
Suhan da murja dake mijinsu baiya musu kulle sukam sun samu damar mayar mata da sakon ta hanyar yar aikan da aka aiko wacce itace take kawowa hadiza rohoto akan dukkan abunda datagani da suke ciki
Rukayya kam kwata kwata mijin nata bai sake mata ba saboda shi mai arxikin dabbobi ne, daga baqon fuska ya shigo saiyahau bori yana cewa anatara masa barayi agidansan akan haka ya raba matayen sa da kowa nasu,yana da arxiki kam amma ya shaharawa wajen yin kyem kyem da abun hannun sa hakama Babu mai ci ko sha agidan sai inyaga dama,
shikam da almajirin gidan sa ma hadxa tasa aka hada baki sannan takejin halin da ruqayya take cikiDuka Yaran Sukanji matukar dadi da sanyi aransu idan akace musu ga umman su acan waje ta zo dominsu tana bibiyar lamuran rayuwar su Dan kuwa bakaramin kaicon rayuwa da tsantsar takaici suke kwasa a gidajen mazajen sun ba.
YOU ARE READING
SHADE OF RUFAIDAH
Spiritual"Na rasa ni wata irin baqar mujiyace,Duk wanda yake tare Dani saiyayi Gamo da baqinciki acikin zuciyarsa. Na rasa ni wata irin mace ce da bani da albarka Sam Sam saidai ayita kuka Dani".. "life is full of negative and positive numbers but Not once h...