chapter 25

938 168 32
                                        


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 25

Daga ta bangaren su yaa sheik kuwa tunda ya idar da sallan fajr daga masallaci sai bai dawo cikin gidan ba ya tsaya a masjid din yanata karatun qur'ani wanda Duk da kasala da kwiuwa dayake neman shigarsa ya hanasa komi bai hanasa cigaba ba da aiwatar da karatun sa ba..

Sanda yay karatun sosai sannan yadan somajin dama dama Duk dama still kanshin bai dena masa nauyi sosai,anan ma baiyi kuskuren komawa cikin gidansan ba,jikin shi yanata basa cewa in har ya shiga ciki to tabbas kwanciya kawai zaiyi,da jallabiyar sa ajikin sa ya wuce direct sashen mahaifiyar sa..

Da kyakkwan sautin Sallamar sa mai cike da nutsuwa da Kamala ya kutso kansa ciki yanamai kalamshe idanuwan sa da mamakin abunda ya tarar da Ita tanayi..
Dan Murmushin gefen baki ya saki yana mai kada kansa wato haryau hjy bazata dena basa mamaki ba

Ita kuwa tunda ta daga Ido ta kalle sa bata kara kallon ko ina ba ta cigaba da abunda takeyi har ya karaso daf da Ita ya rusuna"..kin tashi lpya mama?..lpya kalau Alhamdullhi tace tana sauke wata nannauyan Ajiyan xuciya fuskarta tamkar Babu abunda yake damunta,Allon rubutun ta data gama wankewa ta daga tayi dashi can gefe ta jinginashi da kujera,tawadar da qur'aninta Duk ta Kau da su,u can tell dat ruwan rubutun ne acikin kwanon shan dake gabanta komai zatayi dashi oho yaa sheik dai binta da Ido yakeyi
Tana Dan tofe tofen ta,Yasan yanxu haka yana tsoma mata baki acikin lamarin xatace masa yay mata shiru Dan baisan komi ba,a Kullum acikin alfahari take da ahalinta,da kuma gidan da ta fito a matsayinta na yar gidan malamai,jikar malamai wanda kusan kaf zuriar  mahaifinta da mahaifyarta malamai ne dan haka Babu Wani abun da bata iya ko ta sani gameda da malanta ba,duba da Ita kanta malamin zaure ta soma aura wanda zamanta a gidanshi kawao ya sata iya abubuwa Kuma tasan ta bambace gaskiya tsakanin malamai masuyi tsakanin su da Allah da masu saka son zuciya da asiri..
Shiyasa ma take ganin kamar a duniya babu wanda zai kaita sanin halin danta bukar dan kowa kwatankwacin halayyar sa kadan ne Babu acikin na mahaifinsa marigayi malam Amadu,.

Shiyasa tunda ya fita jiya cikin fushi ita sam hanklinta bai kwanta akansa ba,so bayan ta idda sallolintane ta fidda tsohon ajiya itama tayi yen rubuce rubucen ta da niyyar zata sha ta bawa danta zaidu yasha yauko yaki Allah saiya shi Dan yaa sheik bai yadda da irin abunsu na malantan Nan ba shidai yafi gane asibiti ko addua,Sam Sam baicika son shan Wani ruwan rubutu....

Bayan gaisawar su take cemai yakamata shima ya wuce can abuja yaga ya ake ciki dasu hajya goggo Kar suce ta ajiyeshi akan damuwar jikokinta,Murmushi kawai yay yace insha Allah zai je din,saita kafesa da Ido ganin yadda yake magana yana Dan yatsana fuska alamn kanshin har yanzu nadan damun sa yace mama ke yaushe kenan zaki taho?na dauka tare zamu wuce dake..
Tana lura dashi sosai tacce Ina zaidu,ai ku tafi can kawai inkaga nabar garin nan to komi ya daidata a rayuwar rufaida ne,Dan wayancan kam ban sansu ba..ji jikata ce damuwata...koya ma suke ciki oho?..tsaki taja cikin mita,tace awo ace mutum tsabar ya kashe xuciyarsa bazaima iya siyar Dan waya a hannun sa ana kiransa anajin abunda ke tafiya ba,zaidu ko kataba ganin hannun hadiza da wayar salula?nide ban taba Gani ba..
Kuma Duk wannan laifintane"abar bukar da jahilci amma ai shi ba matsiyaci bane..

Yaa sheik yace mama kamar tana da waya fa,cikin yar masifa ta juyo tace To daman kana sane kabarni inata kumfar baki,wayarta ta rarumo ta Mika masa tana miqewa sakamin lambarta anan,bai mata musu ba ya amsa lalubar aljihun jallabiyar sa yayi Jin ashe baifito da wayar bama yy fitar sauri gudun kar ya rasa salla atke ya maido mata wayar yanacewa mamma ki bari in nafito zan kawo miki kamar banfito da wayar ba,karban wayar tayi tana mita
O o nikam ma mairuwana da hadiza da ake min rowar lambarta
,badon jitakata rufaida bama Ina ruwana da wata hadiza,"..jingina Kai da yaa sheik yay a raunane yasata katse maganan cikin sauri tabishi da Ido Sam Sam bata fahimce yanayin sa bafa,sai tayi shiruuuu"can dai tace Kai zaidu?Wai meye haka kake narke min kamar Mai sabon ciki,ince dai ba sabon matsalar bukar ka dauko zaka yafamun ba?
Zaidu kafa kiyayeni
Kadauka ban fahimce ka bane
Anya zaidu kama runtsa jiya kuwa?
Wai Wai to ya naga idanunka sunyi Wani ciki ciki?
Ka dauko damuwar banza ka dorawa zuciyar ka..to kaima
Saika kashe kanka tunda bajina kakeyi ba,da sauri cikin dauriya yace a'a mama wallhy ba haka bane..
Tunda kince bakison maganan yaa bukar insha Allah bazan Kara kawo miki ba,ni damuwata rufaida ce,Wai naga ba lpya take dashi ba shine Nace toh ya za'ayi da Ita kenan?cike da yar hatsala Tace ohon musu,"..nide na hadata da uwarta,Kun dauka ko bansan abunda nakeyi bane?

SHADE OF RUFAIDAHTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang