chapter 35

577 94 3
                                    


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 35

Anan abuja kuwa babu abunda ya sauya game da yanayinsu a gidan saima abunda ya karu dan bakaramin gurmi su hajiya goggo suketa faman shiryawa akan rashin dawowar yaa sheik Abuja ba wanda ahalin yanxu duk sukabi suka daura ma hjy mama laifin komi sukace Ai taki dawowa abujan ne dan kawai ta rabasu da zaidu..

Wani Shakuwace taban mamaki ya kullu a tsakanin hjy saddika da hjy Adada,daga ranar da imad yazo nigeria wani sati biyun hjy saddika tayi a abujan tare dasu suna famar shagali ana kwamacala wani bin koda hajya jasmine taga wani abu da badaidai ba agidan ta gwada nuna ranta ya baci ko tana son ta tsawatar haka mahafiyarta zata mata fada ta hanata tace mata tayi shiru kartayi maganan gudun kartaje tayi baqin jini a idanun su hjya goggo..

Tsabar Iya nuna bajinta da dukiyarsun da sukeyi da qasaitar su sosai ya shige ma hjy saddiqa zuciya tanajin su har ranta tamkar wasu hamshakan basarakai, to dake ma agaban hjy saddikar kullum suke hirarrakin yadda zasuyi dealing da lamarin hajy mama shiyasa gaba daya itama tabi ta Amince dasu ta kuma saka aranta cewa ai sune da iko da rayuwar yaa sheik ba mahaifyar sa ba hjy hasiya ba,har wani dan Boyayyen kishin hajya mama dake boye a kokon ranta saida ya bayyana ma hjy jasmine wanda ya bata mamaki kwarai dagaske,sai yanxu ta gama lura da nufin mahaifiyarta,tagane cewa Bawani abu bane kawai so take ta raba yaa sheik da inuwar mahaifiyar sa hjya mama,she want her doter to rule him in all his affairs ya zamto dai kamar sun kwace ne shi gaba daya sai yadda akayi dashi.

A tunaninta zaman hjy mama tare dasu shiyake disashe ma yarta haske da karfin iko a gidan mijinta,ta dade tana boye takaicin hakan aranta saidai bata samu hanya ko hujjar dazai saka ta bayyana shi a fili ba,shiyasa zuwansu hjy goggo ya zamto mata tamkar wani nama gasashe daya fado daga sama,tunda ta gane kalar salon su tasan
Dolene ta hada kai dasu dansu yaqi mulkin da hasiya takeyi a rayuwar zaidu..

Zamansu a Abuja sam baima hajy jasmine dadi ba
Dan Banda karya Dokokin da mijinta ya shimfida a gidan sa babu abunda sukeyi,kuma ta lura kamar da sannun su suke aikta hakan aganinsu ai komi na gidan a tsarin hajy mama yake tafiya,so tsarin tarbiyan gidan gaba daya suke ta kkrin su sabunta sa da wani sabon salona daban wanda ita kanta hjy jasmin din bata amince da shi ba.

Gaba daya suka sangarta su shukra da rayuwar kyale kyale,dan karatun qur'ani da addua da aka sabayi duk dare bayan ishai yana neman ya zama tarihi,barinma shukra da gaisuwa ma ta denayin shi  a ladabce sai dan uban kinibibi da manyancen da ta dora ma rayuwanta,yaran da   fiye barinsu suna fita waje sai gashi suna yawon suu a abuja aduk sanda sukaga dama,ta dalilin munafurcin zarah shukra sukayi fada kaca kaca da malak data zargeta akan tana bibiyar imad hardace mata kamar jaka..sosai malak taji haushin wannan furucin wanda yasa ta dauke kafarta cak bata kara zuwa gidanba saidai shi imad din inyagaji sai yaje gidansu suyi hira

Sati biyu kacal mahaifyarsa tayi sannan ta koma kano aka barsu a sukadai a abuja kowa yana yadda yaga dama agaban su hjy goggo,banda imad dat was feeling soo loney sabida babu mufrad babu keeyan dazasu keeping nashi company sumtimes in bai fita ba a dakinsa kawai yake zama cikin tsananin tunani da damuwa daya dorama zuciyarsa game da lamarin rayuwar rufaida.

Ata dayan bangaren kuwa har zarah ta riga ta shige jikin both hjy Adada da hjy saddika da kinibinta,hidima akan hidima,adan dole saida suka fara sake fuska sosai da ita,kwata kwata basu gano tashar game din da zarah taketa famar bugawa akan su ba,da hjy saddika zata wuce kano har Aiport ta biyoshi suka rakata tare,tuni ta amshe lambar wayar mahaifiyar sa safiyar Allah zata kira ta mata gaisuwar safia kota cika mata acct dinta da credit koda bashin kudi zataci bai dameta ba,ita uwar sanin abunda ya dace ne,data samu shigan kuwa har wani irin iko iko take sakawwa acikin maganarta musamman akan lamarinta da imad tana kuma nuna musu kamar ma itace surkuwan su a cikin gidan gaba daya.

SHADE OF RUFAIDAHOnde histórias criam vida. Descubra agora