chaptr 13

993 145 33
                                        

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 13
Formalities...

Bangaren rufaida kuwa tunda suka jefata cikin akwatin gawan Nan jikinta ya kara sukurkucewa da tsananin zazzabi ko inanta yabi ya nakasa ya mutu bata kara iyayin Wani musulmin motsi ba, tamkar a muce haka take Jin kanta,Sauran numfashin ta dake kara diff difff a can can cikin kasar mgwaronta shine shaida gwara daya da zai nuna cewa ma tana raye

Ta dade ahakan kwarai dagske ga kishin ruwa ga yunwa Dan kuwa zata iyafin 3hrs acikin wannan yanayi sai can tukuna suka fara lekota time to time  haka akan zo a watsa mata ruwa a fuskarta inta samu ta hadiya ohon mata,sukam ma Suna hakanne sabida Kar balain warin naman kan Fatima daya babbaju akasa ya kasheta

Bayan hakan Tunda Alaji BATURE ya barsu da Ita awajen basu Wani kulata ba
Ita kuwa rufaida Duk da kasancewar halin datake ciki bai taba hana xuciyarta ambaton Allah da neman mafita agareshi ba.
Bayan kamar awa daya haka suka zo suka dauketa Duk da akwatin gawar suka kaita Wani da aka feffetsa Wani irin magani mai bugar da kwkwala suka ajeta daganan ma ta dauke bata kara gane Inda take ba.

*Kano state Nigeria*
Same day @9:45am

Da sallama sukayi Shigowar su shashen yay sheik Wajen zama ya samar musu ya miqe da sauri kamar zai fice hjy G ta tsaresa Ina zakaje kuma zaidu kaima tafiya zakayi?juyowa yy ya kalleta Dan baiyi niyyar fada mata ba yace zan kira mama ne Hala tana can sama batasan har Kun iso ba,tabe bakinta tayi batace mai uffan ba
Yy excusing dinsu ya fice sashen mahaifyarsan ya nufa Kai tsaye.

Fitarsa ke da wuya hjy adada ta kalli tsohuwar data tsime da alaman Wani abu aranta na ciccinta Tace mama meyafaru?Dan shiru tayi can ta kalle ta Murya kasa kasa tace nifa bangane komi ba,dube mu sai kace wasu bare ace babu wanda zai taho tarban mu sai zaidu?wato wajen sa muka zo shikadai kenan ko?tun jiya nake dokin zuwa inga yayan zaidu da sauran ahalin gidn nan Amma hmmmm...Wani dogon numfashi hjy adada taja tace hmm nifa bana cire ran hasiya ce ta rirrikesu kinsanta da iya tsara ma mutane rayuwarsu
Da shegen son baza mulki uwa wata yar sarki,ni tuntuni banga ma amfanin zamanta agidan zaidu ba kawai zaman saka Ido da takurawa yara,wani
Kuka Hajiya goggo ta fashe dashi kai kace an kunnata waysan ma ta riga ta rabano da yayan zaidu?koma ce musu tayi niba jinin su bane?to ai NI Nan nayi sanadiyar zuwan ubansu duniya tunda Dana dikko shiya haife uban Dan nata.
Weeeeeee weeee fet fet ta cigaba da kuka tana fyace hanci,hjya Adda ta cigaba da kallonta Dan Inda sabo ta riga ta saba da rikicewar hjya G,
"Mama meye haka so kike azo araina mu?ai tunda munzo gidan nan kowa saiya gane cewa mune da iko da zaidu ba kowa ba
Hatta uwar zaidun saita koma matsayinta

Assalamu alaikum
Wasu yan dattijiwar Sallama ne ya dakatar dasu daga bakin kofa Jin haka yasa hjy G saurin share hawayenta tana kimtsawa

Wa'alaikissalam
Shigo daga ciki hjya Adada ta Furta,Duk dama bata kalle wajen ba amma u can tell dat so take taga suwaye suka zo

Bude kofar akayi a hnkli saiga hjya jasmine wanda ta shigo tare da wata kyakkwar mace a gefenta Tasha Wani hadadden super wax blue da mayafinta babba wanda yayi matukar karamata kima da kwarjini,daga ganin ta kasan a kusan sa'ar hjy adadan take, wanda kamanin su da hjy jasmine din kawai ya isa ya sanar dakai cewa mahaifiyarta ce hjy saddiqa fulani

Murmushi ne akan fuskarta harta karaso cikin falon  banda kallon kurilla Babu abunda suke mata kasa da sama da alama yanayin ta ne yadan burgesu,cikin tsananin girmamawa hjya jasmine ta wuce gaban hjy G da hjy adada ta rusuna ta shiga gaishesu,tana tambayar lpyarsu
Sannan hjya saddiqan ta amshe gaisuwar itama ta rusuna tagaida hajya goggo sannan ta miqe zaune ta gaida Hajiya Adada cikin fara'a dakanta ta sbar dasu cewa itace mahaifiyar hiya jasmine
Jiya ta gaya mata cewa Suna hanya shine tace bari tazo dakanta tayi musu barka da isowa
Sosai hakan yay ma hjya goggo dadi aranta,sai albarka take saka ma hjy saddiqa fulani tana dada gode ma karamcinta tamkar basu suke kushe kowa daxun ba..

SHADE OF RUFAIDAHDove le storie prendono vita. Scoprilo ora