chapter 11

1K 170 35
                                    


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 11
Kingsand and queens

_Kano,nigeria._

Sanye da wata tsohuwar malum malum dinsa ya fito daga turakan sa yana famar waiwaye kamar marar gaskiya,tafiya yake a sanda kamar wanda baison aji motsin sa agidan,bai tsaya a ko ina ba sai Inda ake aje masa butarsa daukwa yay ya shiga bayan gida da sauri kafin ya fito yazo ya tarda matan sa a tsaye tayi banga banga a bakin kofar da alamar jiransa takeyi

Wani Daure fuskrsa yy tamau ayayin da yabita da Wani irin Kallo, waje y nema makansa ya zauna ya shiga zuba ruwa mai yawa a hannun sa yana kuskure bakin sa dashi yana tufarwa.
Batace cemai uffan ba harya kammala alwalan,miqewa yy tamkar bai ganta ba ya zo kamar zai wuce ta tsaresa
"Malam banfa gane maka ba..tun wancan satin nake tambayarka batun su rufaida kayimin shiru,toh tunda kace Kar in nemi su ai Kya sanar Dani halin da rufaida take ciki ko?Amma kayimin shiru gaskiya Hakan ba adalci bane malam, Tayaya zaa rabani da yayana sannan akasa min bayani akan lpyarsu ai nima inada haqqin akansu kuma haqqina ne insan halin da suke ciki

A dake ya juyo ya harereta baqin fuskn San nan aturmushe yace
"ke hadiza ki fa kiyayeni..naga rainin kin nan yana so ya zarce matsaya toh wallhy ba anan gidan ba bada ni ba...nasha gabanki yarinya..
Yo Yaya ai nawa ne
In zaki jira in baki amsa to inkuma takurani zakiyi ga fili gamai Doki saiki matse bakina in kin isa.. .
Wani wuff tayi ta karaso gaban sa
"Malam dakata min
Ta kara tsare sa ayayin dayake shirin wucewa.

Ransa ne yay matukar baci ayayi da Ita kuma ta saukar da muryanta cikin magiya da neman alfarma

"Kayiwa Allah ka dubi girman darajan sa Dana iyayenka,ka tuna tun farko nimai biyayyace agareka ban taba saba maka,Dan Allah  ka fada min yadda yata rufaida take ciki arayuwarta,iya alfarman da zakayimin kenan
Kayimin adalci malam kasan da cewa ni uwace kuma inada haqqi akanka da akansu Ina tsoron ranar da zan mutu inje gaban mahaliccina da haqqin su rufaida akaina..Shiru yay sabida yadda tayi magann acikin tsantsanr matsuwa da nuna damuwarta yanayinta na matsuwa da son sanin Inda yayabta suke ya shigesa shima har zuci.

Saidai shi sam baisan komi akan su rufaida,hasalima tunda akayi auren sau daya yaji labarinta a lokacin ma ce masa akayi jikinta babu dadi
Daga Nan bai kara samun su ko awaya ba....yadai bari akan in akwai Wani matsala ai zasu nemeshi su samar dashi,irin tunanin dayakeyi kenan akan sauran yayan sa,musamman ma dake mijin murja da ruqayya su suke ciyarda shi,mijin Jadwa da suhan kuma Suna bashi kudi Duk wata Duk sati...aganin sa zaman lpya da kaunar juna ne yake kawo haka shiyasa ma kwata kwata bai damu ba
Saidai tunda hadiza ta soma tada hanklinta tana farautar sa agidan kamar Dan bera akan batun lamarin rufaida sai shima ya kasa samun kwanciyar hankli da sukuni a zuciyarsa..

Alhaji bature bai kira sa ba haryau kuma bai kara turo masa Wani abun hasafi ko kudi ba
Shikansa wannan shirun  nasu ya damesa a zuciyarsa Amma a fili nunawa yake kamar bai damu ba..

Hawayen dake gangariwa a fuskar matar sa hadieza ya kalla,Ji yyi ransa ya kara baci ya daka mata tsawa yace wuce min agabana
Tunda ke bakiji shashar mata kawai
Nima ai na kira shi ban same sa ba anjima kadan zan nemi Alaji okene ai babban aminin sa mwaji daga garesa.
Daga Nan ya wuce ta ya fita a Gidan cikin fushi

Umma dake share hawayenta batace uffan ba bare ta motsa,wnnan karon inhar hataji labarin rufaida ba alkwari tayi makanta cewa zata fita ta nema makanta Koda Hakan zai kawo karshen zaman auren ta da yaa malam..

*******_Sunday ..7:am Attor,zayd matazu resident._

For like 30 min tana zaune abakin gadonta tanata famar tuno da daren su na jiya,tunowa da batayi sallan asubahi ba yasa ta sauko da kafafunta kasa daga kan gadon ta mike Ahankali ta rinka takawa har ta shiga toilet ta hada ruwan zafi tashige ciki a like 15 mnt tafito tayi wanka tareda wanke bakinta tafito ta dauko bathrobe dinta dat is super white ta aje kusa
hijab dogo har kasa tasa sann ta tada kabbara

SHADE OF RUFAIDAHNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ