BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 33
Kara matsowa kusa malam abduljabbar yay cikin Mamkin ganinta yace koba rufaida bace?kanta dake a can kasa ta dago ahnkli ta dan kallesa ayayin da take kkrin tare tulin ruwan hawayen dake bulbula daga cikin kwayar idanunta wanda ita kanta tasan bata isa ta tsare sa ba,cigaba da kallonta yay har saida sautin muryan ta Mai tsananin sanyi da rauni ya kufce ya fito daga can kasan tantanin makwallonta tare da sakin wata yar karaman dirin numfashin ta Mai tafe da rawa rawa,cikin yar sheshekar kukan datake kkrin danne rurinsa ta daure tace Assalamu alaikum malam katashi lpya?"Lpya" kawai.. yace ynata kallonta duk jikinsa a mugun sanyaye da yanayinta dayake lura daga Nan Wani karamin shirune ya gifta a tsakanin su,baice uffan ba itama bata kara iya ce masa komi ba,kallon yanayinta kawai ya dingayi already jikin sa ya riga ya basa rufaida ba lpya ba,ita kuwa alokcin abubuwa dayawa ne suka shiga damunta suna ruda mata tunaninta game da zuwanta datayi Nan saitanajin kamar bai Dace ma ta fito a wannn yanayin ba
Wani irin rudani ne ya gauraye fuskarta da zuciarta wanda yake kokrin kulleta mata Kai ta hanyar cunkushe mata zuciyarta da karfaffan waswasi
Tunani take aranta tana sakawa tana warwarewa"..shin A Inda mummunan labarin ta ya baza koina a anguwar su tasan dai da kyar ne in shima baiji labarin cewa tayi kisan Kai ba so What if he also choose to misunderstood her now?wajen wakenan zataje ya tallafa mata wajen taso da qarfin imaninta dayake neman gushewa?
tasan dai bazata taba iya komawa ga kawu zaidu aynzi ba,Sam bata son ta Kara jawo masa Wani matsalar da mahaifinta yaa malam,Wani irin karayar zuci ta dingaji ayayin datake wannan tunanin Wanda ya haddasa mata Jin mumuman rauni a zuciyarta Wanda bazatama iya fasalta kalar ciwon dayake tafe dashi ba,Wani irin cunkuso da ciwo ta dingaji a Kan kirjinta da zuciyarta,sai tay wani jimm Babu wani shiri sai taji hawaye zirrrrr nabin kuncinta suna saukowa har kasa bisa kumatunta hartana Jan shessheka sautin kukan nata ne yake fitowa a fili..Cikin yanayin damuwa malam Abdul jabbar ya hau rarrashinta da kalamn sa masu sanyi yana mai bata haquri yace:
"Kiyi haquri ki shigo daga ciki malama rufaida, ai Koma menene matsalar taki bai dace ki tsaya anan kina kuka ba ko?..Dan Allah kiyi haquri ki shigo ki zauna ki nitsu inbawai har kin yanke ma Allah hukunci ba ne
Jin tayi masa shiru yasa yace malama rufaida kinaji kuwa?
A Babu shiri ta gyada mai kai batare da cewa uffan ba tabi umarnin san ta shigo daga cikin masallacin tana Dan goge hawayen dake manne akan fuskarta, can nesa da shi akan tabarma ta nema waje ta zauna,tana zama ta kife kanta akan kafafunta tana famar sauke nannauyan Ajiyan zuciya..Malam dake kkrin sauraran damuwrta Bai wani jira Jin ta bakinta bama yahau mata nasiha da wa'azi masu bala'in shiga jiki da ratsa Imanin mai Imani Wanda acikin furucin san ne kadai yasa ta fahimce cewa ashe shi baima sanda labarin abunda ya afku da Ita da aketa bazawa acikin anguwar jiya ba.
Hakn ya Kara bata damar Jin zata iya fayyace masa damuwarta ta fuskar neman kofar mafita da sauki,tana hawayen ta shiga rero masa kadan daga cikin abunda ya afku da Ita bata iya boye masa komi ba sabida raunin datakeji da Kuma yarda dashi datayi ganin shi bamai saurin fassara bane tana Kuma kyautata zaton bazai tona mata asiri ba.
Malam Abdul jabbar yakasance mutum ne mai rauni da tsananin tausayi,
shima sanda ya zubda hawayen sa sosai agabanta Jin irin ukubar rayuwa da ta fuskanta a hannun mijinta Wanda har ya jawo tayi sanadiyar daukan ransa a wannan yanayiSaidai shi baiyi mamakin jin yadda tace mutanen anguwan sun juya kan maganan ba,Dan wannan din tamkar da dabiar Dan Adam ne na dindin din,wato ya aibata mummunan qaddarar Wani sannan shi yana mai kafafa da nasa laifukan.
sosai malam ya tausaya mata duba da karancin shekarunta duka duka rufaida batafi sa'ar yar kanwarsa maryam dake karkashinsa ba,tunanin yake ta yadda yarinya karama kamar rufaida zata iya dokar kalubalen dake tattare da irin wannan qaddarar shiyasa yashiga bi da kalamansa cikin hikima yana saukakawa yanamai dangata ko Wani matsalarta da ayoyin alqur'ani da kissosi na manzon Allah saw dan ma kartaji kamar da ra'ayinsa kawai yake furta mata wayannan muhimman shawarwari ko danta ji dadi...

CZYTASZ
SHADE OF RUFAIDAH
Duchowe"Na rasa ni wata irin baqar mujiyace,Duk wanda yake tare Dani saiyayi Gamo da baqinciki acikin zuciyarsa. Na rasa ni wata irin mace ce da bani da albarka Sam Sam saidai ayita kuka Dani".. "life is full of negative and positive numbers but Not once h...