BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 40
Kano state nigeria.
Dagata dayan bangaren kuwa sosai abubuwa suka dan daidaitu wa hajya mama dan bakaramin kokori Anty fareesa takeyi akan damuwan dake addabar familynsun ba.
kusan kowani sati saita kawo wa hajya mama ziyara sau uku ko fiye da haka wani binma a wajenta sukeyin weekend tare da y'ay'anta harda mijinta,haka zasu kwana suna debe ma tsohuwar kewa kwana biyun nan ma su suke ciyar da hjyr dan tuni ta sallame maman Abdul datake mata aiki badon halyyarta na son abun duniya ba saidai dan hakan yana daga cikin sabuwar tsarin datake so ta shimfida a rayuwar Ahalinta,aganinta saken da sukeyi akan tarbiyan yayan su shiyake jawowa suke shiga wasu irin matsaloli.
Dakema mijin anty reesan baya da matsalar ra'ayi ko tsanani cikin kwanciyar hnkli suke gudanar da shawarwari tsakanin su,he is just a simple cool human being daya balain sanin ciwon kanshi,rayuwarsa sam babu hayaniya
Wani bin in suna hirarsu ta rayuwa tare da hajiya bazaka taba yarda cewa shi kabilar yoruba bane dan acan ile ifen ma yataso,iyayen sa kuma haryau suna da zama a cikin garin ibadan asalin wayayyun mutane ne ma bota karamci dan haka ita bataci karo da wani marital challenge mai tsauri ba.Jajircewan anty reesa da mijinta akan batunsu rufaida da umma kawai ya isa ya kara
Ma wani dan adam din imani da karfin gwiwa wajen son taimakon su.Abinci,magani sutura duk suna aikowa Saidai fa har yau basa da ikon isaga rufaidar ido da ido sai dai subayar a matsayin sako, sakon ma basu isa su bayyana kansu ba tukuna,ko umma ma yanzu ba'a samun ganinta badon komi ba sai dan tsananin saka ido da dora mummunan kahun xuka da yaa malam ya tsiro mata dashi.
Gaba daya ya hanata sakat wani bin har dukanta yakeyi in ta matsa masa akan batun su rufaida,Daga karshe sai yace duk sanda ta kara taka kafarta a gidan yakumbo da sunan duba wata rufaida bai yafe mata ba har abadan Abada.Sosai hakan ya muzgunawa wa rayuwar umma musamman ma ayanzu da ake yawan tsangamar yarta,tasan dole ne rufaida ta bukace ta a kusa kodan ta rinka kwantar mata da hankli,da batun suhan dayake ci mata tuwo a kwarya,haryau itama yaa malam bai amshe ta ba,zama kawai take agidan mijinta amma bada auren sa akanta sabida tuni alhj okene ya aiko da sakon cewa ya sakesu har yau kuma bai bayyana agarin kano ba,wasu daga cikin matansa har sun gaji sun kama gaban su,aka bar suhan itakadai da uwar gidan sa saratu acikin agidan suna zaman dindin dan suhan ko ta fito batada wajen zuwa doka ne bata isa ta dawo gaban yaa malam ba,da axaba da dadi take zaune cikin tulin yayan Alhaj okene wanda akalla baza'a iya tantace yawansu ba tsabar yawan aure auren dayayi, wasu matansan ma da gatse suke dawowa da yaran su jibga su agidan agaban uwargidan sa hajya saratu,sai suce tunda ubansu ya gudu suma bazasu iya ciyarda su ba,hajiy saratu ita ta dau ragamar komi sauran qaddori da ababen daya rage duk ita ta handame ta siyar, daga anyi magana saita tuma tace anbarta da tulin y'ay'a dole ne ta sissiyar da abubuwan da suka rage ta ciyardasu.
A Cikin tsananin matsatsin tsangawama suhan take rayuwarta, hjy saratu bata kulata bareta sammata abinci,banda baqin cikin azaban fadace fadace da baqaqen maganganu da kishiyoyinta suka rinka jibgawa akanta suna kuma yawo da sunan ta kwarokwaro babu abunda take kwasa,
Kowa gani yake laifin ta ne tunda yar uwanta rufaida ce silar jawo musu duk jarabawar rayuwa da suka fada ciki,baqar maganan safe daban na rana daban suhan bata isa ta wuce a hanya ba..duk wayannan abubuwan da suke faruwa su sukasa ta bala'in tsanar yar uwanta rufaida.Daga cikin sauran yan uwanta wata rana haka sukan nemi suji labarin halinda rufaidar take ciki amma suhan kam pure hatred ne a zuciyrta game da rufaida ayanzu,kuma abun kullum daduwa yake.
A kullum cikin kai kuka wa Allah umma take kwana tana tsayuwar dare tana azumi tanakai kokon baranta can sama game da lamarin dukan yayanta.

YOU ARE READING
SHADE OF RUFAIDAH
Spiritual"Na rasa ni wata irin baqar mujiyace,Duk wanda yake tare Dani saiyayi Gamo da baqinciki acikin zuciyarsa. Na rasa ni wata irin mace ce da bani da albarka Sam Sam saidai ayita kuka Dani".. "life is full of negative and positive numbers but Not once h...