Page-1 Shimfiɗa

338 6 0
                                        

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

_Bismillahir rahmanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai._

*_Labarina ƙirƙirerre ne, ban kuma yarda a ɗauki ko da jumla ɗaya a canza zuwa ga wani abu ba, haƙƙin mallakata ne, dan haka a kiyaye!_*

Page 1

_*SHIMFIƊA*_

Abalah matashiya ce da ba zata gaza shekaru sha biyu(12) a duniya ba. Tun ranar da mahaifiyarta Zeenat ta haifeta sai data tsorata da tsananin kyawunta, manyan idanu, ga kuma gabaɗaya fuskarta wani kwantaccen gashi ne, Fararen idanunta masu haske ne sosai kuma suna da maiƙo, sai dai a maimakon baƙar ƙwaya sai ta zama ruwan ƙasa mai ɗan haske, hakan ya saka idanun suke tamkar na mage(Cat eyes) har kuwa da yanayin zubinsu. Sai dai abinda ya ƙara ɗagawa Zeenat hankali har ma take tunanin aljana ta haifa shi ne yanda 'yar tazo duniya babu tafin hannu(palm) babu kuma yatsu(fingers) a taƙaice daga inda ya kamata tafin hannun ya kasance sai suke a dungulmi. Taso ta wullar 'yar sai dai barazanar da magajiya tayi mata na muddin ta wullar da ita to sai ta kaita gurin 'yan sanda domin wannan yarinyar ganima ce a gurinsu, dan a cewarta za a samu sulalla da ita, dan kyawunta kaɗai ya isa ya saka ta janyo ɗumbin maza.

Da farko Zeenat ta nuna kamar ba zata amince ba, amma daga bisani sai ta haƙura ganin magajiya na neman kashe kasuwarta a bariki.

*ABLAH* shi ne sunan da ta saka wa yarinyar kamar yadda magajiya ta buƙaci a saka mata sunan da ba kowa ke da irin sa ba. sai dai sam yarinyar bata ga gata ba, domin ko ragon suna babu, sannan babu suturar kirki uwa-uba Zeenat madara ta riƙa shayar da ita a maimaikon nono, duk da tana da ruwan nono sosai dan wani lokacin kumbura suke su cika dam har su riƙa mata ciwo amma sam taƙi yarda ta bawa Ablah, dan a cewarta albarkacin magajiya take ci, sannan ko da yaushe safar hannu take saka mata irin ta jarirai dan hannun yarinyar suna matuƙar tsorata ta.

Tunda ta haifi Ablah a gidan magajiya ta tare take renonta har zuwa lokacin da ta shekara guda sannan ta yayeta ta koma ɗakinta dake gidan karuwai, yayinda ta bar Ablah yaye a hannun magajiya.

Tana cika shekara biyu Magajiya ta dawo da ita hannun mahaifiyar a cewarta ba reno tazo yi ba, dan haka tun a wannan lokacin Ablah ta fara fuskantar matsi tun bata da yawo har ma tayi yawo. Zeenat ta kan fita yawon karuwanci ta barta anan gidan 'yan tasha, haka karuwai zasu janyota suna tsokana suna dariya suna kushe halittarta musamman hannayenta da yake da safa haka zasu cire suna ihu. A lokacin Allah ya dasawa Saratu ƙaunar Ablah wadda itama anan gidan aka haifeta, ita bata taso ta san wacece uwarta ba, domin magajiya ta faɗa mata cewar uwarta na haihuwarta ta mutu, kuma ita bata san danginta ba. Saratu ce ta fara gane Ablah bata gani sosai, saboda idan karuwan na zungurinta ta kan riƙa miƙa hannu tana lalubensu tana kuka, hakan ya saka ta kaita asibiti aka rubuto mata magani.

Saratu itama kyakykyawar gaske ce kuma itace mai ƙarancin shekaru a cikin karuwan, dan lokacin Ablah na shekaru uku a duniya ita kuma a lokacin shekarunta sha takwas(18) sai dai fa idanunta sun buɗe sosai ta san maza kuma muguwar 'yar drugs ce. Ita taja Ablah a jiki, a haka kuma har suka yi sabo da Zeenat kasancewar Zeenat shekarunta ashirin(20) a lokacin, shekaru uku ta bawa Saratu.

Zeenat ta kan kawo maza suyi iskancinsu a ɗakin a gaban Ablah sai dai wani lokacin idan taga Ablah ta ƙura mata ido sai ta koreta waje ta rufe ƙofa sai ta gama da kwartonta sannan ta ce mata ta shigo.

Saratu ta kan bawa Zeenat shawara kan ta daina kawo kwartaye cikin gidan amma taƙi yarda, a cewarta sun fi buƙatar gidan, kasancewar ita Zeenat duk da tana da kyau amma kuma ba sosai take samun customers ba, sai dai duk ranar data samu wani hamshaƙin takan haɗa kuɗin da sai tayi wata biyar bata samu daga mazan dake kwana ɗakinta ba.
Ablah na shekaru biyar Saratu ta bawa Zeenat shawarar ta kaita makarantar boko da islamiyya, hakan zai ragewa yarinyar sa idon da take mata. Da farko taƙi yarda ta ce ita sa'idonta bai dameta ba, nan gaba kaɗan itama zata faɗa harkar sai da Saratu ta matsa mata sannan ta yarda ta kaita wata government school. Sai dai tun a wannan lokacin Zeenat ta gane Ablah makauniya ce, tayi tunanin a wancan lokacin da Saratu ke faɗa mata ƙarya ne, sai da aka kaita makaranta anan ta gane Ablah bata gani, dusu-dusu kawai take gani, tana ganin mutane blur, za ta gansu amma kuma bata iya tantance kamanninsu, sannan bata  iya gane mace ko namiji sai dai idan murya taji. Sai lokacin Zeenat ta ɗan ɗaga mata ƙafa kaɗan, ta gane ashe duk kwartayen da take kawowa Ablah bata ganin me take a zahiri sai dai dusu-dusu, hakan ya saka ta ƙara ɗaukar shawarar Saratu tare kuma suka kaita asibitin, sai dai jin an yanko kuɗin glasses babu na ƙasa da dubu goma(10k) ya saka Zeenat cewa a haƙura, saboda tayi jigilar sayen uniform da littattafan makaranta, amma Saratu ta ce a yanka mata guda biyu masu kyau da ɗan 15k da kuma ɗan 20k ta zaɓa mata frame sannan aka auna idon aka ce nan da kwana uku su dawo. To da wannan tubarau'n take gani wanda duk bayan shekara sai an sabanta shi.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now