*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 24
Kallonta ya sake yi sannan ya ce "Husna dan Allah ki fita a harkar matata, ki barmu mu zauna lafiya, na san ke ce kike zugata, duk abinda take ke kike ƙara assasashi, Husna ke kanki fatan da kike yi shi ne kiyi aure ki zauna a gidan mijinki lafiya amma ni a gidana kin hanani, wane wane irin rashin adalci ne?"
"Ni ban hanaka zaman lafiya da matarka ba, hasalima idan tana wasu abubuwa ni nake hanaka, ban taɓa ganin inda gyara kayanka ya zama sauke mu raba"
"Na zauna da matata mun samu fahimtar juna, kuma ta faɗa duk abubuwan da suka faru, shiyasa nazo har gidanku, ni ba zan rabaku ba, saboda tare na ganku, amma dan Allah kiyi haƙuri ki daina shiga tsakanin mata da miji"
"Ita ta faɗa maka nice?"
"Ni dai na faɗa miki, kiji tsoron Allah ki barmu mu zauna lafiya"
Yana gama faɗa ya buɗe mota, ita kuma ta matsa gefe.Yana tayar da mota tayi ƙwafa, sannan ta koma gidansu a fusace. Tana shiga bedroom ɗinta taja waya ta dannawa Hidaya kira.
Hidaya kuwa tana nan kwance kan doguwar kujera, ta rasa mene ke mata daɗi, shi take zuciyarta na mata mugun zugi. Jin ƙarar wayarta ya saka ta furgita, dan ta lula duniyar tunani, yayinda ringing ɗin wayar ne ya dawo da ita hayyacinta.
"Husna dama ina ta son kiranki"
"Dakata malama" Husna ta furta a zafafe.
"Lafiya kuwa?"
"Ban sani ba, ni za ki ciwa mutunci? Har ki aiko mijinki yazo ya wulaƙanta ni, ashe ke baki da sirri"
"Wai mene ne? Ni fa na kasa ganewa Husna"
"Ai dama ba za ki gane ba, Hidaya ni kawai ina goyon bayanki ne dan naga kina da ra'ayin karatu, amma lokacin da kike ce za ki ce Affan ya sake ki ba nice na hana ba"
"Ni fa babu wata magana da muka yi da Affan"
"Hmmm ba za ki yaudareni ki mayar dani mahaukaciya ba Hidaya, insha Allsh kuwa ni ba zan ƙara shiga wani abu naku ba, dan haka idan mijinki ya miki abu can kuje ku ƙarata"
"Wallahi Husna bamuyi maga..." Jin shiru ya sa ta duba wayar ta ga ashe ta yanke kiran. Kiranta ta cigaba dayi tana rejecting a haka har ta haƙura***** *****
Wayar tana kunnensa yana driving da hannu ɗaya. Dariya kawai ya yi kafin ya ce "Jalil ni nayi haka ne dan in gane waye ke zuga Hidaya, saboda ni na san matata ba haka take ada ba. Da nayi tunanin na saketa kamar yadda ta buƙata, sai kuma na zauna nayi tunani, naga irin son da Hidaya take min a baya tun kafin ta aureni har zuwa aurenmu, duk da mun samu saɓani sosai a lokacin da ta riƙa shan maganin hana ɗaukar ciki, amma kuma dana ce sai dai ta zaɓa ko haihuwa ko kuma saki ai haƙura tayi har aka samu Airah da kuma Aryan, ka ga kuwa ai yanzu ba za ta riƙa cewa tana so na saketa ba, dole akwai dalili"
"Kayi tunani mai kyau Affan, dama ba a son miji ya riƙa yankewa matarsa hukunci kai tsaye, ka san mata gajeran tunani ne dasu, a times abinda yazo zuciyarsu kawai suke yi sai daga baya kuma su zo suna dana sani, ka ƙara haƙuri da matarka, ka kuma nusar da ita"
"Hidaya fa ba nasiha za taji ba, zn mata dai ta inda za ta fi fahimta, dan na gano lagonta a yanzu"
"Kar dai ka haukata 'yar mutane, ka san mata da kishi"
"Ashe ka fahimci abinda zanyi"
"Eh mana, a dai raga mata, ina roƙar mata alfarma"
"Za a duba a gani"
Gabaɗaya dariya suka yi, sukayi sallama tare da katse wayar.Kai tsaye Tudun Yola ya nufa gidansu Safiyya, sun ji daɗin zuwanshi, dan ranar ne karo na farko da yaje gidan.
Sun masa tarbar mutunci, aka sa masa tabarma mai kyau a tsaftaccen tsakar gidan nasu. Ya tausaya masu yadda suke rayuwa a wannan ƙaramin gida, Maman Safiyya mai suna Binta, yaranta 6 mata sai namiji auta da ba zai gaza shekaru 13 a duniya ba. Gabaɗaya matan sun isa aure, har da ma wanda ya dace ace suna da yaransu, sai dai halin rayuwa ya saka suke zaune haka ba karatu babu aure, Safiyyar ce kawai ta samu ta aurar itama kuma gashi batayi dacen miji ba har yanzu zaune take a gida.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Fiksi SejarahƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...