*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 6
Ji tayi an makata da ƙasa har sai da ta bugu, wanda hakan ya saka ta ƙwalla ƙara, a kuma gurin ta sume.
*******
Ji tayi ana shafa mata fuska a hankali, ta buɗe idanunta da suka mata nauyi, sai dai cin karo da Ashraf yana murmusa mata hakan ba ƙaramin ƙaɗata ya yi ba.
"Masoyiyata" Ya furta, ita kuma ta miƙe a kiɗime, ta fara kallon gurin da take.
"Anan nake rayuwa a halin yanzu, bani da kowa sai ke domin ni korarre ne daga ahalina, ina so kizo mu cigaba da rayuwa tare."Girgiza kai take tana matsawa baya. "Ashraf kayi haƙuri dan Allah"
"Zeenat kin san za ki gujeni amma kika fara soyayya dani? Kin san irin azabtuwar da nayi a sanadiyyar bijerewa umarnin iyaye akan sai na auri zaɓinsu"
"Ni mutum ce kai kuma aljani dan haka aure da kai ba zai yuwu ba"
"Dole ya yuwu, saboda ke kika janyoni naji daɗin tarayya da bil'adama."
"Ban san kai aljani bane, amma da ba zan taɓa tunkararka da soyayya ba"
"Ƙarya kike" Sai da ta toshe kunne dan sautin muryar sai data karaɗe gabaɗaya dajin. Gam ta runtse idanunta lokacin da taji bugun zuciyarta ya ƙaru. Cikin kunnuwanta duk da a toshe suke da hannayenta amma hakan bai hanata jin maganarsa ba. "Na so naƙi amincewa dake amma kika dage sai mun yi soyayya, sai dana fara son ki har na samu saɓani da ahalina sannan na gano shirinku a kaina, duk da ina matuƙar ƙaunarki amma ban taɓa bibiyar ki ba, sai da kika fara bayar da jikinki ga ɗa namiji" Jin haka ya saka ta buɗe ido, ta kuma kafesu a kan shi. "Kin cuceni Zeenat, kin kuma cuci iyayenki, burin mahaifiyarki kiyi karatu mai zurfi dan ki taimakesu, amma ke kuma burinki shi ne ki zama hamshaƙiyar mai kuɗi wadda za ta riƙa fantamawa, wannan dalilin ne ya saka kika zama karuwar gida." Ta rasa bakin magana, shi kuma ya cigaba da faɗin "Dole ki shigo duniyata Zeenat, dole ki kasance dani ko kuma in mayar da ke cikakkiyar karuwa"
"Ba zan zauna da aljani kuma makashi ba, sai dai kayi duk abinda za kayi a kaina, duk da cewar nayi nadama, amma kaƙi barina, so kake ka mayar dani mahaukaciya"
"Ai tuni ma na mayar dake hakan, domin sai na rama abinda kika min, za ki zama karuwa mai tunɓele, amma kafin nan sai na kawar da ahalinki dan kar su ga abin kunya, musamman mahaifiyarki da ita zan fara, kije gida Zeenat za ki tarar da gawarta. "A'a Ash..." Iska kawai ya hura mata ta zube a gurin.Jin rana a saman kanta ya saka ta buɗe ido, abin mamaki sai ganinta tayi a bayan hostel ɗin makarantar can wani daji da ba kowa ke zuwa ba, tunowa da maganar Ashraf ya saka ta zubura ta miƙe, a gigice ta gyara hijabin dake jikinta ta fara tafiya da gudu-gudu sauri -sauri, bata bi ta cikin makaranta ba dan gudun kar a wani wanda ya santa ya ganta, tabi ta can bayan senate building ta fita, securities dai kallonta kawai suke dan bata ma masu kama da mai hankali ba. Da ƙyar ta samu napep ta masa kwatancen gidan su dake kwanar jaba. a bakin layinsu ya sauke ta tare da cewa "Ki bar kuɗin" Kawai ya wuce, dan yanayin layin ya saka shi kasa shiga, dan dama ba ko wane abin hawa ke iya shiga layin ba saboda baya da kyau sosai.
Gudu take tamkar ranta zai fita, burinta bai wuce taje gida ta hana faruwar abinda ke shirin faruwa ba, domin ta san abu ne da zai iya tarwatsa rayuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba, sai dai kuma tana ƙarasawa tayi turus taja burki a ƙofar gidansu ganin an fito da makara wanda ko shakka babu ta san gawar mutum mafi soyuwa a cikin ranta ne. A ƙasa ta zube tana gunjin kuka tare da damƙo ƙasar dake ƙasan duk da dattin dake gurin bai hanata ɗebo ƙasar ta kalla ba.
"Zeenat...!" Taji muryar ƙaninta dake bi mata, ta ɗago jajayen idanunta tana kallon sa "Ka bar nan Usama, domin na tabbatar ni ɗin a yanzu bani da maraba da gawa."Mazan da suke gurin suka fara faɗin ina matan dake gidan azo a shiga da ita. "Kar ku taɓa ni ku barni bana so" Shi ne abinda take faɗa har aka shigar da ita, kukanta ya karaɗe ko ina hakan ya saka Nabiha fitowa daga ɗakinsu ta ƙaraso inda Zeenat take "Adda..." Ta furta itama tare da zubewa a gurin ta fara kuka.
"Waye ya kashe Umma?"
Jin haka ya saka kowa yin shiru, dan dama tunda tayi wannan rotsen an fara ƙishin-ƙishin ɗin ta haukace "Ki faɗa min Nabiha" Ta furta cikin tsawa.
"Da asuba ne taje banɗaki tana fitowa santsi ya ɗauketa ta faɗi "Ashraf meyasa?" Ta furta tana hawaye. Sai kuma ta miƙe a kiɗime, da sauri wasu mata suka riƙota "Haba ke kuwa ina zakije"
"Kuna nufin zuwa za ayi a rufe Umma da ƙasa, shi kenan ba zan sake ganinta ba, ba zan bar hakan ta faru ba"
"Yi haƙuri Zeenat ki zauna, kiyi haƙuri a yanzu addu'a take buƙata kin ji" A haka dai suka lallaɓata ta zauna ta cigaba da aikin kuka.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Fiction HistoriqueƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...