*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 26
"Naga kamar ranki ya ɓaci, am very sorry please, ga niƙab ɗinki ki karɓa"
Ƙara haɗe rai tayi kuma har lokacin bata bar hawaye ba. Juyawa tayi a fusace ta wuce.
"Kiyi haƙuri dan Allah" Ya sake furtawa yana bin ta, bata tanka masa ba har suka bar gurin."Nabil tunda taƙi karɓa ka wullar mu wuce kawai meye na wani ɓata fuska har da kuka kamar wadda muka ƙwacewa mutunci"
"No ba zan yi haka ba, saboda ai nine mara gaskiya."
"To zamuyi ta bin ta ne bayan bamu san inda za ta je ba"
"Kai dai mu bita, na san in zata shiga gida ai zata karɓa ko kuma mu bawa wani ya miƙa mata."Shiru kawai ya yi ranshi a ɓace ya cigaba da bin Nabil da Ablah.
Kmar wasa kuwa sai gasu har ƙofar gidansu Ablah.
"Dan Allah karki shiga ki karɓa"
Bata tanka ba kawai ta wuce cikin gida."Hmm to taƙi karɓa yanzu ya kenan"
"Bari mu samu wani ya bayar a kai mata ko maigadi"
"Eh to ka bashi."Tana shiga Nabiha na parlour tana zaune tana kallo.
"Hmm yi magana kice an tsaneki"
"Bata tanka ba, ba kuma ta yi magana ba""Na cire mata ne a bisa kuskure kuma na bata taƙi karɓa" Nabil ya faɗa yana kallon maigadi.
"Allah sarki, ai ba zata karɓa ba dama"
"Meyasa?"
"Ai Ablah bata da hannu, shiyasa ma ƙila daka fuzge taƙi karɓa kuma take kuka"
"Bata da hannu?"
Suka faɗa gabaɗaya da mamaki kwance a fuskarsu.
"Eh wallahi dulgulmi ce, ai zai yi wuya kaga ta fita babu hijabi da wannan niƙabin"
"Ya salam" Ya furta a tashin hankali.Nabil kai yake neman kutsawa ciki, Sabir ya riƙosa. "Ina kuma zaka je? Ka bashi niƙab ɗinta ya bata mana"
"Ba zan yi hakan ba, ka matsa dalla akwai aikin da zan yi ciki"
"Wai aikin me Nabil?"
Kallon Sabir ɗin ya yi wanda sai daya tsorata ganin lokaci ɗaya idanunsa sunyi jajir, jijiyoyin jikinsa babu wacce bata bayyana ba, yanayin da bai taɓa ganin abokin nasa a ciki ba.
"Nabil are you okay?"
Bai bashi amsa ba kawai ya fincike hannunsa ya wuce"
"Anya lafiya kuwa?"
"Gaskiya da alamun ba lafiya ba, kuma ka tabbatar ba mahaukaci bane?"
"Ka kuwa san ɗan gidan waye? Ka iya bakinka"
"To nayi shiru."Yanda ya tura ƙofar sai da suka juya gabaɗaya suna kallonshi.
"Tare da namiji kika dawo gidan nan?" Nabiha ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Kallonsa Ablah tayi sannan ta kalli Nabiha."Zan ci maka mutunci sosai wallahi"
Gabanta ya ƙarasa kawai ya damƙi wuyanta. Tsorata Ablah tayi ta ɗan ja da baya tana kallonshi, yadda ya shaƙe Nabiha tamkar zai kasheta.
"Idan kika sake takurawa Ablah zan kasheki, ina ta taraki ne, dan kin ga ban miki komi ba ko? To wallahi sai na kashe ki idan bakiyi wasa ba"
"Waw...wa..way..waye kai?" Ta furta gabaɗaya idanunta sun fito."Daga yanzu dariyarta nake son gani ba kukanta ba, idan ta sake kuka to sunanki gawa"
"Waye kai? A ina ka sanni?" Ablah ta furta lokacin data ƙarasa gabanshi.
"Baki buƙatar sanina Ablah kawai dai ni inuwarki ne"
"Ka sake ta me tayi maka"
"Idan ta ƙara matsa miki wallahi sai na rabata da duniya"Sai kuma ya sake ta, ya zube a gurin baya ko motsi.
Nabiha a kujera ta zube tana mayar da numfashi, ita kuma Ablah ta ƙura masa ido tana ajiyar zuciya, gabaɗaya a tsorace take, ta kasa motsi har Sabir da maigadi suka shigo.
"Nabil meke damunka?"
Bai yi motsi ba haka ya yi ta jijjigashi amma shiru.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...