Page 35

128 8 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 35

*2 years later*

Da ido kawai take bin sa tun lokacin daya shigo har zuwa lokacin daya samu guri ya zauna. "Ina wuni" Ta furta a sanyaye tana kallonsa.
Murmushi ya yi ya ce "Lafiya lau ya kike?"
"Lafiya lau"
"An samu sauƙi ko?"
Murmushi tayi ta sauke kanta ƙasa"
"Yanzu lafiyarki lau babu inda ke maki ciwo?"
Kai kawai ta gyaɗa masa.

Shiru ya ɗan biyo baya kafin ta ce "Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ance min tsawon shekaru huɗu kaine kayi ɗawainiya akan rashin lafiyata"
"Babu damuwa"
"Amma Nabil bai zo ba? Bai kuma kira a waya ba?"
"Waye Nabil?"
"Shi ne wanda ya saka aka kawoni nan"
"Bai zo ba, babu wanda ya kira, yanzu ma abinda ya kawo ni kenan, dan so nake ki faɗa min inda kike a Nigeria sai a mayar dake ko?"
Jin haka ya saka idanunta cikowa da ƙwalla, saboda idan ta koma ma bata san waye zai karɓeta ba.
"Kin yi shiru." Ai kamar jira take kawai ta fashe da kuka. Ya shiga tashin hankali ya miƙe ya ƙarasa gabanta, ya saka hannu yana goge mata hawaye. Kan cinya ta mayar da kanta ta cigaba da kukan har sai da tayi mai isarta ta daina.

"Amma dai kin san cewa kuka ne ya jawo miki ciwon da kike fama dashi?"
Shashsheƙa kawai take har lokacin bata ɗago ba.
"A shekarunki bai kamata ace kina saka damuwa a ranki ba, idan har kina kuka ne dan Allah ya yi ki a haka kina damuwa akan hakan to ki daina, domin akwai wanda nakasar da suke da ita tafi wannan muni."
Sai lokacin ta ɗago ta kalleshi "Wallahi ban taɓa jin baƙin cikin kasancewata a haka ba, sai dai wani lokacin na kan shiga damuwa"
"akan me?"
Shiru tayi bata san lokacin da hawaye ya saukar mata ba.
"Ki faɗa min"
"Ban san wacece ni ba, ban san su waye dangina ba, ban san su waye masoyana ba, ban san yaushe ne..." Sai kuma ta fashe da kuka.
"Ki daina kukan dan Allah, domin a matsayina na Likita zan iya samuɓ matsala idan aka zo aka tarar majinyaci na kuka na kuma kasa controlling."

Bata daina kukan ba sai da ta ɗauki tsawon lokuta masu yawa sannan ta daina.
"Ablah kada kice na fiye takura miki da tambaya saboda tsananin kamar da muke ya saka nake son sanin ke ɗin wacece."
Shigowar da akayi ne ya dakatar dashi.
"Doctor Irfan kana nan kenan"
"Eh ina tare da patient ɗinmu"
Kallon Ablah ya yi ita kuwa ta shiga tsananin furgici jin sunansa, dama kuma itama taga suna ɗan kama amma ba dai taji komai ba sai da aka ambaci sunansa sannan take jin bugun zuciyarta na ƙaruwa. Shi kuwa sam bai lura ba, sai ma maganar da suke yi da ɗayan Doctor da yske tabbatar masa da a week ɗin za ayi discharging Ablah.
Sai da har suka gama ya juyo yaga taƙi ɗauke kai daga kallonsa.
"Ya dai?"
"Kai..ka..kai...ɗan Nigeria ne?"
Murmushi ya yi sannan ya ce "A'a ni ban ma taɓa zuwa Nigeria ba"
Shiru ta ɗanyi jikinta ya yi laƙwas ta ce "Allah sarki, sunanka ɗaya da mahaifina"
"Sunan shi Muhammad Irfan?"
Kai ta gyaɗa.

"Amma ya akai kika sani bayan kince min baki san danginki ba"
"Na san dangin mahaifiyata, na mahaifina ne ban sani ba"
"Idan da rabo shi ma wata rana za ki sani."
"Nagode sosai kuma Allah yasa"
"Amin ya rabbi."
"Nigeria a kano ko?"
"Eh"
"Okay, insha Allah visa ɗinki da komai zai fito a cikin week ɗin nan, da anyi discharging ɗinki sai ki tafi"
"Nagode"
"Karki damu, alƙawarin mahaifina ne taimakawa mararsa ƙarfi, amma ina so idan kin koma kiyi karatu kinji, shiyasa idan za ki tafi zan ma ƙanwata magana tunda ita ta taɓa zaman Nigeria sai ta haɗaki da wanda ta sani a saya miki form ki cike kiyi registrarion ki cigaba da karatunki kinji ko"
Kai kawai ta gyaɗa.

*_4 Days Later_*

Tana tsaye a filin jirgin, shi kuma yana gefenta tare da wanda ya haɗata dashi. Idanunta cike da hawaye take kallonsa, ya yi murmushi ya saka hannunsa ya share mata hawayen dake ƙoƙarin zubo mata.
"Kada ki kuka ki saki ranki kinji, insha Allah nayi miki alqarin indai na samu annual leave zan zo Nigeria wurin friend ɗina, kuma indai nazo zan nemeki tunda na rubuta address ɗinki, ki nutsu kiyi karatu ban da wasa ban da tunani."
Murmushin ƙarfin hali kawai  tayi, a haka har lokacin tashinsu ya yi, tana juyowa tana kallonsa yana ɗaga mata hannu a haka har suka shiga jirgin.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now