Page 40

135 7 0
                                        

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 40

Idanunta sun rufe jikinta taji ya fara shaking, bata ma san lokacin da ta kaiwa Salim damƙa ba, duk da ita mace ce amma sai da ta kaishi ƙasa. DPO da ƙarfi ya kwaɗawa ɗaya daga cikin constable kira ya shigo, da ƙyar ya janye Sabrina dan har ta kakkarce Salim a wuya, dama tashin hankali bai saka ta yanke farce kamar yadda ta saba duk juma'a, to yanzu kam sai ta kama, to ta tara farce sai gashi ya mata amfani.
Ana janyeta ta fashe da kuka, ta kasa cewa komai.

Mommy ma kukan take.
"Mommy ke kin san gaskiya na faɗa idan kuma ƙarya ne Mommy dan Allah ki musa. Taya za ki fifita bare akan 'ya'yan da kika haifa Mommy"

Cikin ɓacin rai Najma ta ce "Wai Salim mene haka? Idan da na goya maka baya to yanzu ba zan goyi bayanka ba, wannan wane irin son zuciya ne"
"Ki rufa min baki Najma ko ranki ya yi matuƙar ɓaci, da aka kawo ni nan waye yazo in ba yau ba? Sai matata ce ke da faman zuwa kuma ta sanar min har gida taje ta roƙi Mommy kn a fitar dani amma Mommy tayi burus"
"To me kake so a yi maka? Ko Salim shege ne ai ba shi ne ya halicci kansa ba,me ya maka da zaka saka ana yi masa allurar guba? Kaii!" Ta dafe goshi tare da fashewa da kuka.

Amal dai bata ko miƙe daga inda take ba, tayi mutuwar zaune kawai.

"A mayar dashi cell ina son ganin Likitin da ya riƙa yiwa Nabil allurar poison"
Ana ɗagashi ya fara faɗin  "Mommy na gode, kin fifita bare akan ɗan cikinki, gaskiya Mommy wannan bai dace ba, na tabbatar da Daddy na raye ba zai mara miki baya ba." Haka ya yi ta surutansa har aka mayar dashi.

                 **** **** *****

"Tayi masa illa sosai a jikinsa, an masa ita da yawa, zai yi wuya ya miƙe, ko da ya dawo hayyacinsa bana jin zai riƙa cikakken awa ɗaya a cikin hayyacinsa." Miƙewa Ablah tayi cikin tashin hankali ta kalli Likitan dake magana. "Ka taimaka dan Allah" Ta juya ta kalli Irfan "Abba dan Allah Nabil ya tashi dan Allah Abba" Sai kuma ta fashe da kuka.
"Baby insha Allah zai tashi, kije waje ki jirani"
"Abba ina son jin duk abinda Likita zai faɗa"
"Ka da kiyi min musu kinji, kije waje"
"Jikinta a sanyaye ta juya ta fita.

Irfan ya kalleshi ya ce "Amma baka ganin idan muka fita dashi ya samu lafiya?"
"Likitocin da za su ganshi a duk ƙasar da zaka kaishi, duk abu ɗaya zasu faɗa maka, muna da ƙwararrun Likitoci anan, wanda muke biyansu da tsoka su mana aikin da muke so, dan haka ina baka shawarar kada ka fita dashi domin ɓata kuɗinka za kayi"
"To amma ta ce min akwai lokacin da har ya ambaci sunanta kuma ya faɗa mata allurar da ake masa tamkar ana kashesa ne, shima duk ba cikin hayyacinsa bane?"
"Ta yuwu cikin hayyacinsa ne, amma gaskiya a yanzu bana jin zai iya yin awa ɗaya cikin hankalinsa, mahaukacin gaske aka so a mayar dashi, to jininsa mai ƙarfi ne shiyasa aka ɗauki tsawon lokacin abin bai gaba zama a jikinsa ba"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
"Gaskiya da an cigaba da masa allura da zai iya rasa rayuwarsa gabaɗaya, duk a yanzun ma yana cikin halin rai ko mutuwa, kayi haƙuri ina faɗa maka maganganun nan ne saboda kaima Likita ne amma da mata ne ma ba zan faɗa ba"
Numfashi Irfan ya sauke baice komai ba.
"Amma karka damu, zamu yi ƙoƙarin ceto rayuwarsa da kuma dawo dashi cikin hayyacinsa, sai dai kuma ba lallai jijiyoyin jikinsa su cigaba da aiki ba, saboda sun yi weak sosai, wasu zasu iya cigaba da aiki wanda suka taɓu kuwa gaskiya shikenan, sai dai mu yi fatan Allah yasa wanda suke kaiwa jijiya saƙon ji da gani da kuma fahimtar abu su tashi."

                    ***** *****

"Nawa aka baka? Me kayiwa Nabil?" Mommy ta faɗa tana kuka sosa.
Amal, Najma da Sabrina suma kukan suke. Sun san Mommy na kuka amma sai dai ƙwalla a idonta su ga ta saka hannu ta goge, sai gashi yau tana hawaye wani na bin wani.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now