Page 39

146 9 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 39

Idanunta a buɗe suke, ta kafeshi a guri ɗaya, duk da ba tunani take ba, tana jin bayanin da Fahad yake yiwa Irfan akan yanayin yadda ta taso. Zama ya yi a gefen sidedrawer bayan ya yiwa Fahad rakiya.
"Kina buƙatar wani abu?"
"Abba ƙarfe nawa?"
"Yanzu tara na dare"
"Abba ina son muje gidan mahaukata"
Kallon mamaki ya bita dashi, tare da faɗin "Me zamu yi acan?"
"Akwai mutumin da ba mahaukaci bane amma sun kulleshi can, Abba wallahi allurar guba suke masa"
"Ta ya kika san allurar da suke masa?"
"Mun je jiya, kuma bayan sun gama allurar sun fita na ɗauki kwalbar na karanta, sannan Abba lokacin da zan tafi ya kira sunana yana faɗin dan Allah kada na barshi anan, dalilina aka masa haka, to ni ko ba dalilina bane bana son barin shi a wannan gurin Abba, saboda yana shan wahala" Ta fashe da kuka. "Ya isa haka, zan yi magana da Fahad amma mu barwa safiya kinji"
"Shi ne ya kaini ƙasar waje aka min magani, nima ina son na ceto shi daga halin da yake"
"Zamu fitar dashi amma ki daina kukan, kin ga kema ba lafiya ne dake ba ko?"
Kai ta gyaɗa sannan ta gyara kwanciyarta, sai kuma Saratu ta faɗo mata a rai, idanunta kawai ta rufe dan ji tayi kanta na mata zafi.

_Washe Gari_

12:00pm
Baya ma iya taka ƙafarsa sai da ƙyar haka aka fito dashi daga ɗakin, shekara biyu har da wasu watanni yana zaune a guri ɗaya ai dole ma jiki ya yi ciwo, uwa-uba allurar da suke masa ko wace rana babu fashi.
"Abba dan Allah a kaishi gida ayi treating ɗinsa, tunda kai Likita ne" Ablah ta faɗa idanunta cike da hawaye.
"Ablah dole sai mun fara kaishi asibiti anyi tests ta haka ne kaɗai zamu gane abinda yake damunsa." Cewar Fahad. Kai kawai ta gyaɗa, Irfan ya shiga back seat tare dashi sannan ya ce Ablah ta shiga front seat, Fahad kuma ya jasu.
"Wane asibiti kake ganin za a kaishi?"
"Ina ganin mu kaishi private hospital wanda suke da manyan Likitocin da zasu duba shi sosai." Cewar Irfan.

Wani katafaren asibity suka je mai suna Hasad specialist hospital a kundila.
Suna zuwa kuwa tests ɗin aka fara yi kala kala kafin a bashi gado, dan wasu tests ɗin sai sun kwana sannan result ke fita. "To Baby anyi abinda kike so gashi dai an kawo shi ko, yanzu what next?"
"Abba nagode sosai Allah ya saka da alkhairi."
"Kin fi haka a gurina, amma addu'ar da kika yi amin ya Allah, yanzu dai gashi kuma koma mene da result ya fito zamu ji"
Murmushi tayi tana kallon Nabil dake kwance idanunsa a rufe, numfashinsa ma da ƙyar yake fitarwa.
"Abba yanzu shi kaɗai zamu bari anan idan dare ya yi?"
"Ba kince iyayenshi a garin nan suke ba?"
"Eh"
"To ai sai muje a sanar musu ko?"
"A'a" Ta furta tsna ɓata rai.
"To ai ya kamata ace sun sani Ablah"
"Abba akwai wani ɓoyayyen abu, domin iyayenshi ne suka kaishi gidan mahaukata, kuma ai kana jin abinda Dr ya faɗa, ana masa allurar guba kamar yadda na faɗa, suna masa saboda duk wani jijiya na jikinsa yayi weak kar ya iya wani motsi na kirki, abu na biyu kuma ƙwaƙwalwarsa lafiyarta lau, gaskiya kar a faɗa masu, a bari ya fara samun sauƙi idan ya buƙaci su zo sai a sanar musu"
"To shi kenan"

"A'a Irfan, kar fa ka biye mata mu shiga matsala, ka san dai ba wanda ya kai iyaye son 'ya'yansu, kamar dai yadda kake nuna mata ƙauna a yanzu to haka iyayensa ke nuna masa."
"Na yarda amma a bayar da kwana biyu ya farfaɗo sosai, tunda dai ba cutar dashi muke ba, kuma kai kanka ai kaga rashin gaskiya a tare dasu, ba dan ka nuna cewar zaka haɗasu da hukuma ba da ba zasu bamu shi ba"
"Haka ne, to Allah ya kiyaye"
"Amin ya rabbi."

****** *******

Wayarsa dake ta ringing Amal ta kalli Sabrina ta ce "Yaya ko meyasa yazo ya saka wayarshi a parlour gashi sai kira ake"
Taɓe baki Sabrina tayi ta juyar da kai ta cigaba da kallo.
Najma data fito daga kitchen da bowl ɗin fruits a hannunta ta kallesu. "Kuna ji ana kira ba zaku iya ɗagawa kuce bayanan ba ko ku saka ta a silent"
"Muka sani ko budurwarsa, ta fara jin haushinsa tayi tunanin 'yammatansa ne mu kuma yazo ya huce fushinsa a kanmu"

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now