*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 32
"Mommy idan har kina korarta kamar ni kike kora fa"
Da mamaki ta kalleshi ta ce "Oh kenan kana ganin matsayinka ɗaya da ita"
"Mommy haka nake ji, idan ta tafi ina zata zauna"
"To ni kuma wallahi ba zata zauna a gidana ba"
"Mommy"
"Na riga na rantse sai dai ka tafi kaima ɗin tunda haka ka zaɓa"
"Mommy korata fa kika yi?"
"Eh korarka nayi ka fita ka bar min gida indai ka dage wannan yarinyar ta zauna"
"Shi kenan" Ya furta yana kallon Ablah ya ce "Muje"
"A'a Nabil"
"Muje nace Ablah" Ya faɗa cikin tsawa, ta juyo kuwa ta kalleshi taga idanunsa sun fara canjawa aikuwa tayi saurin juyawa, ta fita da sauri, shi kuma ya yi saurin zuwa ɗakinsa.Trolley ya ja ya fara haɗa kaya, Amal ta shigo
"Wai me kake ƙoƙarin yi?"
"Tafiya"
"Zuwa ina?"
"Nima ban sani ba"
"Kar kayi haka Nabil"
"Amal ki ƙyaleni kawai"
"Wai Nabil anya kuwa kaine?"
"Bani bane" Ya furta tare da ɗaukar trolley ɗin ya kalleta ya wuce kawai.Har haki take ta faɗa ɗakin "Mommy dagaske fa yake, tsoro nake wallahi anya Nabil ne"
"Nabil ne mana, ka rabu dashi kawai tunda ya isa da kansa"
"Mommy wallahi ba Nabil bane aljanunsa ne dan Allah karya tafi wani abu ya sameshi"
"Muje" Ta furta tana miƙewa."Ba zan bari ka saɓawa iyayenka ba Nabil, kawai ka koma ni na san inda zanje"
"Ablah ba zan iya barinki ba"
"Amma..." Hango su Mommy da tayi ya saka ta yi shiru."Nabil dagaske kake za ka iya barina?"
"Mommy...!" Sai kuma ya yi shiru ya runtse ido.
"Nabil amma ka san baka da lafiya, kuma kai fa ba wani babba bane, baka mallaki hankalin kanka da za a ce ka tafi wani gurin"
"Mommy am 20 fa, ina da hankalin kaina kuma idan har ba za ki bar Ablah ta zauna tare dani ba a cikin gidan nan to dole zan bar miki gida"
"To wallahi sai ta bar gidan nan, kuma babu inda za kaje" Ta kalli inda maigadi da yaran gidan suke. Da sauri suka ƙaraso gurin.
"Ku riƙe min shi, kai kuma Hamza ka kora min yarinyar nan ta fita ta bar gidan nan"
Riƙe shi suka yi gam yana fuzge-fuzge.Tana kuka ta fita, saboda trolley ɗinta ma tana cikin motarsa, kuma ko da tana nan ma bata san ta ya ya zata iya ɗauka ba.
*** *** ***
Ɗiyarka na can a gadon asibiti bata da lafiya bta san inda kanta yake ba, amma kazo nan kana gi wa wata kuka, wadda uwarta ta yaudareka"
Hannu ya saka ya share hawayen sannan ya ce "Mama ba za ki fahimta ba, Ablah abar tausayi ce, ta kasa samun farin ciki"
"Ikon Allah to kai ne za ka sama mata farin cikin?"
"Mama dukkan arziqin da nayi ta dalilinta ne"
"Ban gane ba?"
"Lokacin dana ɗan fara samun karayar arziƙi, a lokacin ita kuma Ablah ta gama makaranta, ta samu kyautar 2M da kuma wasu ƙananun kyautukan irin 100k da award, wannan 2M ɗkn award ne aka bata kan ta cigaba da karatu a ƙasar waje, idan ta fara za su cigaba da ɗaukar nauyin karatun ta, sai dai kuma taki yarda ta cigaba ta ce in yi amfani da kuɗin a kasuwancina, nace zan juya mata ta ce a a kyauta ta bani, Mama da kuɗin ne na juya har arziƙina ya ƙaru, na gina wannan ƙaton gidan, kema na gina miki kika je hajji Mama duk a dilin kuɗinta dana saka a cikin nawa ne"
"Canfi ko? Wato kuɗinta, ta ina ya zama kuɗinta karatun ba dan kai ba za tayi bare har ta samu ilmin? Mtswww sai yanzu nake ganin ashe matarka da gaskiyarta, itama ta kasa riƙeta sai kai gwanin na iya"
Shiru ya yi bai ce komai ba, dan ya lura sam ba zata fahimce shi ba.****
Ganin mota ta tsaya a gabanta ya saka itama ta tsaya cak. Sai dai bata san waye ba, hakan ya saka tayi ƙoƙarin raɓawa ta wuce. Zuge glass ɗin motar aka yi "Ablah" Kallonta tayi, ta gane ta sai dai bata san sunanta ba, kasancewar sau biyu suka taɓa haɗuwa.
"Shigo mota mu tafi" Ta faɗa tana buɗe mata gaban motar. Shiga tayi, sannan Sabrina ta rufe, tare da juya kan motar zuwa gidansu.
"Kiyi haƙuri a bisa abinda aka miki kinji ko"
Bata ce komai ba, sai hawaye da ta cigaba da yi.
Sabrina na parker motar ta sauka, kafin ma ta buɗe tuni Ablah tayi amfani da ƙafarta ta buɗe ta fita.
![](https://img.wattpad.com/cover/351344300-288-k542301.jpg)
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Fiksi SejarahƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...