*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 42
Kallon Abiddeen tayi ta ce "Ka wuce parlour kayi wasa ina zuwa"
"Mommy in hau motana?"
"Eh amma ban da ɓanna"
"To Mommy" Da gudu yaron ya fita, ita kuma ta mayar da kallonta ga Salim dake kwance.
"Yau tsawon kwana huɗu kenan baka fita ko ina ko parlour fa baka son fita, wai mene ke faruwa?"
"Babu wani abu na faɗa miki na ƙara faɗa miki ina buƙatar kaɗaici kuma dan Allah Saudat bana son yawan tambaya" Salim ya faɗa a hasale.Mamaki take sosai yanda kwana biyu ya koyi faɗa. "Amma dai ya kamata na san damuwarka domin ina da haƙƙi akan ha..." Bata ko ƙarasa ba ya taso, tayi saurin matsawa. "Haƙƙi ko to me kike so ki sani a kaina? Ni shege ne bani da uwa bani da uba, yanzu kin ji abinda ke damuna ko? Me za ki min akai? Na san baya wuce kice ba zaki zauna da shege ba" Yana gama faɗa ya miƙe ya bar mata ɗakin, da ido kawai tabi ƙofar daya rufe da ƙarfi.
"To wai mene yake faruwa?" Ta furta tana sauke numfashi.Miƙewa tayi ta fita parlour, sai dai babu kowa sai Abidden da yake wasa abinsa shi kaɗai. "Ina Daddy yake?"
"Naga ya fita Mommy" Yaron ya faɗa yana cigaba da wasa da kayan sasanshi. Ita kuma da sauri tabi ƙofar ta fita. Lalubansa ta fara a katafaren tsakar farfajiyar gidan, dan har parking space taje amma bata ga kowa ba, taje rumfar da suke ɗan hutawa nan ma babu shi. Can bayan gidan ta zagaya inda swimming pool ɗinsu yake, a gefen pool ɗin ta hangoshi zaune ya haɗe kai da gwiwa, abinda ya bata mamaki sosai, ta san yanda Salim ke da dakakkiyar zuciya ba ƙaramin abu bane zai jefashi irin wannan damuwar, dan bata taɓa ganinsa a wannan yanayi ba, a hankali ta ƙarasa inda yake ta zauna kusa da shi, amma har ta zauna bai san ta zauna ba."Kayi haƙuri, ka kuma yi addu'a domin itace maganin ko wace irin damuwa"
Da sauri ya ɗago ya kalleta "Nan ɗin ma sai da kika biyo ni Saudat?"
"Dole na biyoka, ni matarka ce Salim, kuma haƙƙina ne in yi duk iya yina wajen ganin ya saka ka farin ciki."
Shiru ya yi baice komai ba.
"Dan Allah ka faɗa min damuwarka."Shiru ya yi yana jin ƙuna a ransa, ya kalleta ya ce "Zan faɗa miki amma ba yanzu ba, saboda a yanzu bana cikin nutsuwata"
"Shi kenan, Allah ya yaye maka ya kuma baka haƙuri da juriyar koma mene"
"Amin."**** ****
Ƙurawa ƙofar ido tayi lokacin da taji knocking. Har aka buɗe ƙofar bata bar kallon ƙofar ba. "Baby har yanzu baki bar damuwar ba"
Sauke kanta ƙasa tayi, lokacin kuma hawaye masa zafi suka zubo mata.
"Mom kuka take na rasa ya zanyi wallahi"
"Ka bata wayar"
Kan gadon ya hau ya manna mata wayar.
"Hello Bestie ya kike"
"Ina wuni" Ta faɗa ta murya a sarƙe.
"Lafiya lau, meyasa kike damuwa bayan ga Dad ɗinki a kusa dake kuma muma muna hanya"
Shiru tayi bata ce komai ba.
"Ki daina damuwa kinji, muna ƙaunarki kuma muna nan zamu zo mu ganki tunda ya ce ba zai dawo yanzu ba"
"To" Shi ne kawai abinda ta furta.Wayar ya ɗauke daga kunnenta ya kara a nashi kunnen, sannan ya fita daga ɗakin zuwa farfajiyar gidan.
"Irfan kana jina?"
"Eh Mommy"
"Meyasa ba zaku dawo nan gabaɗaya ba, tunda dai ba kowa garemu a Nigeria ba, sannan kuma mu nan ka san saboda aiki ba zamu samu mu taho da wuri ba, dole sai an bamu takardar izni daga gurin aikinmu daga ni har Diana, kai kanka ai saboda Likita ne kuma kalli yadda aka sha fama kafin a samu ka tafi"
"Mommy ai har nayi mata passport,visa ce har yanzu bata samu ba, kuma a hakan ma ta dage ita dai bata so ta tafi saboda wannan yaron dana faɗa miki da kuma wata mata da na gansu tare, Mommy har yanzu Ablah fa bata faɗa min komai na rayuwarta ba, ban san meyasa take da taurin kai ba"
"Ba taurin kai bane, ka san sai hankali zata warware bata wani saba da kai bane, kuma ga wannan matsalolin so na san idan komai ya lafa da kanta zata baka labari ba sai am matsa ba, anyi DNA test ɗin?"
"Mommy anyi, Ablah dagaske 'yata ce" Ya saka hannu ya share hawayen daya cika kurmin idonsa.
"Masha Allah, dan Allah Irfan ka kula da ita ka kuma mata duk abinda take so"
"Insha Allah Mommy"
Sallama suka yi ya sauke wayar kenan ya ga maigadi ya buɗe ƙofa. Tana shigowa ya gane itace, saboda tunda ya diro Nigeria haka yake ganinta da lulluɓin amare.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...