Page 12

95 5 0
                                        

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 12

Tana fita ƙofar gida ta sume, bata ƙara sanin inda kanta yake ba sai tashi tayi ta ganta anan ƙofar gidan karuwai, kuma bata san meyasa ta shiga ba ta kuma kama ɗaki take biyan naira 100 kullum sannan tana fita barikinta, lokacin da ciki ya ɓullo mata kuwa tasha caccaka da ihu a sannan kuma hankalinta ya dawo, ta rasa mene ya kawota wannan gida. Ta kuma tambayi garin aka tabbatar mata da mararrabar jos ne duk da dai sun ɗauki tambayar ta-ta a matsayin tambayar rainin hankali, taso komawa gida amma kuma ta rasa meyasa take kasa tafiya duk da cewar tana saka rana.

A haka tayi yunƙurin zubar da cikin saboda ya hanata rawar gaban hantsi amma magajiya ta hana, tare da yi mata gargaɗin hukuncin da za ta mata muddin ta zubar, daga nan ne ta haƙura har zuwa lokacin da ta haihu, sai dai ta shiga ruɗu da tashin hankali a lokacin da taga 'yar da ta haifa musaka ce.

Ashraf shi ya riƙa ingiza Zeenat tana ta aikata zina, domin bata so amma kuma ta kasa hana kanta, wani lokacin kuka take sosai idan tayi abin, har Ablah ta girma, anan suka kuma shaƙu da Saratu wadda Allah ya ɗorawa ƙaunar Ablah, bata ƙyanƙyaminta kamar yadda sauran 'yan gidan ke yi sannan kuma bata hantararta, duk da ita Zeenat ta kan nuna tsanarta ƙarara akan Ablah wanda sam bata san meyasa ba.

A lokacin kuma da ta fara jinya sun samu saɓani da Saratu shiyasa bata zuwa ta ganta ko ta dubata, sai Hajara ce da take ɗan leƙowa saboda ta san Zeenat ta tara abin arziƙi tana neman hanyar da zata yi ta kwashe, anan Zeenat ke bata labarin rayuwarta har ma tana roƙona da ta sada Ablah da danginta, ta rabata da gidan karuwai.

_Cigaban Labari_
  *Washe Gari*

Da sauri ta fita, ta ƙarasa bakin fanfo duk da cincirindon 'yan ɗibar ruwan wanka, gidan ya ruɗe kowa so yake ya yi wanka ya fita yawon tazubar. Ganin tana ƙoƙarin saka bucket dake hannunta ya saka Ashanty saurin dakatar da ita "Kin ga, ki bi layi kamar yanda kowa ya bi"
"Idan naƙi fa?"
"Sai nayi miki yadda za ki gane"
"Hmm" Kawai Saratu ta ce sannan ta kai robar bakin tap ɗin, a zafafe Ashanty ta buge bokitin ya faɗi ƙasa. Cikin zafin nama Saratu ta ɗago tare da sharara mata mari.

Ai tuni aka hau ihu da shewa, ita kuma Ashanty a zafafe ta yo kan Saratu suka kaure da faɗa, da ƙyar aka samu aka rabasu.
"Ashanty ba girmanki bane ki biyewa yarinyar nan"
"Dama ina da cikinta, da kun bar ni yau na kashe bakin tsanya"
"Ai wallahi ƙaryarki tasha ƙarya, kin san ko da a kai yunwa ban ci fara ba, kuma da sun bar mu ɗin na rantse da sai kin yi jinya"
Tahowa tayi mutane suka ƙara tareta tare da roƙar Saratu da ta shiga ɗaki.
"Babu inda za ni sai na ɗebi ruwa" Ta furta rai a ɓace.
Ummi ce ta ɗauki bucket ta ɗibar mata ruwan sannan ta miƙa mata, ita kuma ranta a ɓace ta wuce.

A kwance ta tarar da Ablah tana ta sauke numfashi, ta ɗauko hanky mai ɗan kauri ta riƙa tsomawa tana matsewa tare da gogawa Ablah a jiki, aikuwa tuni tsigar jikinta ta tashi, ta kuma fara karkarwar sanyi.

"Ablah dan Allah ki sakawa ranki salama ki daina damuwa, kar kina ƙanƙanuwarki wani ciwo yazo ya sameki"
"Aunty shi kenan Ammi wuta za taje?" Cikin rawar murya ta faɗa saboda zazzaɓi ne sosai a jikinta.
"Waye ya faɗa miki, kafuri ne kaɗai zai je wuta, amma idan kika cigaba da yiwa Ammi addua Allah zai yafe mata"

Haka dai tayi ta sambatu har dai Saratu ta gaji ta samo adaidaita ta kaita asibiti. Aikuwa tuni aka basu gado, sannan aka jona mata drip.
Saratu ido ta ƙura mata "Ablah ga ki nan kyau kamar 'yar india, tamkar ma ke aka bawa damar halittar kanki sai kuma kika samu tawaya a hannu da ido da kuma asali" Ajiyar zuciya ta sauke.
"Allah ya baki lafiya..." Bata ma ƙarasa dire maganar ba kira ya shigo mata.
"Magajiya!" Ta furta tare da ɗaga wayar.
"Hello! Uwar ko wane shege" Shi ne abinda Saratu ke kiranta dashi.
Daga ɗayan ɓangaren Magajiya tayi shewa "Hajiya Sarah uwar naira, kowa ya taɓaki bai so zaman lafiya ba, idan ko ana son ɓirɓishin naira to ayi miki biyayya"
Murmushi tayi tana faɗin "Magajiya kenan"
"Uhumm naji ance kin ɗauki waccan musakar ina kika kaita?"
"Ni bani tare da musaka, gaskiya Magajiya zamu iya samun matsala kina kiranta da wannan suna"
"Eyeee! Wani sabon bariki za ki min"
"Ba wani bariki, gaskiya na faɗa miki"
"To naji yanzu dai kuna ina?"
"Kin san dai ban fara sayar da mutane ba bare kice na ɗauketa na sayar ne"
"Ni ban faɗa ba, kin dai san yarinyar nan kadarata ce shiyasa ban so tayi nesa da gidan dandi"
"Magajiya uwar harka, kar ki damu ai zan ɗauko ta na kawo ta gidanki ma, tunda naga kwana biyu kin tafi can kisha iska, kin san zan je Abuja nayi sati tare da Babe ɗina, to zan kawo miki ita"
"To ina nan ina jiran ki kawo ta" Ƙitt ta kashe wayar, Saratu tayi murmushi tana zama gefen gadon, ta kai hannu ta taɓa jikin Ablah taji zazzabin ya sauka.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now