*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 41
Suna ƙarasowa Irfan ya riƙota tare da faɗin "Babu komai ba abinda za su miki ki kwantar da hankalinki." Ta gyaɗa kai tana kallonshi, su kuma gaba ɗaya suka wuce bakin ƙofar sai ta glass ɗin ƙofar da taga suka riƙa hangoshi.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai suka ji an faɗa, suna juyawa suka ga Mommy ta suma. Subhanallahi. Irfan ya faɗa yana ƙoƙarin kiran Likita.
_*2 Days Later*_
Suna zaune gabaɗaya a parlour har da mahaifin Manal wanda ya kasance shi ne babba a gidansu Daddy Alhaji Bashir da kuma ƙaninsa Alhaji Jamil.
Parlour ya yi tsit dan taro ne da Mommy ta haɗa dan ta warware abubuwan da suke faruwa.
"Gaskiya sam ba'a kyauta mana, saboda baya raye sai kuma kiyi ta abubuwa ba tare da saninmu ba, yaran nan fa 'ya'yanmu ne kuma su ɗin amana ce a garemu, mun barki ki riƙesu ne kawai ganin kin shaƙu dasu kuma bai kamata mu tauye miki ba ta hanyar rabaki sasu. Bamu zama masu munana miki ba, amma bamuyi tsammanin haka daga gareki ba" Cewar Alhaji Bashir.
Mommy ta saka hanky ta sake goge hawayen idonta.Alhaji Jamil ya ɗora da faɗin "A gaskiya nima nayi mamaki da bata kira ko waya ta sanar damu dukkanin abubuwan dake faruwa ba, duk da dai tana iya bakin ƙoƙarinta akan yaran, to sai dai muma fa da laifinmu dan tun farko ya kamata ace mun riƙa bibiyarsu lokaci-lokaci."
"Wannan gaskiya ne, yanayin aikinmu shi ya ƙara jan komai, kuma muna ganin ga Salim da yake babba har da 'ya'ya sai nake ganin ai shi zai zama alhaki na kula da 'yan uwanshi amma tabbas mun yi ganganci."
Sai lokacin Mommy ta ce "Kuyi haƙuri, naso gyara matsalar ne da kaina, sai dai kuma abinda Salim ya zo dashi ne mai girma, wanda har ya saka na kasa saka baki nace sai kunzo, dan a gabanku aka yi komai lokacin mahaifinsu na gadon asibiti"
"Wannan gaskiya ne, dan na naɗi muryarsa ma saboda irin wannan rana"Salim, Najma, Amal, Sabrina duk suna zaune a ƙasa babu wanda ya iya cewa komai tunda aka fara maganar.
"Kai Salim"
Jin an kira sunansa ya amsa sannan ya ɗago yana kallon Alhaji Jamil.
"To sai dai kayi haƙuri da abinda zaka ji daga garemu, abu ne da babu wanda ya sani sai yanzu"Parlourn ya ƙara yin tsit babu motsin kowa sai numfashi.
Alhaji Jamil ya cigaba da faɗin "Wannan mata" Ya nuna masa Mommƴy, sannan ya cigaba da faɗin "Ka gode mata, domin ta maka komai a rayuwa, ta maka abinda har abada ba zaka taɓa iya rama mata ba"
Kan shi ya saune ƙasa, shi kuma Alhaji Jamil ya ce "Bayan shekaru uku da aurensu sai suka damu akan haihuwa, domin daga ita har shi mutane ne masu matuƙar son 'ya'ya, dalili kenan daya saka suka fara zuwa AKTH ana dubasu suna kuma karɓar magani duk wata. Wata rana sunje sai ake ta labarin wata mata sa miji da yarinya ɗaya da suka rasu a cikin mota, ance poison ne suka ci, sai dai ba a sani ba ci suka yi da kansu ko kuma basu akayi amma dai akan babban titi sukayi hatsari, gawarsu bata yi komai ba sai dai bincikdn ne ya nuna sunci gaba, dukkansu sun mutu sai wani yaro guda ɗaya wanda ya kasance jariri ne da bai fi watanni biyar ba. Jin haka ya sa Alhaji ya buƙaci ganin yaron kuma ya roƙi alfarmar riƙewa kafin a samu 'yan uwanshi. Aka yi rubutu a asibiti da kuma headquater ta 'yan sanda, sannan aka damƙa yaron gareshi, sai dai har aka shekara babu wani nasu daya zo, dan daga baya ma sai sallah aka musu anan asibitin aka binnesu, shi kuma ganin yadda yake kula da yaron ya saka aka ce ance an bar masa halak malak"Shiru ne ya biyo baya kafin Alhaji Jamil ya ce "Ka san yaron?"
Kai ya girgiza alamar a'a"
"To kaine"
Wata irin zabura ya yi.
"Ka ga nutsu, dalili ne ko ince dole ce ta saka muke faɗa maka wannan."
Fashewa ya yi da kuka mara sauti.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...