*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]__I dedicate this page to all RAINA FANSA Fans #ILYSM❤🩹🌸_
Page 18
Tana rufo ƙofa ta ci karo da Khairiyya.
"Manya maganin ƙanana daga nan kuma sai ina?"
"Yawon nema mana, kin san ai sana'ar tamu ba ta zama bace ba"
"Gaskiya ne kam, yawwa dama ina so muyi magana fa?"
"Wace magana? Dan wallahi sauri nake.
"Kan Magajiya uwar dandi mana, ai wallahi naji daɗi da kika mata haka, dan gabaɗaya ta addabi rayuwarmu."
"Kin ga faɗa na tsakanina da Magajiya wannan bata shafi kowa ba, dan Allah abar maganar"
Taɓe baki Khairiyya tayi tare da faɗin "Shi kenan an bari."Murmushi Saratu tayi tare da faɗin ni zan fita"
"Sai kin dawo"
"Aha."Tana fita ta fara duban inda za ta hango motar, can kuwa ta hangota daga gefe wajen ma babu haske sosai, sannan ba kusa da gidan ya yi parking ba.
Murmushi tayi tana girgiza kai, ta nufi motar kai tsaye. Tana zuwa ta saka hannu jikin glass ɗin motar tayi knocking, a hankali ya fara sauke glass ɗin, da nose mask a fuskarsa dan haka bata ganeshi ba sai jin sassanyar ruwa tayi an watso mata a fuska, ta dai san ba shi ne ba, dan taga hannun daga bayan mota, sai dai ba za ta iya tantance hannun mace ne ko namiji.Sanyin ne ya fara ratsata kafin taji wani azababben zafi, a take kuwa ta ƙwalla ƙara da iya ƙarfinta, kafin ta sume a gurin, su kuma tuni suka ja motar dan sun tabbatar attention ɗin mutane zai dawo kansu.
**** **** ****
Kallota ya tsaya yi, lokacin data kama ƙugu ta kuma tsaya gabanshi.
"Malama kin san dai bana so a tsaya min aka ko?"
"To tunda ka san da haka sai kayi abinda ya dace"
"Indai saki kike buƙata Hidaya to ba zan sakeki ba, kuma karatu ne ban amince kiyi ba."
"To aikuwa wallahi baka so zaman lafiya a gidan ka ba, rashin mutunci kuwa na dinga yi maka har sai ka bani takarda ta."Ɗan cije lips kawai ya yi, ya miƙe ya bar mata gidan gabaɗaya. Kallon ƙofar parlourn kawai take, kafin ta ɗauki wayarta a kufule ta zauna a kujera gami da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.
"Husna wallahi zan yiwa Affan abinda bai taɓa zato ba"
"Ƙawata ki bi komai a sannu, ba a gaggawa a abinda ake nema, kar fa kije garin neman gira ki rasa ido"
"Wane ido zan rasa? Ni fa gabaɗaya na gaji da zama da Affan, haba Husna kefa gaki nan har kin gama Masters da ƙananun shekarunki, nima da ace ban yi aure ba ai da tuni na ɗora da pHd, amma gabaɗaya aure ya durƙusar dani, haba!"
"Ni dai ina goyon bayanki ne dan naga kina so, amma kuma bana goyon bayan ki kashe aure Hidaya, domin ba lallai ki samu miji kamar Affan ba"
"Inji wa? To wallahi ni na san sai na samu duk irin mijin da nake so idan har da kuɗina kuma da ilmi na"
"Akwai fa abubuwan da kuɗi basu bada shi Hidaya, ki dai yi tunani"
"Ni bani da wani tunani daya wuce cikar burina a yanzu."
"To sai ki ƙara hura masa wuta amma dai kar kiyi abinda za a sakeki dan Allah."
"Shi kenan, amma wallahi ni tuni na gaji da zama dashi"
"Ki dai ƙara haƙuri"
"Shi kenan, ya su Mommy?"
"Sai yanzu kika tuna dasu?"
"Ba za ki gane ba, raina ne a matuƙar ɓace"
Dariya Husna tayi.Ɓangaren Affan kuwa yana driving amma ji yake ransa a matuƙar jagule. Wayarsa ya janyo ya kira amininsa Jalil.
"Affan ya dai?"
"Lafiya lau Jalil kana ina ne?"
"Ina gida, ka san yau weekend"
"Haka ne, bari nazo gidan na sameka"
"Amma lafiya? Na ji yanayin naka seems like kana da damuwa"
"Sai nazo dai za kaji komai Jalil"
"Alright sai kazo"
Wayar ya ajje ya cigaba da driving, sai kawai Ablah ta faɗo masa a rai.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...