*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 9
Murmushi ya yi wanda ita kanta ta kasa gane ma'anar hakan "Ban miki dan ki bani wani abu babba ba, da farko dai nayi miki ne dan Allah, domin in dai ina da hanyar taimakon mutum zan iya taimaka masa kamar dai yadda nayi miki a yanzu; abu ɗaya dai nake neman alfarmar shi a gurinki" Ya tsagaita da magana, ita kuma da mamaki ta bisa dan jiran abinda zai faɗa, jin shirun ya saka ta ce "Wane abu?"
"Zuciyarki!" Yanda ya faɗi kalmar zuciyar ma sai taji dumm, tayi sanyi kuma ta rasa amsar da zata bashi.
"Zeenat ba zan miki dole kan ki soni ba, amma tun lokacin da idona ya yi tozali da naki naji wani abu a kanki ban kuma tabbatar da soyyayya bace sai a yanzu"Shiru tayi tamkar wadda ruwa ya shanye, wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan yunwa, tabbas Irfan shi ne irin mazan da ta daɗe tana son haɗuwa dasu, sai dai duk wanda ta haɗu dasu amfani kawai suke da ita amma a yau ta samu mai son aurenta bayan kuma ga Mustapha can ya tafi domin ta.
"Baki ce komai ba" Ya katse mata tunanin.
Har ta motsa baki da niyyar yin magana ya ce "Zan baki lokaci kiyi shawara, domin bana so ki yankewa rayuwarki hukuncin da bai dace da ita ba"Murmushin ƙarfin hali kawai tayi lokacin da ya ce zai tafi kuma yana biɗar lambar wayarta.
"Bani da waya"
Kallon mamaki ya riƙa bin ta dashi kafin daga bisani ya ce "Insha Allah anjima zamu zo tare da Diana, kuma zan kawo miki waya dake da Sister ɗinki"
"A'a, hakan ma mun gode, kar ka ɗorawa kanka wani nauyin"
"Dan na kyautata miki ai ina ganin ba wani abu bane, domin kece mafarkina wanda nake fatan ya zama gaske"
Wata ajiyar zuciya ta sauke, wadda har sai data fito fili.**** **** *****
"Dama ni na san ba banza ba, amma sai dai yazo a ƙurarren lokaci" Cewar Nabiha, lokacin tana gyarawa Baba kwanciya.
"Ban gane yazo a ƙurerren lokaci ba?"
"Ina nufin Mustapha ya riga ya karɓi ragamar"Ajiyar zuciya Zeenat ta sauke tare da faɗin "Amma fa irin wannan shi ne mafarkina Nabiha"
Kallonta Nabiha take kamar tana karantarta, kafin ta ce "Ya zo a lokacin da bai dace ba Adda, Mustapha ya tafi ne domin lafiyarki, kin ga kuwa babu yanda za ai ki fara soyayya da wani."
Kawai tsintar kanta tayi a jin haushin furucin Nabiha duk da kuwa ta san cewa gaskiya take faɗa, domin daga abokan Mustapha har 'yan uwa ba wanda ke son alaqarshi da ita, amma shi ya jure ya kuma bada ranshi ko ya mutu ko ya rayu kan lafiyarta.**** *** ****
"Wai ita waccan da ta fita mene alaqarku? Dan naga kina fuzgen kama da ita"
Rafi'a ta taɓe baki tare da faɗin "Ɗiyar ƙanin Dad ce, sai shegen naci, Babansu ɗan caca ne fa, kuma wai yanzu daya kwanta magashiyan shi ne suka zo neman taimako, kin san talakawan da suke da 'yan uwa masu kuɗi"
"Ai ina ganin ba wani abu bane, domin Allah yana bawa wasu kuɗi ne ya talauta wasu domin jarabawa, masu kuɗi su taimaki talaka shi ne cin jarabawarsu mararsa kuɗi kuma su yi tawakkali da kuma yarda kan cewa Allah ne ya jarrabesu da talauci ba wai dan baya son su ba face dan gwada imaninsu."
"Kin ga nifa ba wa'azi nace kiyi min ba, amma babu yadda za ai mutum ya sha wahalar tara kuɗi kuma wani na can na zaman kashe wando sai ya dauka ya bashi, Diana kiyi tunani mana"
"Ɗan uwa daban yake Rafy"
"Kin ga ya kamata muyi mu fita, saboda we have alot to cover, ga kuma time yana tafiya" Rafi'a tayi saurin kawar da maganar tana janyo veil ɗinta.
"Kamar naji kince Sweetyna ne ya kawo ki ko?"
"Yes ya yi dropping ɗina ya wuce"
Ɗan turo baki tayi kafin ta ce "Amma ko ki kirani mu gaisa"
"Apologise to me ƙawata, yana sauri shiyasa ban kiraki ba, kema ai kin san bama haka, baki ji nace zan je na ɗauko wayana a motar shi ba"

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...