*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 36
"Kina nufin Zeenat ta rasu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta tare da dafe kai.
"Zeenat ta rasu ban nemi yafiyarta ba, wa'iyazubillah"Tsaki kawai Nabiha tayi sannan ta ce "Ashe tun a lokacin ka san komai amma shi ne ka ɓoye, to ga ɗiyar Zeenat nan, ka mayar da ita gurin dangin ubanta su riƙe ni ba zan iya ba"
"Dakata Malama" Ya dakatar da ita yana kallonta rai a ɓace. "Yarinyar nan da kike gani a yanzu haka daga gurin mahaifinta take, kuma idan kinji gatan da ya ce ayi mata sai kin yi mamaka a hakan ma bai san ita ɗin 'yarshi bace ina ga ya sani, zan mayar da ita kamar yadda kika buƙata, amma ni baki isa ina tsaye kina faɗa min maganganu son ranki ba, baki da wannan arziƙin, kuma kinyi asara wallahi, jininku ɗaya da Zeenat uwa ɗaya uba ɗaya amma kike ƙin abinda ta haifa kuma na san ba zai wuce saboda tawayarta ba, da naki ɗan ne fa? Wallahi wannan abin kunya ne, kuma kai kana mijinta amma ka kasa nuna mata muhimmancin ɗan uwa, ko dan a baya ba zan manta ba a gaban surukan Zeenat kika riƙa cewa cikin shege ne dama ita karuwar gida ce, ko za ki tona asirinta ba a gaban iyayen mijinta ba, amma da yake baki da kishin ɗan uwa ko kuma kina mata ɓaƙin cikin ta auri mai kuɗi, ashe dai abin bai tsaya kan Zeenat ba, har jininta ba za ki iya riƙewa ba saboda bata raye, to ki sani insha Allah wannan shi ne gani na ƙarshe da za kiyi wa wannan yarinyar"Da sauri ta kalleta kuwa, ita kuma kanta yana ƙasa tana ta hawaye.
"Am dama bana so na katse maka magana ne, amma ni bana biye mata akan wannan abu, ita kanta Ablah za ta shaide ni akan hakan, saboda haka ina sodan Allah ku daina yanke hukunci akan abinda baku sani ba, kuma ni ba zan bari Ablah taje ko ina ba"
"Ba zan zauna ba" ta furta tana kuka tana kallon Mustapha.
"Abba ance ciwona yana da matuƙar haɗari, ina so na samu farin ciki. Tun ina ƙarama na gane bata sona, ban taɓa jin tayiwa mahaifiyata addua ba sai dai ta faɗa mata maganganu masu zafi, akwai ranar dana roƙeta kan ta yafewa mahaifiyata ko da za ta cigaba da baƙanta min, amma taƙi ta riƙa aibata ta duk da ta san tana kwance cikin kabari, ni kuma tana nuna min tsana ƙarara ta sanar min dan babu yadda za tayi ne shiyasa take zaune dani amma ta tsane ni, dan haka nima yanzu da na sake mallakar hankalin kaina ba zan taɓa zama inda ba a sona ba, ko da ba a ga mahaifina ba dama na dawo ne saboda kai Abba, na san hankalinka a tashe yake kana neman inda yake shiyasa dana samu lafiya nazo, shekarana biyu a kwance" Ta ɗanyi shiru tana shashsheƙa."Ku mu tafi" Ya faɗa tare da juyawa ya fita.
"Mami na gode da haƙurin zama dani da kika yi tsawon shekaru. Abba na gode da ilmi sutura da jajircewarka a gareni ba zan manta wannan karamcin ba, na san dama Mama ba zata taɓa bari na zauna ba, dama nima ban zo da niyyar zama ba. Kuma tun a gate maigadi ya sanar min Hamdiyya ta warke, kuma nayi farin ciki da haka. Sannan Abba duk kuɗina dake gurinka da wanda ka juya min wallahi na bar maka halak malak." Tana gama faɗa ta juya ta fita, cikinsu babu wanda ya iya magana.
Tana fita ta tarar dashi a jikin mota ya dafe kansa, tana ƙarasawa gabansa ya ɗago yana kallonta.
"Waye kai? Mene alaqarka da mahaifina? Ina zan ganshi dan Allah?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Ki kwantar da hankalinki Ablah, yanzu kika shigo ƙasar, kuma kina buƙatar hutu, yanzu dai zan kama muku ɗaki a hotel da duk abinda kike so za a miki acan zan kama muku standard room.
"Dan Allah ina son na sani, hankalina sam yaƙi kwanciya wallahi, dan Allah ka taimaka min" Sai kuma ta fashe da kuka.
"Ablah" Ya ambaci sunanta ita kuma bata kalleshi ba.
"Nima kamar mahaifina a gareki, domin mahaifinki aminina ne"
"Ina mahaifina yake?"
"Yana nan kuma dana sanar masa naga 'yarshi to zai zo, ina mai tabbatar miki da zai zo"
Lallaɓata ya yi har ta haƙura suka tafi, ya kaisu babban hotel ya kuma kama mas babban ɗaki sannan ya biya kuɗi masu yawa wanda in sun buƙaci abinci ko nasha.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...