Page 7

79 6 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 7

Kuka sosai take lokacin data buɗe ido ta ganta kwance akan gadon asibiti, Nadia na zaune a gefe tana goge hawaye.
"Dagaske Yusuf ya rasu?"
Kuka Nadia ta saki ta rungume Zeenat, hakan ne ya tabbatar mata ba mafarki take ba.

Bata yarda ta zauna ba, dole suka bata sallama duk da a lokacin akwai zazzaɓi mai zafi a jikinta.

Ko tantama batayi ta san Ashraf ne ya raba Yusuf da duniya amma 'yan uwan Baba sun danganta hakan da sakacin shi, saboda fita yake sai kuma sanda ya ga dama ya dawo, musamman a yanzu da ya ga babu ran Umma, dama itace suke yawan faɗa akan cacar, to kuma yanzu babu ita. 'Yan uwan Umma kuwa tsalle suka yi suka dire kan sai sun tafi da yaran, shi kuma ya ce ba uban daya isa ya ɗaukar masa 'ya'ya saboda ai basu san ciwon su ba, sai yanzu za su riƙa nuna iko dasu.

Haka dai suka sha faɗa sosai, har ma suka ce ko wani abu ya faru kar a nemesu tunda ya nuna basu da iko a kan yaran 'yar uwarsu, shi kuma ya ce ya amince.

                   **** **** ****

"Tana matuƙar bani tausayi" Ya furta yana kallon Auwal.
"Wallahi mamaki kake bani Musty, kamar wani wanda bashi da zuciya, yarinyar nan babu wulaƙanci da cin fuskar da bata maka ba, bana mantawa akwai ranar da ta ce ita gara ta riƙa kallon fuskar alade akan taka, amma shi ne yanzu data ƙare mata take kulaka"
"Har yanzu Zeenat bata ce tana sona ba, kuma ni ina ƙara sonta ne a ko da yaushe"

"Aikuwa ba a gidan nan ba, dan ba zan yarda ka kawo min mahaukaciya gida ba"

Jin muryar Mama kamar daga sama ya saka duk suka kalli inda amon muryar ta ke fitowa, daga ɗakin da suke girki ta fito, wanda gabaɗaya da langa-langa aka yi shi.

"Amma Mama bai kamata ki yanke wannan hukuncin ba" Mustapha ya yi maganar cikin kwantar da murya.

"Na yanke, kuma ban ga uban da zai saka in janye ba, yarinyar nan har haɓo tayi maka, mace mahaukaciya zaka kawo mana a matsayin suruka?"

"Zeenat ba mahaukaciya bace Mama..."

"Dakata Mustapha!" Ta yi saurin tarar numfashin sa kafin ta cigaba da faɗin

"Macen da take tunɓele take haukan da har ana riƙeta, ita kake son ka aura? Dama ance so hana ganin laifi, da alama dai ba ka gano illar auren mahaukaciya ba, tunda ka san dai ba a taɓa zama tsakanin mai hankali da mara hankali, ko kana so ka faɗa min cewa nishaɗi ne ya sa take hauka?"

"Mama ni har yanzu ban gaskata ba, domin wani abin da tayi za ki ga a take tayi nadama, bana raba ɗayan biyu, ko dai ture aka yi mata, ko kuma aljanu ne suka taɓa ta"

"Af! Ana nan dai, haukan dai take, to wallahi baka isa ba, ko Zeenat ƙalau take ba zan iya haɗa zuri'a da ita ba, mahaifinta riƙaƙƙen ɗan caca, wanda kaf faɗin unguwar nan babu wanda bai san rashin kamun kai irin na mahaifinta ba"

Ganin dai Mama na ƙara janyo wani abu na da ban ya saka shi tsuke bakin sa ya yi shiru.

                    ***** ***** *****

"Ɗan caca ɓarawo ne..." Jin haka ya saka shi juyawa ya kalli yaran, wanda suna ganin ya juya suka tsere.

"Kutmar***! 'Yan ƙwal uba iyayenku ne ɓarayi mararsa tarbiyya" Cewar Baba lokacin yana ƙoƙarin saka kai cikin gidan nashi.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now