Page 5

96 4 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 5

𝓑𝓪𝔂𝓪𝓷  𝓦𝓪𝓼𝓾 𝓜𝓲𝓷𝓽𝓾𝓷𝓪

Tana kwance a tsakar ɗakin ya shigo, ganinta a ƙasa wanwar ga jini ta hancinta ya saka shi saurin zuwa gabanta ya tsugunna. Hannu ta miƙa masa, kamar ba zai riƙe ta ba sai kuma ya riƙota, tana tasowa tayi saurin rungumeshi, sai kuma ta ɗan ɗauke numfashinta, ɗan jijjigata yake ya kasa ɗagota, sai kuma daga baya sannan ya ɗago yana kallonta. "Zeenat! Zeenat!!" Shi ne abinda kawai yake nanatawa, cikin tashin hankali ya saɓeta, sai kuma ta buɗe ido ta fara tari, a ɗan juye take kallonshi "Ru...ruwa..." Shi ne abinda ta faɗa, shi kuma ganin ruwan akan mirrow ya saka ya yi saurin mayar da ita kan gado a hankali ya kwantar, yana ƙoƙarin tashi ta janyoshi gabaɗaya ya faɗa kanta "Subhanallahi, ya faɗa tare da tashi ya ɗauko ruwa ya bata ita kuma tasha tana ta sauke ajiyar zuciya kamar gaske.
"Zeenat waye shi?"
"Ya gudu"
"Muje asibiti?"
Kai ta girgiza, sannan ta ce "Bana so kowa ya san abinda ya faru za a iya ɓata min suna, sannan su Umma ma ba zasu fahimceni ba"
"Amma mene ya kawo ki hotel Zeenat?"
"Cewa aka yi inzo ga Zuby nan suna faɗa da wani saurayi" Ta furta tana tsiyayar hawaye kamar gaske.
"Yanzu haka ma da ita aka haɗa baki dan a ruguza rayuwarki, Zeenat dan Allah ki rabu da ƙawayen nan naki wallahi babu alkhairi a zamanki dasu"
Kai kawai ta gyaɗa alama ta gamsuwa.

_Washe Gari_

Wani rantsatstsen lace ta saka wanda aka mata ɗinkin wrapper gown tayi kyau ta kuma kama jikinta, haka ya saka shape ɗin jikinta da kuma kyawun surarta ya bayyana. Lace ɗin purple ne, light and dark, hakan ya saka ta saka gyale purple tare da wani dogon takalmi, glass ta saka a saman goshin sannan ta fito tsakar gidan.

"Wow...! Yayata tafi ta kowa" Shi ne abinda Nabiha ta faɗa lokacin tana tattara bokatan da aka dama koko.
Murmushi kawai Zeenat tayi tare da samun kujera ta zauna, tana faɗin "Ke dai bari, ni wallahi na gaji da kullum sai anzo ɗaukata, ya kamata ma mutum ya sayi mota.
"Da kuɗin motar ai gara ki bayar muyi jarin wani abu ko mun samu rayuwarmu tayi kyau"
Ɗan taɓe baki tayi sannan ta ce "Har yanzu Umma bata dawo ba?"
"Wallahi kuwa"
"Ni dai ƙilan sai dai ace mata na tafi school dan gaskiya ba zan iya jira ba"
"Wai Adda Zeenat dama duk wannan adon makaranta za kije?"
"Eh mana"
"To ai ni wallahi na ɗauka wani taro ne na biki za kije"
Mtsww "Baƙauyiya"
Gabaɗaya dariya sukayi.

Zuby bata shigo gidan ba, dan dama ba al'adarta bace shiga gidansu sai idan ta kama, sai dai tana jin horn ta tashi ta fita.
"Ya dai? Na san zuwa yanzu labari ya karaɗe makaranta, mun yi waya da Zuby ta ce za ta zo ɗaukata kuma sai na ganki."
"Hmmm" Zaheeda ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Akwai matsala fa"
"Matsala? Ba dai fuskata ta fito a wannan videon ba?"
"In wannan ne ai da sauƙi Zeenat..." Zaheedah ta faɗa kamar za tayi kuka.
"Mene ke faruwa ki sanar dani"
"Ina tunanin Ashraf aljani ne"
"What..?" Ta furta cikin tashin hankali.
"Mun shiga uku Zeenat duba ki gani."

Karɓar wayar tayi jikinta na rawa ta fara kallon video ɗin, gabaɗaya babu shi sai Zeenat ɗin ita kaɗai take ta abubuwan da tayi"
"Amma meyasa baku sanar min tun a jiyan ba?"
"To ina muke da nutsuwar nan, kin san muna sauke ki sai muka wuce restaurant, to bayan mun ci abinci ne sai muka buɗa dan mu kalla, shi ne muka ga haka. Dukkanmu jiki a saɓule muka koma gida, amma kuma tun a jiyan bana samun Zuby a waya, sai yau da safe ake faɗa min ai a asibiti ta kwana kuma ma rai ya yi halinsa."
"Me...me...me kamar ya rai ya yi halinsa"
Hannu ta saka ta goge hawaye tare da faɗin "Zuby ta rasu, jiya ta fara ciwon ciki aka ɗauke ta zuwa asibiti kafin kuwa aje har ta rasu." Ta ƙarasa maganar da kuka.
"Idan Zuby ta rasu jiya da waye muka yi waya yau?"
Kallon juna suka yi a tsorace, a lokacin kuma kira ya shigo mata, gabanta ne ya faɗi duk da baƙuwar number ce amma hakan ya razanata. Da ƙyar ta samu ta ɗauka jikinta a sanyaye ta kara a kunne.
"Hahahahhhhh......!" Wata mahaukaciyar dariya ce ta sauka a dodon kunnenta hakan ya saka ta sauke wayar tare da kallon Zaheedah sai kuma ta mayar da wayar kunnenta. "Zeenat ni za ku yi wa tarko, ni zaku cuta..." Bata jira me zai ce ba ta kashe wayar.
"Shi ne!" Ta furta tare da fashewa da kuka "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta cikin tashin hankali.
Jikin Zaheedah gabaɗaya shaking yake, ta kasa cewa komai saboda tsananin tashin hankali da furgici da suka shiga.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now