*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 16
Da sauri ya bi bayanta ya kuma dakatar da ita da faɗin "Yarinya ce ƙarama, wani ma bare ya riƙeta bare ke, kina ji fa ta ce a hannunta take, dalili ne ya saka ta dawo da ita, haba Nabiha ban san ki da haka ba"
Kallon shi tayi ranta a ɓace ta ce "Zeenat ita ta cuci kanta Abban Yara, ka so Zeenat sosai amma ta riƙa nuna tafi ƙarfinka, ban so Zeenat ta mutu ba naso tazo taga arziƙin da ka samu"
"Karki damu da wannan domin ba dan nayi mata gori Allah ya bani arziƙi ba, ke dai mu tayata da addu'a tunda dai a yanzu bata doron ƙasa"
"Ai jininta tana nan, ni dai ina fatan kar aljanin ya dawo ɗaukar fansa"
"Tame kuma? Bayan Zeenat bata raye"
"To yanzu wancan ɗakin za a gyara mata?"
"Wane ɗaki?"
"Na baƙi mana"
"Larura fa gareta, taya ya zamu wareta, haba Mamin Yara kiyi haƙuri mana"
Kai ta dafe tare da faɗin "Ni kam an cuceni wallahi" Da sauri ta wuce ta shiga ɗakin.Kallon Ablah ya yi da take rakuɓe, hannunta na cikin hijab ya ce "Taso muje ko" Kallonshi tayi da manya sexy eyes ɗinta masu matuƙar kyau, duk da yana cikin glass amma hakan ba zai hana a gane basu da lafiya ba, duba da yanayin ƙwayar tana da matuƙar haske ba kamar wadda aka fi sani baƙa ce siɗik.
Miƙewa tayi a sanyaye saboda ta san ba lafiya ba yadda taga matar gidan wadda Saratu ta tabbatar mata da itama mahaifiyarta ce amma kuma tana nuna kamar bata sonta.Suna shiga suka tarar da Nabiha zaune a parlour kan one seater ta ƙurawa gu ɗaya ido, suna shiga kuma garesu ta mayar da kallon nata, ranta a ɓace kamar ba ita bace take fara'a a ɗazu.
"Zauna a kujera Ablah" Ya faɗa, lokacin ita kuma ta dalla masa harara, murmushi kawai ya yi ya zauna kusa da ita.
"Mamin Yara dan Allah kiyi haƙuri, yarinyar nan ɗiyar 'yar uwarkice, kuma jini ɗaya yafi ƙarfin wasa"
"Ni na tabbatar da lafiyarta ƙalau ba za su kawota ba, bama zan san an haifeta ba, sai yanzu da suka ga ba zasu iya ba tunda tana da larura"
"Kece dolenta su ai ba dolenta bane, kiyi haƙuri" Haka ya yi ta lallaɓata har dai ta haƙura taja kayan Ablah zuwa ɗakin yaran.**** **** ****
Yau kwana biyu kenan amma sam bata jindaɗi, ji take kamar ta ɗauko Ablah ta cigaba da zama da ita. Ita dai haka nan Allah ya ɗora mata son Ablah ko kaɗan bata son taga yarinyar a dumuwa, sai dai ta san zama da Ablah a gidan karuwai abu ne mai matuƙar haɗarin gaske, musamman a yanzu da taga Magajiya na ƙoƙarin mayar da ita nama.
Jin hayaniya ya sa ta miƙe daga kishingiɗen da take, duk da ta san faɗa ba wani abu ne na mamaki a gidan ba duba da yadda gidan yake na 'yan balaja'u.
"Ina take munafuka na rantse yau hukuma ce zata rabani dake"
Jin muryar Magajiya ya saka Saratu fita da sauri, aikuwa a ƙofar ɗaki ta ci karo da Magajiya "Yawwa gara da kika fito kafin na saka a fito min dake tantiriya"
"Tantiriya?"
"Eh haka nace, ko kina da wani sunan da yafi wannan? Ke da aka haifa a kwalta"Jin wannan furuci ya yi mugun ɓatawa Saratu rai, sai dai ta danne tare da ƙaƙaro murmushi na dole sannan ta kalli magajiya "To uwar tantirai mene ke faruwa?"
"Ke ki kiyayeni kar ki kuskura ki faɗa min magana"
"To kina da sunan da yafi wannan ne? Ko me muke anan ke uwarmu ce a harkar.""Yau kuma Magajiya kece kike faɗa da Sarah, haba ba girmanki bane"
"Ke rufa min baki baƙar munafuka, ina ruwanki? To duk shegiyar data ƙara saka mana baki ta tabbatar wa'adin zamanta ya ƙare a gidan nan"
Jin haka ya saka duk suka ja baki suka yi shiru, sai dai kuma ko wacce ta fito ta kuma kafa idanu dan taji gulma."Kwana biyu na baki, ina nufin awa 48 ki dawo da Ablah idan kuma ba haka ba..." Ta ƙyasta mata hannu "Kin san sauran"
"Ablah ta tafi kenan Magajiya sai dai kiyi haƙuri, amma ba zan zauna ina kallo a cutar da ƙaramar yarinya ba, dan haka Ablah na sadata da danginta."
"To ke kuma zan sadaki da 'yan sanda ne, dan ba za ki jawo min bala'i ina zaman zamana ba."
"To 'yan sanda ai ba yau na fara arangama dasu ba, abinda na sani dai ko na shiga dole zan fito"
"Hmmm! Dama ance tsintacciyar mage bata mage"
"Magajiya kenan, ko me zaki faɗa ki faɗa dan yau babu hayaniya a kaina, amma ki sani idan kika kaini bango reshe zai iya juyewa da mujiya"
"Me kike nufi?"
"Ina nufin zan iya kaiki bayan kanta"
"Jar uba, ni za ki kai bayan kanta Saratu?"
"Ƙwarai kuwa Mannira, yau dai bari in kiraki da sunan yankanki"
"Taɓ lallai"
Tsaki kawai Saratu taja sannan ta koma ɗaki.
![](https://img.wattpad.com/cover/351344300-288-k542301.jpg)
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...