Page 29

104 8 1
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 29

Maigadi da sauri ya shigo dakin, lokacin Nabiha da Mustapha sun isa gaban Ablah.
"Yallaɓai shi ma fa yana can ya suma"
"Shi wa?" Mustapha ya furta a kiɗime dan ya manta ma da Nabil.
"Ɓaƙon nata"
"Subhanallahi" Ya furta yana miƙewa da sauri.

_Few Minutes Later_

Suna zaune a parlour gabaɗaya har Hamdiyya. Ablah kanta yana bisa gwiwarta data ɗagota ta jigina kanta a jiki, har lokacin bata bar hawaye ba.

"Gaskiya a san yanda za a yi da wancan yaron, dan ni wallahi tsoro ma yake bani"
"Wane tsoro ke ana neman mafita kina wata magana da ban, ai dai kin ji abinda Ablah ta faɗa zuwa yanzu kin san shi ɗin ba aljani bane"
"Amma ai aljanin yana jikinsa taya za a bar min shi cikin gida."
"Nabiha dan Allsh ki barni in yi tunanin mafita karki ska min ciwon kai:
"Mafita ai bamu da ita, tunda har Ashraf bai tafi ba yanzu yazo da wani salo kuma, ni ban ma taɓa ganin kafaffen aljani kamar wannan ba, kawai a bashi ita a huta tunda ai sonta yake ba ƙi ba ba zak cutar da ita ba"
"Wace magana ce kike faɗa haka?"
"To ai gaskiya ce, kar yazo ya fara mana ɗauki ɗai-ɗai kamar yadda ya yi a baya, gara kawai a bashi ita"
"Idan Hamdiyya ce aljani yake so za ki bashi?"
"To ai Hamdiyya bata yi komai ba, haka uwarta ma bata yi komai da aljani zai addabi rayuwarta ba, kuma muna azkar mun fi ƙarfinsa"

Ablah miƙewa tayi, duk suka bita da ido, bata kalli kowa ba kawai ta wuce.

"Idan har kika cigaba da muzguna mata haqqinta ba zai taɓa barinki ba"
"Bani da wani haqqinta a kaina, dan duk wanda nake dashi na sauke"
Tana gama faɗa ta miƙe ta wuce itama.
Hamdiyya ma tashi tayi, karo na farko data nufi ɗakin Ablah a sanyaye, dan a baya sai dai rashin kunya ko gargaɗin ko kuma idan Abbanta ya saka ta kirata.
Tana shiga ta tarar da Ablah zaune gaban gado tana hawaye, bata ma san Hamdiyya ta shigo ba, sai jin hannun Hamdiyyar tayi a fuskarta tana share mata hawaye.
Kallonta tayi "Kiyi haƙuri Ablah kiyi haƙuri dan Allah"
Ƙara fashewa tayi da kuka, Hamdiyyar ta rungumeta, shekaru 7 kenan sai yau ta samu kafaɗar da ta tallabeta a lokacin da haayenta yake zuba, itama Hamdiyya kuka kawai take, a yanzu ne kawai taji tana matuƙar tausayin Ablah.

"Kukan ya isa haka" Suka ji an faɗa daga bayansu.
Duk ɗagowa suka yi suka kalli Mustapha.
Hamdiyya da sauri ta miƙe ta rungume Mustapha "Abba sam Mami bata son Ablah"
"Ya isa haka" Ya kama hannunta suka ƙarasa gaban Ablah.
"Ablah yau fa aka sallamoki daga asibiti kuma Dr ya ce ki daina yawan damuwa da ɓacin rai"
Majina taja sannan ta ce "Abba yanzu shi kenan aljani zai ɗaukeni ya tafi dani cikin aljanu?"
"A'a hakan ba za ta faru ba"
"Mami ta ce idan ba ayi haka ba zai fara kisa, kuma ta bani labarin Ammina" Bakinta har karkarwa yake tana maganar.
"Ablah kina nufin kin san komai game da Ashraf?"
"Abba na san komai game da rayuwar mahaifiyata da yadda aka sameni da yadda Ammi ta maka kai da Ashraf, Ammi bata raye na roƙi Mami ta yafe mata amma taƙi ta ce ta tsneni sosai shiyasa nasha Jik dan na mutu kawai"
"Yanzu Ablah kina sane d idan mutum ya kashe kanshi wuta zai je shi ne kika sha Jik?"
"Na manta Abba ni kawai ji nayi ina son barin duniya"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya sauke sjiyar zuciya sannan ya ce "Kin ga komai zai wuce fa, zan yi magana da Nabiha kuma batun Ashraf ma zamuyi magani"
"Abba kawai ka bar ni ya ɗaukeni, bana so kowa ya shiga matsala saboda ni, ka ga wancan mutumin bai san komai ba amma gashi nan ga shiga rayuwarsa, amma idan ya tafi dani na san ba zai ƙara shiga jikin wani ba dan ya yi magana dani"
"Ba zai yuwu mu barki da aljani ba"
"Abba..."
"Bana so ki riƙa wannan maganar ni na san abinda zan yi" Yana gama faɗa ya miƙe da sauri ya bar ɗakin.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now