*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 22
Mamaki abin yake bawa wasu, yayin da wasu suke ganin abin a tsantsar iyeyi.
Sun sha kuka sosai kafin Maryam ɗin taja trolley ta tafi, ita kuma Saratu ta koma ɗaki ta cigaba da rera kuka.A koda yauahe idan ta tuna bata san kowa ba kuma bata da kowa ta kanji babu daɗi amma a yanzu kuka take na rashin asali, tun yanzu duniya ta fara juya mata baya, tabbas duniya rigar aro ce, kana cikin fantamawa sai dai kaji an amshe. Ita da maza suke rububi mata kansu yaba kyaunta suke amma yamzu gashi ta zama abar tsoro kuma abar ƙyama ga kowa, ita kanta idan ta kalli fuskarta tsorata take, dalili kenan daya saka ta fasa duk wani madubin ɗakin, dan data kalla take jin matuƙar ɓacin rai.
A yanzu kam ji take ina ma itama tana da dangin da zata koma garesu, sai dai ina, bata san su ba, ba kuma ta san a ina suke ba.
*Jigawa State*
Tunda aka sauketa a tasha take jin tsananin faɗuwar gaba, tunani take da wane ido za ta kalli alhalin nata. "Hajiya tafiya ne?" Jin muryar mai napep ne ya dawo mata da tunanin data faɗa.
"Eh Yalwawa zaka kaini" Ta furta tana ɗaukar trolley ɗin ta saka a napep.Har ta isa ƙofar gidansu ta fargaba ta isa, babu abinda ya canja a gidansu, sai dai unguwar ta ɗan canja mata.
Tana sallamar mai napep raja trolley ɗinta zuwa cikin gidan."Umma ga Yaya Maryam" Ƙanwarta Hafsa ta faɗa tare da dire tsintsiyar hannunta ta ƙarasa ta rungumeta cikin jindaɗi. Umma kuwa tana fitowa Maryam ta ƙarasa gabanta, tana rungumeta kuwa a tare suka fashe da kuka, a haka Baba ya fito ya samesu.
Sakin Umma tayi ta durƙusa gaban Baba ta cigaba da shashsheƙar kukan.
"Ya isa haka Maryam ki shiga ciki ki huta ki kuma ci abinci.Kwananta biyu a gidan sannan suka samu zama da Babanta da kuma Ummanta.
"Meyasa kika yi haka Maryam? Kin kuwa san irin tashin hankalin da kika saka mu ciki kuwa?"Kuka sosai take dan bata ɓoye masu komai game da inda ta tsinci kanta. Salati kawai Baba yake yayinda Umma ta fashe da kuka, dan irin tarbiyyar da ta bawa yaranta bata yi tunanin a cikinsu wani zai yi ƙaramin saɓo bare babban kamar bariki.
"Yanzu me kika tsinta a barikin? Yadda kika je haka kika dawo Maryam, sai dai ga fuskarki nan ana gani an san kina shafe-shafen mayukan bleaching dan ni kam na san ba haka kike ba, kuma baki da ƙuraje ko kaɗan a fuska"
"Nayi nadama Umma, nayi dana sanin bijire maku"Baba ya gyara murya ya ce "Sannan Faisal ɗin nan ke kika ce kina so, kika kawo mana shi a matsayin mijin da za ki aura, amma sai kawai ki gudu dan ya ce ku biyo zai aura"
Shiru tayi tana share hawaye.
"Ita wadda kika ƙi haƙura a haɗakun, kika dage sai dai ki zauna ke kaɗai, da kin yi haƙuri da ita ɗin ba mai daɗewa bace, domin Allah ya karɓi rayuwarta tun a gurin haihuwa""Yarinya mai ladabi da bibiya, har ƙasa take gaisheni, sannan bata haɗa ido dani ba. Allah ya mata rahama" Cewar Baba.
"Amin ya Allah ai gaskiya mace ce mai kirki"
Ita dai Maryam bata ce komai ba, haka aka tashi zaman, iyayenta sun yafe mata sannan ance ba za a taɓa faɗawa dangi cewar bariki tayi ba saboda surutu, sai dai duk wanda za ta aura za su faɗa masa gaskiya, kafin nan kuma za tayi istubura'i.
Da yamma suna zaune da Hafsa suna ta taɗi, "Yaya fa jiya mun yi chat dashi sosai, ya ce sai kin huta zai zo ya ganki"
"Wane Yaya?"
"Yaya Faisal mana"
"Zuwan me zai yi?"
"Haba Yaya Maryam, ni fa na san har yanzu Yaya Faisal yana ƙaunarki"
Taɓe baki tayi tare da faɗin "Daga baya kenan wai an yi sadaka da mayya, haba Hafsa duk ba dalilinsa na shiga baƙar rayuwa ba, ai babu wata soyayya tsakanina dashi"
"Allah Yaya Maryam ya damu sosai lokacin da kika gudu, ko ita Aunty Binta wallahi kullum addu'a take Allah ya dawo dake dan ku fahimci juna"
"Ashe wai ta rasu?"
"Eh har ta kusa shekara biyu da rasuwa, a gurin haihuwa ta rasu, amma ta haifi 'ya mace sai aka mayar da sunanta, yarinyar tana gidansu"
"Shi bai ƙara aure ba?"
"Eh yana nan har yanzu bai ƙara aure ba"
"Ok"

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...