Page 4

95 5 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 4

_Za ki tafka babban kuskure muddin kika ce za ki yi faɗa dasu Zuby._ Wata zuciyar ce ta faɗa mata haka ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da zama kan tsohuwar katifarsu wadda da kaɗan tafi tabarma.
"Zuby itace madubi na, dan ko suturun da nake taƙama dasu ta sanadin tarayya dasu na samu" Iska ta furzar mai zafi, gami da miƙewa tsaye ta jingina da bangon ɗakin nasu wanda ko fulasta babu.
_Idan nayi sau ɗaya na san shi kenan, kuma ba zan taɓa bari kowa ya sani ba, sannan na san suma za su rufa asiri tunda mun zama ɗaya._ Shiru ta sake yi lokacin da zuciyarta ke rattobo mata bayanin nan.
_To amma meyasa sai ni? Saboda ni nake soyayya da Ashraf? To ai nima ba son shi nake ba, so nake ma na rabu dashi dan ya zame min ƙadangaren bakin tulu._ Ta sake furtawa jikinta a saluɓe ta kai mazaunanta ƙasa, tare da dafe kai.
"Ya zama dole na amince da ƙudirin su muddin ina son burina na auren mai kuɗi ya cika."

Umma ta buɗe labule tare da faɗin "Lafiya naji kamar kina magana ke kaɗai?"
A ɗan tsorace ta kalleta, sai kuma ta ƙaƙalo murmushin ƙarya, "Wallahi Umma ina hadda ne, saboda sati biyu ban je islamiyya ba so nake na koma"
"Ya dai kamata, dan ga Nabiha nan har ta kusa sauka, shiyasa nace miki idan ma kina ganin baki da lokaci ki shiga ta asabar da lahadi, saboda dole sai an haɗa biyu"
Murmushi tayi tare da faɗin "Insha Allahu zan shiga Umma"
"Hakan ma ya yi, Allah ya taimaka"
"Amin" Ta furta a sanyaye.

Kwana biyu sam bata zuwa ko ina sai dai a 'yan kwanaki biyun akwai wani maƙocinsu daya takura mata shi a lallai dole son ta yake, ita kuwa a tsarinta ma bata ga ajinta a ko kusa da unguwarsu ba bare cikin unguwar tasu, samari masu kuɗi da take buri har yanzu babu ɗaya na kirki daya taɓa tsareta da sunan so na gaskiya, sai dai sha'awa kuma kai tsaye suke faɗa mata, kasancewarta mace mai diri, komai na jikinta ya yi dai-dai da irin yadda ake son mace ta kasance, sannan ta fuska ma tana da kyau, dan kuwa tana da manyan idanu masu maiƙo, da kuma dogon hanci, haɗi da ƙaramin baki, tana da tudun leɓe kaɗan, sannan tana da saje da kuma kwantaccen gashi a gaban kanta. Tana da dogayen gashin ido haɗe da gira cikakka kuma kwantacciya, bata da tsayi sosai sai dai ba za a kirata gajera ba, sannan kuma bata da ƙiba kuma ba siririya bace 'yar (Chubby) da ita.

Suna ta faman tace ƙullun awara da Nabiha keyi kullum da magriba,  sai ganin yaro suka yi ya shigo gidan "Wai ana kiran Zeenatu"
"Uban waye yake kirana Zeenatu?"
"Ubanki ne...!"
Gabaɗaya suka juya ita da Nabiha jin muryar Baba.

"Zeenatu na raɗa miki ko za ki canza ne?"
Bata ce komai ba yaron ya fita.
"Malam wannan zagin ai bai kamata ba.."
"To ke kuma a zagwai gwai, ai na san ke kike zuga su wurin ƙin yi mini biyayya" Ya mayar da kallonsa ga Zeenat "Ɗauki gyale kije ki ga ko waye"
"Baba ni na san ba wani baƙon kirki bane"
"Ki ɗauka kije ko na kwashe miki albarka, 'yar baƙin ciki, na rantse in bakiy wasa ba a caca zan saka ki kin ga idan ba a samu nasara ba sai a bayar dake na huta da sadaka"
"Allah ya sawwaƙa mata, wallahi muddin ka sake saka 'ya'yanka a caca na rantse da Allah zamu gudu ne mu barka dan ba zan lamunta ba, haka ka saka Nadia da ƙyar aka kashe case ɗin"
"Ke dai kika sani" Ya faɗa tare da komawa ɗakinshi.

Zeenat ɗaki ta shiga ta ɗauko gyale sannan ta fice rai a ɓace.

"Kenan kai ne?" Ta furta tana tsaye fuskarta a tsuke.
"Zeenat sai yaushe za ki bani dama?"
"Har abada ba zan taɓa baka wata dama ba wallahi, kai wai Mustapha baka da zuciya ne?"
"In dai akan son ki ne gaskiya bani da ita"
"To bari kaji ko giyar wake nasha ba zan iya auren ƙasƙantaccen mutum talaka kamarka, ni abin kunya ne a gurina a zo a ganka anan ina tsaye da kai, ina gargaɗinka da ka fita a sabgata, kar na ƙara ganin ka tattago wannan akwalar ƙafar taka kazo da sunan gurina kazo, idan ba haka ba wallahi zan ci maka mutunci" Tana gama faɗa ta juya ta koma ranta a matuƙar ɓace.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now