*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 25
Sai lokacin ta lura da maigadi da kuma Nabil, idanunsu ma a kanta suke, dan haka ta fasa tare da miƙewa da sauri.
Lumshe ido ya yi, yana ɗan murmushi tare da miƙewa tsaye, "Bari na koma ciki"
"To yallaɓai."Ana kiraye-kirayen sallar magrib ta ƙarasa gida. A hankali take tafiya cikin falon tana ƙoƙarin ƙarasawa ɗakinta.
"Munafuka ina za kije?" A tsorace ta juyo tana kallon Nabiha."Daga ina kike?"
"Islamiyya"
"Islamiyyar da ake tashinku tun ƙarfe 5:30 amma ki dawo min gida ƙarfe kusa 7 kice min daga islamiyya kike?"
"Mami da nisa, kuma a ƙasa nake tahowa"
"A ƙasa ko?"
"Mami wallahi dagaske nake miki"Hamdiyya data fito rungume da ƙatuwar teddyn da kullum take riƙo kamar an manne ta da ita, ta kalli Nabiha ta ce "Mami ƙarya fa take, wllahi akwai wata ƙawarta Salma tare suke ita take janta, kuma da ganinta ma 'yar iska ce"
Kai take girgizawa tana hawaye.
"Yanzu ke da kike musaka dungulmi ga kuma rashin gani har kin san iskanci ko?"
Kuka kawai take, dan tun zuwanta gidan shekarun ɗa tayi a gidan ranaku kaɗan ne ba a gana mata azaba."Kin taso gidan karuwai ni dama na san za a rina, kai Zeenat ta cuci ahalinmu yanzu yarinya ƙarama shekara sha tara amma kin san iskanci kin san bin maza, ni dama na san tun ranar da aka kawo min ke an riga an gama buɗe idanunki da kwartaye ko?"
"Mami wallahi daga islamiyya babu inda..." Ko ƙarasa faɗa bata yi ba Nabiha ta wanka mata mari sai da har glass ɗin ta ya faɗi ƙasan tiles ɗin. Hannunta ta saka ta taɓa kumatun tana kallon Mami dusu-dusu saboda babu glass a idanunta.
"Yau sai kin gane kurenki baki gaji da shan duka ba."Hawaye kawai take ta sunkuya ƙasa tana laluben glass ɗin nata, ga ƙafarta da za ta iya mayar da glass ɗin akwai safa a ciki, tana iya lallaɓawa ta cire da kanta da mayar da hannayen nata amma yanzu da faɗuwa ya yi bata san ina zata ganshi ba, bare ta san yadda zata mayar dashi fuska. Sai jin saukar wayar wuta tayi a jikinta.
Miƙewa tayi ta ruga, Mami na dukanta, ga bata ganin komai, bata ankare ba ta buga goshinta da bango, a take a gurin ta ƙwalla ƙara tare da sumewa.
_Few Hours Later_
A hankali ta buɗe idanunta da take jin suna mata ɗan zugi-zugi. "Abba...!" Abinda ta fara furtawa kenan, saboda kanshi idonta ya fara sauka, muryarta ma ko fita batayi sosai.
"Ta farka" Ya furta yana kallon Nabiha, sai a lokacin idanunta suka kai kan Nabiha a take ta fara jera mata sannu.
Mamaki kawai take tana kallonta tana faɗawa Mustapha cewar ƙararta kawai suka ji suna shigowa ɗakin suka tarar da ita kwance kan tiles kanta ya fashe shi ne suka yi gaggawar kiran Dr yazo ya mata dressing ya kuma saka mata drip, awa biyu cur tayi a sume.Kai kawai ya gyaɗa tare da faɗin "Ki haɗo mata tea mai kauri"
"Ok. Ta furta sannan ta miƙe ta fita.A ƙofar ta tsaya tana hararar ƙofar tamkar suna ganinta.
"Ni ko dan wannan abin da kake mata ai zan ƙara ƙulewa, kuma wallahi dan dai kawai Mama ta shigo maganar amma da ba zan ji tsoron faɗa maka duk abinda nayiwa wannan yarinyar ba. Rai a ɓace ta wuce kitchen."Ablah dagaske faɗuwa kika yi ko itace tayi miki wani abu?"
"Abba faɗuwa nayi"
"Amma idan faɗuwa kika yi wannan sahun marin dake fuskarki fa?"
Shiru tayi, sai kuma ta ce "Tun a Islamiyya ne, mu samu saɓani da ƙawata shi ne ta mareni"
"Ablah na san ke ba mace bace mai hayaniya bare kiyi faɗa, meyasa baki son faɗa min gaskiya"
"Dagaske nake" Ta furta lokacin kuma wasu hawayen masu zafi suka kwararo mata.
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Narrativa StoricaƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...