*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 28
Da ido kawai take bin shi da kallo dan bata gane shi ba.
Kallon Hidaya ya yi ya ce "Na santa" Sannan ya ƙarasa gaban gado.
"Sannunki" Ya furta yana kallon Amira.
"Yawwa sannu"Hidaya sakin baki kawai tayi ganin ya tafi gaban budurwa ya barta da yarinya a gado.
Abaya ce a jikin Ablah ta rufe hannayen ba wanda zai gane dungulmi ce, amma shi yana ganinta ya ganeta, saboda kamaninta basu canja ba, sai dai kyau data ƙara sannan kuma ta zama cikakkiyar budurwa, ta ƙara tsayi ta kuma ɗan rame dan wuyanta ma duk ƙasusuwa sun bayyana."Ablah baki gane ni ba?"
Kallonshi take ta gyaɗa kai alamar eh.
"Baki tuna Uncle ɗinki ba, lokacin kina 12year, nace ki zauna a gun Magajiya zan je na dawo na kaiki gurin danginki"
"Ohhh!"
"Kin gane?"
"Eh na tuna, kace min za ka dawo kuma baka dawo ba"
"Na dawo na tarar baki nan, kuma ban san ina aka kaiki ba"
"Aunty Sarah ta kaini wurin dangina, yanzu haka ina zaune tare da ƙanwar Ammina"
"Masha Allah gaskiya nayi miki murna sosai, ko itace wannan?"
Kai ta girgiza tre da faɗin "Ba ita bace, tana gida"
"Meke damunki na ganki a asibiti?"
"Bani da lafiya amma na samu sauƙi ma"
"To Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne"
"Amin ya Allah"
"Zan kuwa gaisa da ita tunda na ganta"
Murmushi kawai tayi dan yadda ya yi maganar ta tabbatar da shi ɗin ba ɗan uwansu bane kamar yadda ya faɗa a baya."Mara lafiya kuma kuka kawo, Allah ya bata lafiya"
"Amin Ablah"
Likitan daya shigo suka kalla gabaɗaya."Sannu Ablah"
Murmushi tayi, bata ce komai ba.
"Yanzu jiki ya yi sauƙi ko?"
Kai ta gyaɗa alamar eh.
"To ki kula kin ji, dan Allah kar ki sake shan wani abu da niyyar ki kashe kanki"Kallon Affan tayi suka haɗa ido, tayi saurin suke ido ƙasa.
Shi kuma Dr ɗin ya cigaba da cewa "Kisa ba shi ne maganin damuwarki ba, kuma ga yanzu kina da ciwo, ki rage damuwa kin ji"
Kai ta gyaɗa, wasu hawaye masu zafi suka zubo daga idanunta.
"Yanzu insha Allah zamu baki sallama, ki kula da shan magunguna kinji ko?"
"Insha Allah" Ta furta a sanyaye.Dr yana fita Affan ya bi shi.
"Dr" Ya kira sunanshi, ya juyo yana kallon Affan ɗin. Hannu ya miƙa masa suka yi musabaha.
"Ina son sanin abinda ya faru da ita, dan na san ba za ta faɗa min gaskiya ba"
"Kai a wa kenan?"
"Ni ne wanda zata aura"
"Oh kayi haƙuri ban sani ba"
"Karka damu"
"Allah yasa ba kaine maganin matsalarta ba"
"Idan har ban saka ta farin ciki ba ba zan taɓa saka ta baƙin ciki ba."
"Masha Allah"
"Mu ƙarasa office"
"Okay"Hannu ya saka ya dafe goshi lokacin da Dr ya gama masa bayanin komai.
"Amma mene ya haddasa hakan?"
"Damuwa, gaskiya akwai abinda ke damunta sosai"
"Shi kenan insha Allah zan san abinyi"
"Wataƙila ko larurar dake tare da ita ne ya saka take damuwa"
"Shi ɗin ma ba a ce a'a ba, amma insha Allah koma mene zamuyi maganin matsalar"
"To shi kenan Allah ya taimaka"
"Amin"Yana shiga ɗakin ya tarar Ablah tana kwance ta juya baya tana kallon bango, Amira ma bata nan, bai kuma san bacci take ko idanunta biyu. Hidaya kuwa fuskarta a ɗaure kamar an aiko mata da saƙon mutuwa.
"Har yanzu bacci take?"
Hararar shi tayi, bata ce komai ba.
"Afuwan nayi laifi ko?"
"Hmm!"
"Kiyi haƙuri, itace yarinyar dana baki labari"
"Yar 12yrs?"
"Eh ashe baki manta ba"
Murmushi tayi tare da faɗin "Allah sarki, itace ta girma kenan?"
"Eh gata nan kina ganinta"
"Allah sarki" Sai kuma ta saki ranta, dan a yadda ya bata labari babu maganar soyayya bare batun aure, uwa uba ya ce kawo mai ita aka yi hotel ai bai isa ba ya fara wannan ɓarin zancen.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...