Page 8

105 5 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 8

A kiɗime take kallon Malamin dan gabaɗaya ta gama karaya ta sare sosai, dama a tsorace take sai kuma gashi ya haɗa mata da tsawa.
"Ki riƙa addu'a domin kin san babban makami ne, ki dage akan hakan"
Kallon Nabiha tayi suka haɗa ido, sannan a sanyaye ta ce "Insha Allahu Malam."

Suna fita taja tanga ta tsaya, kallon Mustapha tayi idanunta cike da hawaye ta ce "Mu haƙura kawai Mustapha, ba zan iya bari ka tafi ba bayan ance gurin yana da haɗarin gaske"
"Zeenat komin haɗarinsa zan je, saboda ke" Kallonsa kawai take hawaye wani na bin wani a idanunta.

"Amma Mustapha ina ganin kar so ya saka ka salwantar da rayuwarka" Nabiha ta furta a sanyaye.
"Hmmm!" Ya yi murmushi sannan ya ce "So babu abinda baya sawa, na daɗe da soyayyar Zeenat a cikin zuciyata kuma zan bautawa soyayyarta"
Kallon Zeenat ya yi ya ce "Kalma ɗaya nake so ki furta min tare da alƙawari"
Da manyan idanunta take kallonsa wanda suka ɗan yi red kaɗan.
"Ina jinka"
"Ina so ki faɗa min kina sona, kuma za ki aure ni, wannan shi ne abinda zai ƙara min ƙwarin gwiwar tafiya, sannan ina so kiyi min alƙawarin bayan mu babu wanda zai san nayi wannan tafiyar."

Har ƙasa Zeenat ta kai gwiwoyinta tana kuka, kafin ta ɗago ta kalleshi ta ce "Ina sonka Mustapha so mara musaltuwa, kuma na maka alqawarin muddin ina raye bani da miji sai kai, ina matuƙar ƙaunarka"
Murmushi ya yi gami da lumshe idanunsa, har cikin ransa yana jindaɗin kalamanta.
Haka suka hau mota suka koma Kano dukkansu da damuwa a ransu, yayinda shi kuma Mustapha yana cikin farin cikin karɓar soyayyarsa da Zeenat tayi, sam bai hango tarin bala'un da zasu tunkarosa a wannan tafiyar da zai yi ba.

Cikin sati ɗayan nan kuwa sun sha soyayya sosai kamar su cinye kansu, Mustapha ƙara jindaɗi yake ganin kuma yana ƙara ɗebe mata kewar damuwarta, sai dai kuma sam bata ƙara ganin Ashraf ko mafarki dashi ba bare ya kashe mata wani.

                 ***** ***** *****

"Gobe ne zan tafi, da asuba nake son tafiya domin daga Roni Malam zai sakani a hanyar zuwa dajin nan"
"Mus...!" "Kar ki ce komai Zeenat addu'a kawai za ki yi min Allah ya dawo dani lafiya ya kuma saka nayi nasara"

Ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin "Ina matuƙar ƙaunarka Mustapha, zan zauna ko tsayin wane lokaci ne domin na jira dawowarka. Ina matuƙar ƙaunarka, so nake maka mara musaltuwa Mustapha"
"Nima ina son ki Zeenat, kuma zan dawo mu yi aure mu haihu mu tara zuri'ar da za suyi alfahari damu"
Murmushi tayi, tare da ɗan rufe fuska.

Tayi kuka sosai tare dayi masa fatan alkhairi a lokacin da zai tafi.

_Bayan Wata Ɗaya_

Tana kwance tana barcin rana wanda ya zame mata jiki a yanzu, dan da yamma awara suke soyawa ita da Nabiha a ƙofar gida, da safe kuma suna Koko, hakan ya saka bata da lokacin isasshen bacci sai rana, dan da dare sai sun yi wanke-wanke sannan su tace gasarar koko kafin su kwanta, hakan ya sa basu kwanciya da wuri kuma su farka da wuri.
Jin kamar ana shafa gashin kanta ya saka ta buɗe ido a hankali, zumbur ta miƙe zaune, dan karo tayi da fuskar Ashraf.
"Ni za ki yiwa haka Zeenat? Wato so kike kiga bayana ko?"
A kiɗime ta miƙe daga zaune zuwa tsaye ta fara ja da baya
"Ba zan mutu ni kaɗai ba Zeenat sai dai mu tafi tare"
Runtse ido tayi tana ƙara ja da baya har sai da ta kai bango sannan ta tsaya "Allah baya barin azzalumai Ashraf" Ta furta tana haɗe jikinta guri ɗaya.
"Hahaha! Ke har akwai azzalumin daya wuce ki Zeenat? Duk wanda na kashe a dalilinki na kashe, kuma alhakin hakan na kanki sannan zan..." Bai ƙarasa ba, ita kuma bata buɗe ido ba. Sai kawai ji tayi Nabiha na faɗin "Mene ke faruwa Adda?" A hankali ta buɗe idanunta ta sauke inda Ashraf yake amma kuma sai taga wayam. A gurin ta sulale tare da fashewa da kuka. "Kin sake ganinsa ne?" Kai ta gyaɗa alamar eh.
"Kiyi addu'a Zeenat insha Allah kin fi ƙarfinsa"

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now