Page 15

89 5 1
                                        

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 15

Wayar na kunnenta fuskar nan sam babu annuri a cikinta.
"Husna wallahi ban jin zan iya yi masa magana, ni yana shigowa ma naji wani baƙin ciki ya kuma turniƙeni"

Daga ɗayan ɓangaren Husna ta ce "Karki yarda ki raga masa, ke namiji fa ba ɗan goyo bane, sai kin nuna masa dagaske sannan zai dawo hanya, idan kuma ba haka ba wallahi kina nan za ayi babu ke, ni fa gani nake baƙin ciki yake karki zo ki wuce shi a karatu shiyasa yake ta wani 'yan fuzge-fuzge."

"Aikuwa zai yi ya gama dan na rantse akan karatun nan sai dai ya sake ni"

"A'a Hidaya ki dai bi a sannu, yanzu waye yake son saki, na waje na nema kuma ke da kika samu kina so ki yiwa kanki sakiyar da ba ruwa."

"Hmm ba zaki gane ba Husna, aure fa babu wani abu a cikinsa face wahala, ke ni wallahi rayuwar 'yammatan ci tafi daɗi, amma yanzu ka ji da 'ya'ya ka ji da ubansu, ni wallahi gabaɗaya dana sanin aure nake"

"Ke dai naki mijin ne baki dace ba, yana da taurin kai na lura, sai kin yi dagaske wallahi"

"Hmm aikuwa mu zuba mu gani dan wallahi ni ɗinma ba kanwar lasa bace"

"Kar dai ki nemeshi sai ya nemeki dan ya gane ke ɗin mai daraja ce kuma mai tsada"

"To ƙawata insha Allah hakan zan yi"

"Yawwa to sai anjima"

"Allah ya kaimu."

Tana katse wayar ta kalli Aryan ta ce "Ina Daddy ɗin naku?"
"Yana room ɗinsa" Taɓe baki tayi kawai.

                **** **** ****

"Ba zai yuwu ba gaskiya akan me?" Saratu ta faɗa tana haɗe rai
"Mene ba zai yuwu ba, ban gane ba"
"Ba zan iya yarda ina gani a salwantar da rayuwar Ablah"
"Aure ne salwantar da rayuwa?"
"Eh mana duk ɗaya, saboda dududu yaushe tayi girman da za a mata aure, kuma a tafi da ita garin da bamu sani ba, Magajiya ba haka muka yi dake ba, ba zan taɓa yarda ba gaskiya"
"Aikuwa dole ki yarda, dan tun tana ciki na ƙudurta a raina zan samu kuɗi da ita, ko kin manta yarjejeniyar da muka yi da uwarta?"
"Ablah fa mutum ce kamar kowa, sannan tana da larura, ya daga haɗuwa da mutum kawai haka nan ba siɗi ba saɗaɗa ya ɗauki har naira miliyan biyu ya bayar, a taƙaice siyanta ya yi fa"

Zama Magajiya ta gyara sannan ta ce "To bari kiji, an kaita gurinshi a hotel ta kwana biyu, yaji zaqinta da garɗinta sai yaga gara ya aureta ya zauna da ita yana morar kayanshi."
Baki ta saki sannan ta ce "Gurin namiji fa, Ablah ɗin? Magajiya daga kawota naje Abuja sai ki kaita gurin maza, nawa Ablah take, ko ƙirgen dangi fa yanzu ta fara"
"Ke ma daga haka kika fara, saboda kina shekaru sha biyar na saka aka mayar dake cikakkiyar mace"
"To itama Ablah a bari ta kai haka, ba zai yuwu ba"
"Zan ga abinda zai yuwu tsakanin maganata da taki"

Miƙewa Saratu tayi ta fita, magajiya ta biyota, Ablah na zaune kan tabarma ta takure guri guda.
"Ta so mu tafi Ablah" Saratu ta faɗa tana kallonta.
"Ko kin ɗauke ta kun tafi dole ki dawo min da ita, saboda na yanke hukunci a kanta kuma da zarar ya dawo dole ki kawo ta"

Saratu dai bata ce komai ba ta kama hannun Ablah suka fita.

"Lallai yarinyar nan wallahi dani kike zancen, ina raga miki ne kawai saboda ba ƙananun kuɗi kike kawowa ba."

                        ***** *****

Kallonta tayi fuskarta babu walwala sam, ta haɗe hannaye tare da faɗin "Na roƙe ki da girman Allah Hajar"
Murmushi Hajara tayi sannan ta ce "Babu abinda za kiji daga gareni, ai da ni 'yar iskarki ce, sai yanzu da kike neman abu a gurina shi ne kika san ki kwantar da kai, kin san ko da a bariki muka sameki ai mun girmeki a haife"
"Eh na sani, amma ni dai dan Allah kiyi haƙuri na roƙeki da girman Allah"

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now