*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 27
Kamar an mintsineshi haka ya miƙe tsaye a kiɗime. Sabir kallonsa ya yi ya ce "Lafiya Nabil?"
Bai masa magana ba kawai ya fara ƙoƙarin fita.
"Baka da lafiya fa Nabil"
"Lafiya ta lau" Ya furta a fusace.Suna sauka parlour ya sake dakatar da ita. "Nabil wai ina kake ƙoƙarin zuwa?"
Kallonsa ya yi, sai da yaji zuciyarsa ta tsaya na wucin gadi saboda yadda yaga idanunsa sun canja sun yi jajir, ga kuma jijiyoyin ko wace gaɓa ta bayyana tayi kore shar. Da sauri kuwa ya sake shi, shi kuma ya fita.Sabir cikin tashin hankali ya fara kiran Mom.
***** *****
Har ya fara cin abinci ya kalleta ya ce "Na ji gidan shiru ina yaran?"
"Sun tafi gidan Mama ka ga yau ba islamiyya kuma suna cikin hutu shi ne nace su je su yi weekend ɗinsu a can."
"Ablah fa? Ko har da ita aka tafi?"
Ɗan taɓe baki tayi sannan ta ce "A'a cewa tayi ba za ta je ba, tana can ɗaki ka santa ba son zama take a waje ba"Har zai yi magana kawai yaji an bango ƙofar falon an shigo, ganin matashin namiji ya saka suka miƙe gabaɗaya. Ita ta gane ko waye saboda har yanzu tana jin ɗan fargaba idan ta tuna, shiyasa sam bata sakaci da addu'a. Shi kuma Mustapha karo na farko daya fara ganinshi.
"Lafiya ka shigo gidan mutane babu ko sallama?"
Bai ko kalli inda Mustapha ya ke ba, kai tsaye ya fara dosar inda ɗakin Ablah yake.
"Malam ina zaka je" Mustpha ya furta yana ƙoƙarin tafiya, Nabiha tayi saurin riƙeta, a fusace ya kalleta ita kuma a tsorace ta fara girgiza kai.
"Ki sake ni, ya namiji zai shigo har gidana kuma yana dosar inda ɗakunan baccinmu suke kice na ƙyaleshi.?"
"Ash...Ashraf ne"
"Wane Ashraf? Ashraf ɗin ne nake gani kike gani?"
"Wallahi shi ne, ranar ma shi ne ya shaƙeni"
"To kuma idan ya cutar da Ablah fa?" Ya furta yana fuzge hannunsa ya nufi ɗakin shi ma.
"Abban yara ba zaka iya dashi ba"Yana zuwa ƙofar ɗakin bugu ɗaya ya mata ta ɓalle, ya shiga, idanunta har sun fara zjuyewa bakinta yana fitar da farar kumfa, numfashi kawai take ɗai-ɗai domin tuni ta fara fita hayyacinta.
Ɗagota ya yi, yana daga zaune ya fara danna cikinta, idanunta suna kanshi shi ma kallonta yake da idanunsa da suka koma jajir tamkar garwashi.
"Ba zan bari ki mutu ba Ablah" Ya furta da wata iriyar murya mara daɗin ji.Mustapha daya shigo cak ya tsaya. "Mene haka? Me ke faruwa?"
Lokacin ma Nabiha ta shigo, a tsorace take kallon Ablah da take fitar da farar kumfa daga bakinta.
"Ku kawo manja, ku hanzarta"Ba wanda ya motsa, kallon Nabiha ya yi ya ce "Ɗauko manja a kitchen kiyi sauri mana"
"Me mene?" Ta furta a ruɗe.
"Nabiha manja za ki ɗauko ko so kike ta rasa ranta"
Sai lokacin ta dawo hayyacinta, tayi saurin zuwa kitchen ta ɗauko gaba ɗaya jikar man tare da kofi.Tana zuwa taga Mustapha a tsugunne gaban Ablah kusa da Nabil da take gani a matsayin Ashraf. A tsorace ta ajiye jakar a gabanshi, Nabil ɗin yaja robar ya buɗe tare matse bakinta ya fara ɗora mata, tana gama sha ba'ayi mintuna ba kawai ta fara amai. Sai da ta amayo jik ɗin nan sannan kuma ta lumshe ido daga kwance, sai kuma hawaye ya gangaro mata ta gefen fuska. Janyeta ya yi, ya mayar da kanta ƙasa, ya ƙura mata ido sannan ya miƙe tsaye.
"Zaku iya kiran Likita, kuma idan baku kula da ita za ta iya kashe kanta saboda baƙin cikin da muguwar matarka take saka mata."
Runtse ido Nabiha tayi jin wata iriyar murya da bata yi kama data mutane ba.
"Waye kai? Kuma ya akai ka san hakan ta faru da ita, tunda ni na san Ablah ko waya bata riƙewa"
"Ni garkuwarta ne" Ya furta kuma sai a lokacin suka haɗa ido da Mustapha, tsorata ya yi, da sauri ya kauda kai. Shi kuma Nabil ya kwashe da dariya sannan ya wuce ya bar ɗakin suna tsaye duk sun kasa motsawa.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...