Page 38

138 9 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 38

Tare da ma'aikatan suka shigo, da ƙyar aka ɓamɓare hannunsa daga wuyanta.
"Ku fita Hajiya zamu masa allura"
"Dama yana yin haka?"
"Bai taɓa yi wa kowa ba, amma dama wasu lokutan ya kan yi ƙoƙarin jiwa kanshi ciwo."

Sun juya suna ƙoƙarin fita kawai suka ji ya ce "Ablah tafiya za kiyi kina kallo zasu min allura, dan Allah ki hanasu karki bari su yi min tana matuƙar cutar dani"
Jin haka ya saka ta juyo da sauri.

"Hajiya karki damu da abinda yake faɗa, kin dai san mahaukaci, kuma zai iya ƙara illataki idan kika tsaya."
"Kada ka ƙara kiransa mahaukaci" Ta faɗa cikin tsawa tana kallon Likitan, sannan ta ƙarasa gaban Nabil ɗin ta tare "Kada kuyi masa allura shi ba mahaukaci bane, idan har Nabil mahaukacine ba zai taɓa ganeni ba, matsalarmu iri ɗaya ce depression ne dan Allah ku bamu damar kai shi asibiti"
"To ke a suwa? Dole mu yi aikinmu"
"Dan Allah karkuyi masa allurar mahaukata" Ta sake faɗa tana kuka, da ƙarfin tsiya suka matsar da ita gefe, yana ta fuzgewa haka suka masa allurar. Suna gamawa Likitan ya kalleta "Idan ba a masa ba da yanzu ya kasheki ai, da ƙyar fa muka ƙwaceki"
Kallon Likitan kawai take kukan ma ya tsaya cak. Ya kalli masu aikin ya ce "Idan sun fita karku manta ku rufe ƙofar yanzu babu abinda zai iya"

Suna fita ta ƙarasa gurin Nabil da sauri, gabansa ta durƙusa Sabrina ma ta ƙaraso gurin. Jikinsa gabaɗaya rawa yake, bakinsa na kakkafa, ya kalli Ablah idanunsa a jujjuye.
"Saboda ke ne.... Ban sani ba ko sonki nake amma meyasa baki dawo ba sai yanzu da rayuwata ta lalace, kullum kasheni suke da wannan allurar idan suka min ji nake tamkarrrr...." Bakinsa taga ya tsaya cak. Zabura tayi, ta ƙarasa gaban kwalbar kasancewar ta ɗan karanci wasu magunguna da allurai da ake mata a Australia. Ɗagawa tayi tana karanta jikin kwalbar, ta sake kallon Nabil da har idanunsa sun lumshe a lokacin.

"Duk wanda keda sa hannu a abinnan wallahi ba zan barshi ba, sai na ƙwatar maka 'yanci, wannan allurar guba ce ba magani ba, Sabrina sa mana a jaka wallahi sai na kaisu ƙara. Ɗaukar  allurar tayi ta duba. "Kai...!" Ta furta tare da miƙewa tsaye.
"Ablah mu tafi" Ta furta tare da fuzgar Ablah.

Sabrina na driving Ablah kuma na gefe tana tuno irin maganganun da Nabil ya furta mata.
"Ina zan sauke ki"
"Headquater"
"Ta ina kenan?"
"Bompoi"
"Ablah ina nufin ina ne kike zaune na sauke ki, ba zai yuwu ki kai ƙara ba dole sai naje gida"
"Saboda me?"
"Saboda wannan abin ya shafi gida ne, bai kamata a kaiwa 'yan sanda ba, zan je nayi magana dasu Mommy"
"Ki faɗa min dalilin daya saka aka kai Nabil gidan mahaukata"
"Za kiji komai amma ba yanzu ba Ablah"
"Meyasa ba yanzu ba"
"Ki faɗa min inda zan sauke ki.

                  ***** *****

"Amma meyasa kika barta ta fita?"
"Ta dage min akan sai taje, shiyasa na barta"
"Amma ku san awa biyu da tafiyarta shiru babu ita."
"Kuma ta ce min ba zata daɗe  ba."

Sai lokacin Irfan ya ce "Fahad ko dai zamu je mu binciko ta,ni fa hankalina bai kwanta ba"
"Idan ma mun fita ta ina zamu fara Irfan? Ka haƙura ka..." Knocking ɗin da suka ji ya saka duk suka kalli ƙofar. Fahad ne ya ƙarasa jikin ƙofar ya buɗe, yadda suka yi tsammani kuwa itace.

Jiki a sanyaye ta shigo ɗakin, Irfan ya ƙura mata ido, yanayin tafiyarta da kuma yadda fuskarta tayi kalar tausayi sai ya ga kamar Zeenat ce a ranar daya fara ganinta.
"Ablah" Maganar da taji ne ya dawo da ita hankalinta, dan ta ɗauka ma Saratu ce ta buɗe ƙofar dan ta san ita kaɗai ta bari.
"Ina wuni" Ta furta tana ɗan rissinasa.
"Lafiya lau"
Kallon Irfan tayi shima ta gaidashi, amsawa kawai ya yi yana kallonta komai nata kamar na Zeenat har muryar, bai gane hakan ba sai a yau, ga baƙar abayar dake jikinta ta matuƙar yi mata kyau sai ya ganta kamar ba Ablah da ya yi jinya bace.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now