*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 23
"A'a Magajiya kar ayi haka dake" Aliya da ta ƙaraso gurin tayi maganar da sauri, duk suka juya suna kallonta. Ita kuwa Saratu idanunta ta kasa ɗauke su daga kan Magajiya. Gida fa ya ruɗe sai hayaniya ake, wanda basu san mene yane faruwa ba sai a lokacin ake labarta musu.
Ihu da hayaniya da shewa babu wanda babu a lokaci.
"Wallahi sai ta fito da Ablah shegiya muguwa mai baƙar aniya"
Magajiya ta furta rai a ɓace."Ke 'yan sanda nake gani fa" Aziza ta faɗa tana kallon Ashanty.
"Wallahi sune" Ai tana rufe baki taga yawan nasu, dan haka tayi ƙoƙarin tserewa ta ɗayan ɓangaren, sai dai ina sai da aka cafketa.Ranar dai kamar an masu shune, domin kusan fin rabin wanda ke gidan an kamasu, wasu kuma sun tsere. Magajiya dai babu halin gudu dan haka tsayawa tayi aka kameta gabaɗaya haka aka watsasu a manyan motoci har uku da aka kawo, tuni aka wuce dasu dasu cell wanda aka tanada lokaci zuwa lokaci saboda karuwai.
Lumshe idanunta tayi, taji wasu hawaye masu zafi suna zubo mata, mayafinta taja ta rufe fuskar saboda karuwan sun dameta da surutu.
***** ***** ******
"Yau wata guda kenan ana yi muku lakca anan, zuwa yanzu na san da yawa daga cikinku sun gane illar abinda suke aikatawa, kuma ina fatan zaku nutsu ku koma gidajen iyayenku ku samu miji kuyi aure. Wanda kuma basu da kowa, mu zamu ɗaukeku mu riƙeku a hisba har ku samu mijin aure.
"Ni wallahi ba zan je Hisba inyi rayuwa mara 'yanci ba" Fahima ta faɗa tana murguɗa baki.
"Zamuje daku ko wacce ta ɗebi kayanta, sannan zamu baku dubu goma-goma ku shiga mota, zamu baku lambar waya idan mun tabbatar kun koma gidajen iyayenku kun nutsu zamu kawo muku ziyara tare da baku jari, ga wanda suke buƙata ko neman mijin aure ƙofa a buɗe take, mu dai fatanmu ku shiryu ku zama mutane na gari domin ku mata ne kuma iyayen al'umma"
Kuka sosai wasu suke, tare da tsantsar dana sanin shigarsu rayuwar karuwanci rayuwa mara aji. Sai dai ita Saratu ta rasa me za tayi, kuka ko kuma me? Kawai matan dake ta surutu a gefenta take sauraren, suna faɗin za su koma gidajen iyayensu su roƙesu gafara, wasu na faɗin za su koma ga danginsu, ita kam bata da ko ɗaya a hisba za ta zauna ko kuma a ina? Tambayar da ta kasa bawa kanta amsa kenan.
_Zamana a garin nan babbar barazana ce ga rayuwata._ Shi ne abinda ta furta a ranta, dan a tunaninta ko da ta zauna a Hisba kawai zata rayu ne a ƙuntace domin bata saba ba, ita kuma bata da wani buri a yanzu daya wuce ta nemi kuɗin da za ta gyara fuskarta, kawai lgos ce ta faɗo mata, dan haka ta saka a ranta can kawai za ta nufa ta kama 'yan kuɗaɗenta.
A farfajiyar gurin masu ƙawaye sallama suke tayi da juna, ana ta 'yan koke-koke.
"Magajiya jikina gaba ɗaya yana bani yarinyar can itace tayi miki shune" Hajara ta furta tana gyara tsayuwa.
"Ai yarinyar nan ba ƙaramar muguwa bace, na rantse da Allah sai ta gane kurenta, kaɗan ta gani"
"Yanzu dai meye abinyi, ga dukkan alamu fa akwai wanda har yanzu basu shiryu ba, me zai hana mu ɗanje a janyosu, kin ga sai a kisu wancan gidan dana gina kafin ki samu ki karɓi naki gidan"
"Aliya ke kina ganin gidana zai karɓu ne? Ai ni kam an gama ruguza rayuwata tattaƙin arziƙina abinda nake samu nake rufawa kai asiri amma tsabar rashin mutunci an kawoni an haɗani da yara sannan gidan da nake taƙama dashi an ƙwace.""Gashi wancan Guy ɗin sai damuna yake akan cikon kuɗinsa, shi fa motarsa ce kawai aka yi amfani da ita da kuma murya amma ya dameni wallahi"
"Duk damunsa kuwa ai dole yayi haƙuri ka samu a kwakwaso kuɗin kafin a bashi ko"
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...