Page 44

211 8 2
                                        

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 44

Irfan kallonsa kawai yake cike da mamaki kafin ya ce "Kai kuma?"
"Eh, domin tun Ablah tana ƙarama nake da burin aurenta sai dai Allah bai yi ba har yanzu"
Ajiyar zuciya Irfan ya sauke tare da faɗin "Tabbas kai mutumin kirki ne, kuma ina girmama duk wanda Ablah ta kawo min a matsayin mutumin daya taimaketa a lokacin da take buƙatar taimako, kuma kaima kana ɗaya daga cikinsu. Sai dai abu ɗaya zuwa biyu zai saka naƙi baka Ablah"
"Wane abu kenan?"
"Ablah tana da larura da take buƙatar wani kusa da ita a koda yaushe kai kuma mutum ne mara zama guri ɗaya, abu na biyu kuma kana da mata, wannan sune manyan dalilaina"
"Zan yi ƙoƙarin tafiya da ita duk inda zanje"
"Hakan ba abu ne da zai ɗore ba, dan Allah kayi haƙuri, kayi haƙuri ka riƙa kallon Ablah a matsayin ƙanwarka koma mahaifi gareta"
Duk yadda yaso ya masa bayani amma abin ya faskara a ƙarshe dai haƙurin ya yi, sai dai ya roƙi alfarmar ya bar Ablah a Nigeria sai dai ya ce zai yi magana da Ablah ɗin.

*1 year later*

Ganin tana ta bin ta da ido ya saka tazo kusa da ita tare da kara hannunta a fuskarta. Murmushi tayi gami da sauke ajiyar zuciya.
"Ya dai?"
"Kawai kyau kike min"
"Ni ɗin?"
Kai ta gyaɗa tare da faɗin wallah Aunty ke ɗin masha Allah"
"Kai Ablah ni dana wuce talatin duk na tsufa"
"Ba wani tsufa Aunty, kin ga da fuskarki ta da, data yanzu duk fa gwanin sha'awa"

Zama tayi kan gadon ta tanƙwashe ƙafa tare da kai hannayenta haɓa. "Ke alheri ce a gareni Ablah, ina matuƙar godiya gareki da kuma mahaifinki dama 'yan uwanki da duk suke nuna min ƙauna tun da aka kawo ni har zuwa yanzu, babu wanda yaji ƙyanƙyami na"
"Aunty kenan, kin kasa gane kece rayuwata"
Murmushi tayi tare da faɗin "Na sani Ablah."
"Amma wallahi ina son zuwa Nigeria Aunty"
"Na san baya wuce saboda ki ga Affan ko?"
"Ai shi muna video call, ni kawai ina son zuwa naga halin da Nabil ke ciki, bana so nace Uncle ya duba min na fi so naje da kaina, sannan kuma ina so naje na gaida Abba na kuma ga 'yar uwata Hamdiyya"
"To idan Abbanki ya dawo ki faɗa masa mana"
"Zan sake faɗa masa, amma shi idan ina faɗa wai sai ya ce ba yanzu ba"
"Ki cigaba da naci zai amince"
"To shi kenan, amma ni na lura Daddy baya so na matsa daga kusa dashi ne kuma yanzu ba zai iya zuwa Nigeria ba dan aiki ya masa yawa anan, amma ni na gane, saboda  Aunty Diana babu yadda batayi ba ta ɗaukeni ko sati biyu nayi amma yaƙi yarda"
"Nima ai na fahimci haka"
Murmushi kawai tayi tana faɗin "Idan yaƙi sai na haɗashi da granny"
"Ƙarar Abban naki za ki kai"
Dariya tayi tana sauka daga gadon.

*07:00pm*
_Austrilia_

Ana turo ƙofar ta gane shi ne dan hakata ƙara haɗe fuska tare da sunkuyar da kai.
"Baby wai fushi kike dani shine ana dinner kika taso kika dawo nan?"
Bata bashi amsa ba, ba kuma ta kalleshi ba.

Ya ƙarasa gefen side drawer ya zauna.
"Kuka kike" Ya furta da mamaki.
"Ina son ganin halin da Nabil yake"
"Nace miki Fahad zai je, idan ma kina so har video call sai kuyi dashi"
"Abba ina so naje Nigeria ne, akwai Abba bayan Nabil, akwai Hamdiyya, sannan akwai ƙawata Salma duk ina so na gansu, dan Allah Abba"

Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin "To naji, amma ki bari na samu takardar izni daga asibiti sai mu tafi tare"
"Abba iya ni da Aunty Sarah ma fa zamu iya suwa mu dawo"
"Gaskiya ba zan yarda ki tafi ke kaɗai ba tun daga nan har Nigeria"
"Amma wancan karon ni kaɗai na tafi fa"
"Shi ma dan ban san ke 'yata bace, kuma a hakan ma kin ga ai sai dana haɗaki da Fahad nace ya tabbatar ya kaiki har gida"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 29, 2024 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now