*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 11
Gidan da za a kaita a matsayin amarya nan ya yada zango. Bayan ya yi parking motarsa a wurin ajiye motaci tare suka fito suka jera zuwa cikin gidan.
Har za ta zauna a parlour ya ce "Taso mu shiga ciki Babe a matse nake"
Bata musa masa ba haka ta shiga ya rufe ɗakin da key._1 Hour Later_
Daga toilet ya fito yana ɗaure da towel a ƙugu, ita kuma tana kan gadon jikinta lulluɓe da blanket, idanunta a rufe suke.
"Babe ba dai bacci kike ba?"
A hankali ta buɗe idanunta da take jin alamun bacci ta kalleshi "Wallahi bacci nake ji" Shi ne abinda ta faɗa a hankali. Murmushi ya yi ya ƙarasa gaban mirror ya ɗauki mayuka yana shafawa dan already ya kawo kayanshi gidan. Sai da har ya saka kaya sannan ya je gefen side drawer daga side ɗin da take kwance akan gadon ya zauna.
"Da na san haka aure yake da daɗi da ban azabtar da kaina ba wurin jinkirta nawa auren, ko dan, wataƙila dan na haɗu dake shiyasa Allah ya jinkirta min." Murmushin yaƙe kawai tayi, dan ta san Irfan farin shiga ne a harkar, ba dan kar ya gano ta san maza ba da ta ce ita bata gaji da kasancewa tare dashi ba."Amma salonki tamkar ba farin shiga a aure ba" Ya furta idanunsa a kanta, itama shi take kallo.
"Mene sirrin?" Kunya kawai taji ta rufeta dan haka tayi saurin tura kanta cikin blanket ɗin "Ki fito ko na yaye ki duka?"
"No haba Irfan"
"Idan baki so to ki fito mu yi magana"
Dole ta saka ta fito dan bata so ya cire blanket ɗin daya zama shi ne abinda ya ɓoye surar jikinta.
"Zeenat ban san mata ba, ban taɓa neman mata ba, ba zan gane virgin da kuma wadda ba virgin ba, amma na rantse da Allah ni ba manemin mata bane, kuma yau ne karo na farko dana fara sex da mace wadda kece kuma a matsayin matata kike, ban kusanceki ba har sai dana biya sadaki, kuma shaidu suka shaida ɗaurin aurenmu" Kallon shi kawai take bata ce komai ba "Ina so ke ma ki rantse min cewar ke virgin ce ni ne namijin farko da kika sani" Ji tayi gabanta ya yi wata muguwar faɗuwa, ta fara ganin wani duhu-duhu a idanunta. "Ki faɗa min gaskiya ta hanyar rantsuwa kamar yadda nima na rantse miki."Wata dubara ce ta faɗo mata, dan haka tayi saurin miƙewa, ranta a matuƙar ɓace kamar wadda aka aikowa saƙon mutuwa. Ganin zata ɗauki kaya ta saka ya sashi saurin kai hannu ya riƙe "Me kuma ya faru?"
"Gida zan tafi"
"Amma naga kamar ranki a ɓace, kuma gashi ko wanka baki yi ba, a haka za ki tafi?"
"Eh saboda bani da amfani a gurinka, kenan baka yarda dani ba tunda har zaka ce sai na rantse maka akan gaskiyata" Sai kuma ta fashe da kuka. Rungumeta ya yi tare da faɗin "Am sorry Babe wallahi ba haka nake nufi ba."
Langwaɓewa tayi jikinsa, tasha kuka wanda da gaske na takaicin budurcinta ne da ta ɓarar a baya, bata taɓa tunanin a talaucinsu zata auri mai kuɗin da zai so ta domin Allah ba, musamman yadda taga idan sun zo ƙarara suke nuna mata lalata suke son yi da ita.Sun daɗe a haka kafin daga bisani ya lallaɓata taje tayi wanka ta shirya sannan ya mayar da ita gida.
Babu wanda ya gane ta fita kasancewar yau ake yinin biki gidan shaƙe yake da 'yan'uwa da abokanan arziƙi.**** **** ****
Murmushi ya yi yana shafa sajensa kafin ya ƙara gyara kwanciyar da ya yi. "Ango kwanciya fa ba taka bace"
"Fahad naji daɗi sosai ashe haka aure yake?"
Murmushi Fahad ya yi tare da faɗin "Yanzu dai ka samu lafiya ka rage shan lemon tsami da kuma magunguna da allurai saboda ciwon mara."
"Kuma ka san yawan shan magani ma baya da amfani musamman na bature."
"Hakane, dan in ka zama addicted to zai daina maka amfani kwata-kwata"
![](https://img.wattpad.com/cover/351344300-288-k542301.jpg)
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Ficción históricaƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...