Page 33

139 7 0
                                        

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 33

"Hakane domin magungunan ciwon suna da tsada sosai, idan kuma aka ce aiki za a mata to gaskiya zai zama risk, ta yuwu ta tashi ko kuma ta rasa rayuwarta gabaɗaya, a shawarce gara a ɗorata kan magani"
Dukkansu an rasa mai cewa komai, har sai da ya ce "Za ku iya zuwa kuyi shawara daga nan zuwa kwana biyu"
Miƙewa suka yi duk jikinsu babu ƙwari.

"Wannan shi ake kira dala  ba gammo, yanzu mene abin yi?" Sabrina tayi maganar tana kallon Nabil.
"Ban sani ba, kaina ya kulle"
"Ina fatan ba sanadina ta samu ciwon nan ba"
Bai ce mata komai ba, suka wuce ɗakin da aka kwantar da ita.
"Nabil anya wannan ba 'yar india bace ko shuwa arab, ka ga gashi har tsakiyar baya, kuma a kwance baƙi ƙirin" Sabrina ta faɗa lokacin data ƙarasa gaban gadon. Shi ma kallon Ablah ya ke da ta juya baya tana barci, tsakiyar kanta an yanke gashin ƙwal anyi ɗinki a gurin inda ta bugu a ƙasa.
"Sabrina ina zamu samo 20M?"
"Taɓ ai wallahi babu, kawai ka san me zai faru?"
"Sai kin faɗa"
"Kaje ka faɗa a gidansu ga halin da take ciki sai su san abinyi"
"Ina za su samu wannan kuɗin? Ga uwar ta saka uban a gaba ta hanashi sakat, na kira numbersa ko ɗazu muna gida wallahi bama ta shiga"
"Aikuwa indai hakane akwai matsala, dan ka ga dai daga kai har ni babu mai aiki, kuma ni wallahi kuɗin account ɗina ko 5M basu kai ba, ai in ba gadonmu za ka haɗa ka sayar ba, babu inda za ka samu wannan kuɗaɗe masu ubn yawa, kuma ka ga dai takardun gidaje da filaye duk suna gurin Yaya Salim"
Lumshe  ido kawai ya yi bai sake cewa komai ba.

_A Month Later_

Tura ƙofar ya yi a hankali ya shiga. Tana kwance a gadon kamar ko wace rana idan idanunta a buɗe yake sai dai kawai aga hawayen na fita ta gefe da gefe amma sam bat magana. Zama ya yi a gefen gadon, ya ƙura mata manyan idanunsa. Hannu ya saka ya share mata hawayen ta bishi da ido kawai da alamu sai lokacin ta san ya shigo.
"Insha Allah sai kin samu lafiya, zan yi komai dan tabbatar da hakan Raina Fansa ne a gareki Ablah, ban san meyasa ba ni dai naji kawai ina son taimaka miki, kuma zan iya komai dan tabbatuwar haka, kiyi haƙuri tsawon lokacin da aka ɗauka ba a tafi kaiki magani ba, bamu da kuɗin a hannu dole sai daya ɗsukemu lokaci wurin sayar da kadara, amma nesa tazo kusa, an gama miki komai, jibi insha Allsh dani dake zamu tafi Australia domin nema miki magani"
Bakinta ta motsa, tana son yin magana amma ta kasa.
Miƙewa ya yi yana kallonta ya fita.

Kai tsaye office ɗin Dr ya je.
"An gama tsara komai, zaku bi flight ɗin ƙarfe 12:30am, amma ba tare zaku tafi airport ba, daga nan ita za a kaita, tunda ga passport ɗinta da komai, idan kunje ƙasar ma, ma'aikatan asibitin sun san yaushe jirginku zai yi landing, za su ɗauketa su kaita asibiti, kai daga nan ba zaka same ganinta ba sai a asibitin, wannan takardar dana baka ita za ta tabbtar musu da kaine ka kawota kuma kaine da alhakin sanin duk abinda zai faru da ita acan ko da kuwa basu buƙatar ɗan jinya to kai dai za ka kasance a tare da ita ko wace rana"
"Ok Dr sannu da ƙoƙari na gode Allah ya saka da alkhairi, yanzu daga nan ma idan na tafi ba zan dawo ta asibitin nan ba zan wuce Airport kawai"
"To shi kenan, Allah ya bata lafiya"
"Amin ya Allah"

                  **** **** ****

Tun a parlour ya lura da irin kallon da Mom ke masa, amma dai ya ma ze ya wuce bedroom ɗinsa kawai, ya shirya kayansa tsab ba tare da kowa ya sani ba, ya shiga wanka ya fito ya shirya tare da zira jallabiya,  komawa toiletɗ in yayi dan ya ɗora alwallah, yana ciki yaji alaman an shigo sai daya gaba sannan ya fito dan ya yi tunanin ma Sabrina ce ta shigo, amma yana fita yaiske Salim Mommy Salim da kuma Najma.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now