Page 31

114 5 1
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 31

Kamar daga sama taji ana faɗi tashi muje, a hankali ta buɗe idanunta da suka mata nauyi, ta saukesu kan ɗan sandan daya ke tashinta daga doguwar sumar da tayi.

Zaune ta miƙe tana ƙarewa ɗan ƙaramin cell ɗin da ko iya miƙar da kafafunta ba za tayi a ciki ba.
"Tashi muje anzo ganinki, shu'umar yarinya gashi ko ankwa idan an saka ba riƙe hannunki za tayi ba zamewa za tayi, ga nakasa amma sai iskanci, shiyasa da Allah ya miki kyau sai ya gundule shegun hannuwan, ke wannan da kina da hannu ba a san me za kiyi ba"
Kuka kawai take tana kallonsa. Haka ya tasa ƙeyarta har ofishin  DPO

"Ablah haka kika koma? Ko suna dukanki ne?" Ya furta ya ƙare mata kallo, fuskarta tayi duhu da ƙananun ƙuraje, ga kuma wata irin zugewa da tayi, hakan kuma bai hana fuskarta yin ja ba.
"Ai dole mu dake ta ko dan ta gaya mana gaskiya."
"Amma Yallaɓai ai kana ganin tana da lurara ko, sannan ba fa kisan kai tayi ba"
Sai lokacin ta fahimci mai maganar saboda muryarshi da taji.
"Uncle, ina Hamdiyya an ganta?"
Shiru ya yi yana lumshe idanunsa dan zafi sosai yake ji a ransa.

*_Abinda Ya Faru A Baya_*

Nabil ne ya fara matsawa inda take ya ɗauki wayar, hakan ne ya saka ta miƙe a fusace ta kalleshi "Ina Hamdiyya?"
"Ban sani ba, tare fa muke da ke"
Kuka ta fashe tare da faɗin "Wallahi da saninka aka ɗauketa saboda kai ka janyo ni ka mayar baya, na shiga uku"
"Taya zan saka a sace mutum? Mene ribata idan nayi hakan?"

Sabrina ce ta dafata tare da faɗin "We are very sosai Ablah, mun san a nan 'yar uwarki ta ɓata kuma a dalilinmu, amma insha Allah ma yanzu za ki ganta.
Amal da fa ƙaraso gurin tambaya take lafiya?
"Muna tsaye anan kawai sai aka yi offing lights ɗin gurin nan gabaɗaya, wai haske na dawowa muka neme sister ɗinta ko sama ko ƙasa"
Mamaki Amal tayi sosai kafin ta ce "Inajin dai fita tayi"
"Da farko muma hakan mukayi tunani, amma daga baya sai muka ga wayarta a ƙasa.

Abu dai kamar wasa har shaɗaya na dare babu Hamdiyya babu labarinta, dole suka je station na kusa da gurin suka yi reporting sannan suka mayar da Ablah gida.
_Me zan faɗawa Abba? Meyasa tun farko na biyewa Hamdiyya muka yi ƙarya?_ Shi ne abinda take faɗa a ranta.
"Zamu shiga muyi masa bayani Ablah." Nabil ya furta yana kallonta, Sabir dake driving ya ce "To ai dole ma mu faɗa, saboda case irin wannan babban abu ne, ni addua ma nake Allah yasa ba aljanin ne yazo ya saceta ba"
"Kai ana maganar hankali kana kawo shirme a cikinta.
"Wallahi da gaske nake"
Sabrina ta ce "Kun ga dan Allah abar maganar, kai kuma Sabir kama daina faɗar haka kar ka ƙara ɗaga mata hankali"

Ita dai bata ce komai ba har suka isa parlorn gidansu.
Sabrina ce ta murɗa handle ɗin suka shiga gabaɗaya. Nabiha da Mustapha duk suna zaune a parlor, suna ganin shigowarsu gabaɗaya suka miƙe.
"Ablah daga ina kuke tsawon wannan lokacin?"
Shiru tayi ta sauke kanta ƙasa.

Nabiha kuwa sai data ƙare musu kallo tas sannan ta ce "A ina kika baro Hamdiyya?"
Jin haka ya saka ta fashe da kuka, a kuma gurin ta durƙushe tana kukan hakan ya ƙara ɗaga musu hankali musamman Nabiha.
Nabil da kanshi ya faɗa musu yadda ya gayyace su birthday ɗinshi da yadda ita Ablah tayi ta damun Hamdiyya kan su tafi gida da kuma yadda Hamdiyya ta ɓata.
"Ba komai nima bari naje nayi reporting. Suna fita kuwa Nabiha ta rufe Ablah da duka, yana shigowa ya tarar da hakan da ƙyar ya ƙwaceta.
"Nabiha wai mene haka?"
"Kamarya? 'yata ta ɓatar fa?"
"Hakan da kike yi shi ne zai saka a gano inda Hamdiyya take? Karki manta itama Ablah ai 'yarki ce, ko za ki daketa ba irin wannan dukan ba, idan kuma hukunci ne ai dukkansu zamu haɗa muyi musu tunda mu dai basu faɗa mana za su je birthday party ba, biki suka ce kuma ita Hamdiyya ai itace mai cewa bikin ƙawarta ne"
"Hmm ita Hamdiyya ina take da wannan plan ɗin, ita Ablah ita zata kitsa mata, haka kurum na yiwa yarinyata tarbiyya wata banza da tayi rayuwar karuwai zata ɓata min, wallahi ba 'yar Zeenat ba ko 'yar waye sai ta faɗa min inda ta kai min Hamdiyya"

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now