Page 17

73 6 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 17

"Nabiha bakinki ne yake faɗar wannan kalamin?"
Shiru tayi tana ƙara haɗe rai, shi kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "A tunanina ko wani ne ya faɗi haka za kiyi faɗa dashi dan ganin kin kareni, amma sai gashi ke da bakinki kina faɗar haka"

"Ni kuma a tunanina ko mene indai har aka ce na Zeenat ne zaka ƙyamace shi amma sai gashi har ka fini tarairaya, ai akwai aure a tsakaninku idan har ka sakeni, shiyasa ma na fara tunanin haka"

"Ni gani nayi ɗiyar 'yar uwarki ce, kuma itama kamar 'ya take a gurinki, kuma 'ya'yanki ai kamar 'ya'yana ne."
"Ban da na Zeenat Abban Yara, macen da ta wulaƙantaka, ta ƙyamaceka, wallahi naso Zeenat na raye tazo ta ga yadda ka koma, ka wadata ka samu nasarori a rayuwa, kasuwancinka sai ƙara haɓaka yake, naso tazo a ƙasƙancenta na nuna mata iyakarta ta kuma gane cewa ba a raina matsayin wani"
"Nabiha duk ki daina wannan maganar, saboda ita kam ai ta-ta ta ƙare sai dai mu bita da fatan samun rahamar ubangiji, kuma 'yarta ni ba zan wulaƙanta ta ba saboda bata da laifi, ba ita tayi min laifi ba, kuma lokacin da akayi bata nan bata san anyi ba ba ta zo duniyar bama"
"Ni dai na faɗa maka babu ruwanka, ka barni da ita kawai, kuma ban yarda ta ƙara shiga ɗakin mijina ba"
Da sauri ta miƙe ta wuce ɗakinsa shi kuma ya rufa mata baya.

Tana shiga ta saka hannu ta ɗalawa Ablah duka, aikuwa zubur ta miƙe a tsorace "Sakko, kin samu guri kin wani baje"
"Wai Mamin Yara mene yake damunki"
"Ciwon hauka, wallahi idan naga dama sai ta bar gidan nan, ai akwai dangi"
"Amma naga ai kin fi kusa da Zeenat ko?"
"Ai bata ɗaukeni haka ba ita" Kallon Ablah tayi sannan ta ce "Wuce dalla muje"
Da sauri Ablah ta sauka daga gadon, Nabiha ta tisata gaba har parlour.

"Anan nace ki zauna idan kuma ba zaki zauna ba" Ta ruƙo mata kunne wanda har sai da ta cije laɓɓanta. "Idan na ƙara cewa ki zauna a guri kika tashi to sai na yanke kunnenki ɗaya, nan ba bariki bace, ba gidan karuwai bane kinji ko?" Kai kawai ta gyaɗa dan masifar tsoron Nabiha take tun jiya da tazo taga tana mata faɗa da kallon banza.

Ɓangaren Mustapha kuwa bai fito daga ɗakin ba, anan ya kwanta dan shi ma ya ɗan ƙara matsewa kafin ya fita kasuwa.

*07:15am*

"Wannan naku ne, wannan kuma ki kaiwa waccan musakar yarinyar."
"Mami wai Haidar ya ce anan za ta cigaba da zama?"
Shiru Nabiha tayi kafin ta ce "Eh anan za ta zauna"
"Gaskiya mu dai tsoron hannunta muke Mami"
"Babu abinda zai muku"
Kwaɓe fuska tayi.
"Kin ga ai bance a ɗakinku za ta zauna ba, za a fita da ita wancan ɗakin kinji"
Kai ta gyaɗa, sannan ta wuce.
"Hamdiyya kuyi sauri saboda school"
"To Mami."

Tana zuwa gaban Ablah ta dungurar da robar. Ablah kuwa tana kai dubanta ga abincin ta zabura tare da matsawa baya.
"Mene wannan?"
"Oho" Hamdiyya ta faɗa tare da wucewa.

Indomie'n take kallo, 'yar kaɗan a cikin robar bai fi tayi fork biyu ko uku ba, sai kai da ƙafa da wuyan kaza, abinda ya tsorata kenan, dan ita bata taɓa gani ba, ita tunda take cin nama bata taɓa ganin kai da ƙafa ba, dan tayi tunanin kan ma mai rai ne shiyasa har ta zabura tayi baya.

Dungulmin hannunta ta saka tana goge hawaye da suka fito mata, ta ajje glass ɗinta a gefe ta cigaba da rera kukanta mara sauti, a haka har Nabiha ta gama kintsa kitchen ɗin ta fito.

Hamdiyya, Haidar da Aslam suna dinning area suna karyawa sai Ablah dake zaune tsakiyar parlour tana kuka. Kallon Ablah tayi sannan ta ƙarasa inda take "Mene kike kuka?"
Ɗagowa tayi ta kalleta "Ina son ki kaini gurin Aunty Sarah"
"Aunty Sarah?" Ta maimaita, ita kuma ta ɗaga kai alamar eh "To ai ni ban ma san wacece haka ba, dan haka ki rufa min baki kafin in zaneki sai kiyi kukan mai dalili."

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now