Page 19

96 7 0
                                        

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 19

               **** ****
Affan yana fitowa daga gidan Jalil kai tsaye gidansu ya wuce, ya daɗe suna hira da mahaifiyarsa, sai kusan agrib take sanar dashi tayi magana da babanshi akan yarinyar nan, amma dai bai bada goyon baya ba, ya dai ce za su yi magana.

"Bari nazo na tafi Hajiya, dan na san da anyi magrib zai shigo, kuma Jalil ya ce min zai zo gidana anjima, to kuma hira da Baba na san zan iya kaiwa tara, amma dai gobe idan Allah ya kaimu zan dawo"
"Allah ya nuna mana lafiya"
"Ka gaida min yaran"
"Za suji insha Allah"

Bai ƙarasa gida ba ya tsaya a wani masallaci nan ya yi sallah.
Yana fitowa ya ci karo da wata babbar mace da kuma budurwar a gaban motar shi a tsaye.

"Sannu Baba dan Allah zan ɗan ari motar"
"Yaro dan Allah ko za ka taimaka ka miƙa mu nan asibitin Nassarawa?"
Ɗan lumshe ido ya yi, ya sake kallonsu, nafarko bai sansu ba basu sanshi ba, na biyu zamani da babu wani tsaro, na uku kuma ya san yanzu Jalil zai ƙaraso, gashitafiyar gabaɗaya ta saɓa, shi da zai je Rijiyar Zaki mene zai mayar dashi asbitin Nassarawa"
"Baba bari na baku kuɗin Napep sai ku ƙarasa ko?"

"Dan Allah yaro ka taimaka ka kaimu, saboda tana da lurura ne kuma yanzu kafin ma a samu ɗan sahun aiki ne."
Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli matashiyar da take ta lumshe ido tana cije leɓe da alamun ciwo yana cinta daurewa kawai take.
"Shi kenan ku shiga muje"
Ya faɗa yana buɗe motar.

Suna shiga kuwa ta fara masa godiya, kafin daga bisani ta ɗauko waya ta kira number tare da karawa a kunne.

"Salamu alaikum"
Daga ɗayan ɓangaren aka amsa mata.
"Habiba gani nan na tafi kai Safiyya asibiti"
"Ciwon ne ya kuma tashi?"
Eh wallahi kin ganta nan tun safe take fama sai kawai naga gara na kaita asibitin da ɗan abinda ya ragemin"
"To wai shi Shamsu mene yake yi? Ya kuwa san bata da lafiya?"
"Ya sani mana, ai Allah ya isa tsakanina da bawan Allahn nan, yarinyar nan a gidanka ta samu larura amma kuma ka dawowa da iyayenta ita, saboda tsabar rashin imani"
"To wai ya saketa mana dole ne auren nasu"
"Taurin kai gare shi yaƙi sakinta, kuma wallahi zan gwada masa ni surukar zmani ce in har bai bata takarda ba"
"Gaskiya dai idan ta kama harkotu sai a makashi"
"Ki bari kawai, ni yanzu na wuce asibiti, yanda ake ciki zan kira in sanar daku"
"To shi kenan Allah ya bata lafiya"
"Amin ya Allah"

Tana kashewa ta ƙara dialing wata number duk abinda ake Affan yana ji dan wayar a hands free take sakata.
"Salamu alaikum Naja kina jina?"
"Yaya ina ji, ina wuni"
"Lafiya lau ya gida da yara"
"Yara lafiya lau, ya jikin Safiyya?"
"Jiki dai ya ƙara tashi, dan yanzu haka yau tun safe take zubar da jini, kai maza tsinannu ne, wai Shamsu baya da imani ko kaɗan ƙila so yake yarinyar nan ta mutu, danhska auren shi ko da kacaaa ɗaura sai an kunce"
"Shegen yaƙi ya bayar da takarda ko?"
"Eh wallahi yaƙi, wai yana son matarsa, dan ubansa yana sonta ya riƙa azabtar da ita, kai namiji, namiji hmmm"
"Yanzu ina Safiyya ɗin?"
"Gata nan zamu koma asibiti dan naga har idanunta sun fara canja kala"
"Wane asibiti?"
"Nassarawa"
"Gani nan zan taho yanzu kuwa"
"To shi kenan sai kin zo"
"Yawwa"

Tana kashe wayar ta kalli Affan ta ce "Yaro kayi haƙuri na manta ka mana halacci kuma kaji ina ta zagin maza"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Babu damuwa"
"Duk da haka na san za ka ji ba daɗi tunda nai jam'i, amma halin mazan ne sai su wallahi, yanzu yarinyar nan haka ta aure shi baya da komai ta zauna dashi, yanzu kuma gashi ciki ya fito mata a bayan mahaifa, wallahi yarinyar nan mu muka haɗa kuɗi aka samu aka mata aiki, kuma yanzu tana ta zubar da jini dan rashin imani ya dawo mana da ita gida, sannan kuma yaƙi ya bata takarda"

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now