Page 13

96 6 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 13

_Bayan wasu mintuna_

Tana zaune a ƙasa ta raɓe jikin bango tana goge hawaye, shi kuma yana zaune kan gadon hannunsa a haɓa ya rasa ma me zai yi.

"Kukan ya isa haka" Ya furta yana kallonta.

Kanta yana ƙasa sam ta kasa ɗagowa ta kalleshi.

"Ki goge hawayenki magana zamuyi"

Hannu ta saka tana goge hawayen, duk da wasu na zuba, da ƙyar ta samu ta tsayar da hawayenta.

"Ya ya sunanki?"
"Ablah"
"Ablah!" Ya maimaita sannan ya sake kallonta.
"Shekarunki nawa?"
"Sha biyu"
"What!" Ya furta yana miƙewa tsaye. "Yarinya ƙarama za ta kawo min" Ya dafe goshi kafin ya ƙaraso inda take ya saka kujerar madubi ya zauna, ita kuma da sauri ta ƙara matsawa.
"Ki kwantar da hankalinki Ablah babu abinda zan yi miki kin ji"
Kai ta gyaɗa sannan ta sauke ajiyar zuciya.
"Amma ina iyayenki?"
"Ammina ta rasu" Ta faɗa tana zubar da hawaye.
"Allah sarki no wonder ashe Mama bata raye na san da ba zata yarda a kawo ki nan ba ko da zaku ci ƙasa." Bata ce komai ba, kuma har lokacin bata ɗago ta kalleshi ba.

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya sake faɗin "Yanzu a gurin wa kike zaune? Kuma ina ne gidanku?"
"Ammina a gidan karuwai take, data mutu Aunty Sarah ke kula dani, shi ne yanzu ta kaini gidan Magajiya"
"Wace Magajiya?"
"Ita ce shugabar gidan karuwai" Ta furta a sanyaye, duk da dai bata da wani wayo dan da tana dashi bama zata zauna tana wannan bayanan babu sirri ba.

"A gidan karuwai aka haifeki kenan?"
Kai ta gyaɗa masa, sannan ta ce "Bana son zama a gidan ina faɗawa Ammi amma sai dai ta dokeni, da bata da lafiya babu wanda ya kula da ita har ta mutu"
"Kina zuwa makaranta?"
"Eh ina zuwa amma tunda Ammi ta mutu ban sake zuwa ba saboda bani da lafiya"
"Wane aji kike?"
"Jss2, a islamiyya kuma izufinmu ashirin"
"To yanzu dai kin ɗauke ni a matsayin Yaya?"
"Za ka kaini gun dangina? Bana son zaman gidan karuwai"

"Ablah bana son ki riƙa ambatar gidan karuwan nan kinji, dan Allah ki daina, kuma kowa ya tambayeki kada ki ƙara cewa a gidan karuwai kike kinji?"
Kai ta gyaɗa alamar to.
"Yanzu dai naga har tara tayi, kina jin yunwa?"
"Eh inaji kuma ban yi sallah ko magriba ban yi ba"
"To ga toilet ki shiga sai kiyi alwallah" Shiru tayi ta ƙura masa ido.
"Ko akwai wani abin?"
"Bana iya alwallah da kaina" Ta furta tana kallonsa da manyan idanunta.
"Tashi muje"

Shi ya ɗoro mata alwallah sannan ya yana mata mayafin ta tayar da sallah shi kuma ya fita.

Bayan ya yi mata order ya sanar masu su kai mata sai ya koma farfajiyar hotel ya shiga motarsa ya rufe. Kujera ya kwantar tare janyo waya, Hidaya ya kira har tayi ringing ta katse bata ɗaga, kamar kar ya sake kira sai kuma ya sake a karo na biyu, shi ma sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga.

"Sai yanzu ka ga damar kirana Affan" Shi ne abinda ta faɗa lokacin da ta ɗaga.

"Kiyi haƙuri ayyuka ne suka min yawa"

Gajeran tsaki taja sannan ta ce "Bacci nake ji sai da safe"
"Yar..." Ji ya yi ta katse, ya kalli wayar sannan ya sauke ajiyar zuciya.

*Affan Kabir Ahmad*

Tun tasowarsa ya taso ne da hazaƙa, domin zai yi wuya a yi jarabawa ya kasa zuwa na ɗaya ko na biyu, hakan ya saka iyayenshi jajircewa a kansa, duk da ba wasu masu kuɗi bane, mahaifinsa ƙaramin malami ne a makaranta secondary wanda yana ɗaukar ɗaliban aji ɗaya zuwa uku wato jss1 to jss3 Hausa Language, yayinda mahaifiyarsa ta kasance full house wife, dan daga secondary school bata ƙara gaba ba.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now