*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 20
Zama tayi a kujerar da take facing ɗin tashi, "Abban Yara gani, Allah yasa dai lafiya?"
"Lafiya lau, ina Ablah ne?"
"Tana can ɗakinta"
"Ban ji motsinta bane"
"Ai bata shigowa nan idan bada dalili ba, kullum tana can, idan ta fito ma sai dai ta zauna a tsakar gida."
Kai kawai a girgiza, ta kalƙeshi ta ce "Ya naga kana girgiza kai"
"Sai nake ganin kamar ba Nabihar dana sani bace, kamar canja ki akai"Murmushi tayi kafin ta ce "Abban Yara kenan, ni dai na rasa dalilinka na faɗin haka"
"Mamin Yara Ablah yarinya ce mai larura bai kamata a riƙs barinta ita kaɗai ba"
Jin haka ya saka annurin fuskarta disashewa, ranta ɓace ta ce "Ita fa ba kurma bace, ba gurguwa ba, duk da bata gani amma ai tana da glass ɗin da yake taimaka mata wajen ganin komai tar."
"Eh duk da haka a shekarunta bai kamata ace sn ware mata ɗaki a can gefe ita kaɗai ba, mutane sai su zagemu"
"Zagin mutane ni ba zai dameni ba, kuma kada ka manta yarinyar nan a gidan karuwai ta tashi,wataƙila Zeenat na barinta ita kaɗai ta kwana a ɗaki ma, ni ban ma gama yarda da tarbiyyarta ba tukun, dan haka ba zan gwamatsata cikin 'ya'yana ta ɓata min su, sannan kuma yaran nan gabaɗaya tsoronta suke taya kake tunanin zan kaeota ɗakin su, ba zai yuwu ba"Kallonta kawai yake tunda ta fara magana har ta kai aya, sannan ya ce "Ni dai na yi shawara ban sani ba ko za ki so ta"
"Shawarar me?"
"Zan mayar da Ablah makaranta arabi da boko"
"Makaranta kuma?"
"Eh saboda ta rage zaman kaɗaice"Murmushi kawai tayi, wanda na takaici ne kafin ta ce "Ka san me?"
"Sai kin faɗa"
"Dama a raina naji ina so na mayar da ita islamiyya saboda mahaifiyarta jahilci ne ya kaita ƙasa, har ta shiga hurumin aljanu, to ni ba zan hanata ilmi na addini ba a matsayina na musulma, amma maganar karatun boko Ablah ba zatayi ba, tunda ta samu primary ɗin ma ya isa"Mamaki sosai ya cikashi har ma ya rasa ta inda zai fara magana, wai yarinyar da ta kasance ɗiyar 'yar uwarta wadda suka kasance uwa ɗaya uba ɗaya amma kuma take mata wannan baƙar izayar.
"Nabiha akan me ita ba za tayi ba, bayan su Hamdiyya duk suna zuwa meyasa?"
"Saboda nima Zeenat ta hanani karatu, aka biya mata ita tayi domin mu ƙananun ta tallafa mana, amma sai ta shiga harkar bin maza, haka 'yan uwana suka mutu na rage ni kaɗai, kuma haka ban yi karatun ba tun daga jss3 ban cigaba ba, kuma gashi ina rayuwa ba abinda na rasa, dan haka itama ba za tayi ba"Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin "Wato idan na fahimce ki Nabiha, kallon Zeenat kike yiwa Ablah, kuma kina son duk haushin Zeenat da kike ji ki sauke shi a kanta, amma ina so ki sani, ramuwa ba alkhairi bace, ki rama sharri da alkhairi sai ki ga daidai a rayuwarki, bare na tabbatar ita kanta Zeenat da za ta dawo yanzu ba zata maimaita kuskuren data aikata ba, haba Mamin Yara, yanzu ita ƙaramar yarinya ce bata san komai ba kuma ko babu komai Zeenat jininki ce, hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka zubar"
"Sai dai idan bai dameka da azaba ba, amma idan ya hanaka barci tuni zaka biya a yanke"
"Ni dai kiyi haƙuri ki manta abinda Zeenat ta miki saboda ita ta-ta ta ƙare, babu abinda take buƙata face addu'a dan Allah ki rungumi ɗiyarta, ki mayar da ita 'ya Nabiha"
"Bana ƙaunarta ka barni a haka kawai, baka san yanda nake ji akan mahaifiyarta bane"
"Amma ai bata raye"
"Duk da bata raye ɗin, ai wannan jininta ce, kuma jini ba wasa ba"
"Ki faɗi alkhairi akan yarinyar nan, idan ta tashi taji kina faɗar haka ba zata taɓa jindaɗi ba"
"To karta ji mana, ni ina ruwana"
"Shi kenan, zuwa next week zamu koma sabon gidan"
"Wai da gaske?"
"Eh an gama komai sai tarewa ya rage"
"Wow mun zama 'yan lamido crescent kenan, gidan ya bala'in burgeni"
"Ai dama abinda zai burge ki nake so, abinda kuma zai faranta miki rai"
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Tiểu thuyết Lịch sửƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...