*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 21
Sai kuma ta dai-daita nutsuwarta ta ce "Oh ni za ki rainawa hankali ko? Barikin za ki min ne, to ni bariki a cikinta na taso kuma ni uwarki ce a bariki ba zaki layance min ba"
Murmushi Aziza tayi tare da faɗin "Magajiya kenan, ai ni bana ƙwai na sai da zakara, bari na nuna miki shaida"
Wayarta ta buɗe ta kunna mata voice recording da tayi musu. Sai daya ƙare tas sannan ta ce "Idan kin so zan rufa miki asiri idan kuma baki so ba zan tona ta yadda kina ganin gidan nan amma zai gagareki shigowa daga ke har 'yan korenki"
"Yanzu me kike buƙata?"
Dariya ta ɓaɓɓaka sannan ta ce "Yanzu kika yi magana, amma da kina son kiyi min ta 'yan bariki, ai ko da ke uwata ce a bariki karki manta ance makoyi fidda ma'iyi na riga na gana gogewa"
"Yanzu naji duk ba wannan surutun nake son ji ba, me kike buƙata, dan na san tunda kika naɗi murya ba banza ba"
"Yawwa abu biyu ne kacal babu yawa"
"Ina ji"
"Zaɓi biyu ne, ko dai ki bani miliyan biyar, ko kuma ki bani miliyan biyu amma da sharaɗin ba za ki ƙara karɓar kuɗin ɗakina ba, zaɓi ya rage naki"
"Kin kuwa san mene miliyan? Ko dan ba za ki sani ba dan ni na tabbatar barikinki bai taɓa haɗaki da ko wanda zai baki dubu ɗari biyu a lokaci guda"
"Ya isa haka Magajiya" Aziza ta faɗa tana miƙewa tsaye.Taku biyu tayi ta dɗn tsaya "Ni dai na faɗa miki abinda nake buƙata, babu ruwanki da na taɓa riƙe manyan kuɗi ko ban taɓa ba, sannan idan kim ga dama za ki iya sakawa a kasheni ko nima a watsa min acid, sai dai zan miki albishir da cewa na bayar da wannan recording ɗin ga wata ƙawata dake wajen gidan nan, wadda bata ma sanku ba, na kuma faɗa mata kar ta saurara, amma daga zarar taga wani abu ya sameni kawai ta watsa kowa ya san abinda ke faruwa."
"Me kika ɗauke ni ne? Itama da nayi mata haka laifi tayi min shiyasa na koya mata hankali"
"Nima ai laifin nayi miki tunda na buƙaci kuɗin da na san kin fi ƙarfinsu amma kina nuna kamar ba za ki bani ba"
"To wai me kike nufi da ba zan baki ba? Ni ɗin ma har yanzu ban samu ba, ko da kika ji muna maganar ai cewa muka yi idan ya bayar"
"To yanzu nima sai ku saka ni a cikin naku lissafin idan kuma ba haka ba asirinku ne zan tona"
Shiru Magajiya tayi, tana ƙara jin haushin Saratu da duk a sanadinta ne aka raina ta, dan ita ta fara nuna cewa bata isa komai a wajenta ba.
"Shi kenan za ayi yadda kike so, amma dan Allah ki goge abin nan, saboda tsaro"
"A yanzu kam babu wani dalili da zai saka na goge, amma daga zarar naji dumus, to zan goge mana"
"Shi kenan"
Taɓe baki kawai Aziza tayi.********
Madubin dake hannunta ta raɗa da ƙasa, sai kuma ta fashe da kuka.
Shigowar Maryam ɗakin kenan ta tarar da madubin a tarwatse a ƙasa.Ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙarasawa gaban Saratu, ta ajje mata ledar a gabanta, sannan ta kalli madubin.
"Sarah dan Allah kiyi haƙuri ki rungumi kaddararki"
"Maryam bani bace, wannan bani bace, abin tsoro Maryam, taya za a ce na koma haka?" Ta faɗa cikin matsanancin kuka.
"Ƙaddarar ki ce a haka Sarah kiyi haƙuri ki rarrashi zuciyarki, kin ga haka kika fasa madubinki babba yanzu kuma kin fasa wannan, dan Allah kiyi haƙuri."Maryam...!" Ta furta da murya kuka
"Na'am"
"Shi kenan yanzu na zama haka? Shi kenan bani babu ƙara samun wasu kuɗaɗen? Maryam waye zai ɗaukeni a haka?"
"Sarah ba za a rasa ba a cikin mazan da kike dasu"
"Tare dake muka je wajen Alhajin Nasir ya yi mana korar kare, to ina kike so naje yanzu?"
"Ai na san ba shi ne kawai wanda yake da kuɗi a mutanen da kike mu'amala dasu ba, ki tunano wani ni ba zan kasa rakaki ba"

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Fiction HistoriqueƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...