*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 2
Ita kanta Malama Shamsiyya ta kasa motsawa daga inda take tsaye. Saratu ce taje ta ruƙo Ablah wadda dama a dalilinta ne suka samu saɓani da Zeenat har ta kai su ga yin gaba, saboda Saratun bata son abinda Zeenat ke yiwa Ablah, sai kace ba itace ta kawo ta duniya ba.
"Kiyi haƙuri Ablah" Shi ne abinda Saratu ta faɗa tana kuka, wanda kaf gidan karuwan ita kaɗai tayi wa Zeenat kuka a matsayinta na wadda bariki ce ta haɗasu.
"Aunty Sarah dan Allah ki faɗa masu kar su binne Amminah, ni na san bata mutu ba"
"Kiyi haƙuri Ablah addu'a za kiyi mata"
"Anyi wankan gawa ne?" Malama Shamsiyya tayi tambayar.
"Ai nan babu wanda ya san yadda ake, mu dai mun wanketa da sabulu da ruwa sai muka feshe likkafanin da turare"
Kai Malama ta girgiza tare da ƙara jin tausayin wannan bayin Allah da mutuwa sam bata zama darasi a garesu ba, dan yadda taga wasu sun cigaba da sha'aninsu sam abin bai wani damesu ba.
"Ƙaryar banza, shishshigi da ƙwala kai a faranti" Ashanty ta furta tana kallon Saratu sannan ta wuce.
Malaman makarantar su Ablah sun yi kara domin kuwa Malama Shamsiyya ita tayiwa Zeenat wankan gawa, su kuma sauran Malaman maza suka haɗu da wasu daga cikin 'yan unguwa suka roƙesu aka sallaceta sannan aka kaita zuwa kushewarta.
**** **** ****
"Ablah na roƙeki kici abinci kuka ba magani bane, kin san kina da ulcer dai ko?" Saratu ta faɗa da robar takeaway a hannunta tana roƙar Ablah wadda ta dawo ɗakinta da zama tun ranar da Zeenat ta rasu.
"Aunty Sarah shi ke nan yanzu ba zan sake ganin Ammi ba? Kuma babu wanda ya damu da mutuwarta sai ke kaɗai Aunty"
Hannu Saratu ta saka ta goge hawaye, yau kwana huɗu da rasuwar amma kullum idan taga Ablah na kuka sai taji duk ta sare, tabbas bata so rayuwar Zeenat ta ƙare a haka ba, musamman a yadda ta bata labarinta.
*Labarin Zeenat*
Gudu take tamkar taci ƙafar kare, sai dai kuma duk wannan gudun bai hana idan ta waiga taga wanda ke bin ta yana gab da cimmata, duk iya ƙoƙarinta na son ganin ta kuɓuta daga sharrin sa, sai dai hakan ya ci tura, kasancewar ruwan sama daya ɓalle lokaci guda har ma ta daina ganin gabanta sosai, duk da cewar dajin da take ciki baya da yawan bishiyu amma a halin da ake ciki wanda ake maka ruwa kamar da bakin kwarya shi ya yi sanadiyyar tsagaita gudun nata, ba wai dan ta daina ganin gabanta ba, a'a saboda ƙasan da take takawa ta tabbatar da taɓo ne, dan kuwa idan ta saka kafin ta cire abu ne da yake mata matuƙar wuya, ɗan juyawa tayi dan ta tabbatar da mai bin nata yana tare da ita har a lokacin ko kuwa ya gaji ya tsaya, sai dai tana juyawa taga yana ƙoƙarin cafko fuskarta, da sauri ta koma kallon gabanta sai dai bata ankara ba sai ganinta tayi gaba ɗaya ta faɗa wani wawakeken rami da bama ta san iya zurfinsa ba, sai dai tayi imani cewa wannan rami baya da maraba da rijiya ko wani tafkeken kogo.
Jin ana ɗan bugun ƙafarta ya saka ta tashi daga mummunan mafarkin da take, wanda har ta manta cewa yanzu ba mafarki bane, dan tana miƙewa tayi ƙoƙarin bawa rigarta iska, sai dai kuma Umma ta riƙota tana faɗin,
"Ni ce ki nutsu"
Kallonta tayi sai kuma ta fashe da kuka "Umma tsoro nake, na shiga uku" Ta faɗa tana rungumeta.
![](https://img.wattpad.com/cover/351344300-288-k542301.jpg)
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...