*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 43
"Subhanallahi, Ablah lafiya?" Ya furta yana tsugunnawa gabanta, sannan ya kalli Saratu. "Baiwar Allah lafiya kuwa?"
Bata masa magana ba kawai ta saka hannu ta ɗago Ablah. "Muje gida"
"A'a" Ta furta cikin kuka.
"To ina zaku je?"
Kallon Saratu tayi sannan ta kalleshi.*_Few Minutes Later_*
Suna zaune kowa ya yi shiru, gwiwar hannunta ta saka tana share hawaye bayan ta gama bashi labarin duk abubuwan da suka faru.
"Kenan itace wadda ta kawo ki gidan Alhaji Mustapha?"
Kai ta gyaɗa alamar eh.
"Allah sarki sannu baiwar Allah mun gode sosai Allah ya saka miki da mafificin alkhairi.
"Amin" Itama Saratun ta amsa tana zubar da hawaye.Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin Affan ya ce "Amma duk da haka bai kamata ku taho ba, Ablah ba a fushi da mahaifi."
"Uncle ba zan iya barin Aunty Sarah ba, tayi min abinda ba zan iya nesa da ita ba, kuma na santa kafin in san Abbana, ita tasha wahalata ba shi ba, ita ta fara gina ni tun daga kan arabi har zuwa boko, da ace zan iya ɗaye fuskata na bata da wallahi zan bata ni na zauna a hakan"
"Shi Abban naki ya san da wannan labarin?"
Kai ta girgiza alamar a'a, sannan ta ƙara da cewa "Har yanzu ban bashi labarin komai ba, bana son na faɗa masa cewar a gidan karuwai aka haifeni"
"Dole ya san komai Ablah, shi ɗin ai mahaifi ne, kuma ina tunanin shi ne dalilin da ya saka ya yi mata magana mara daɗi saboda bai san wacece ita da alaqarku ba, amma na san da ba zai guji wadda ta mayar da ɗiyarshi mutum ba."
Shiru tayi bata ce komai ba.
"Kiyi haƙuri ki tashi muje na mayar daku, domin na tabbatar duk inda yake hankalinsa a tashe yake, ita kuma Auntynki na miki alqawarin zan biya kuɗi a fitar da ita waje dan a gyara mata fuskarta."Da hawaye a idanunta amma kallonshi take tana murmushi.
"Uncle da gaske kake?"
"Ablah ba zanyi ƙarya da girmana kawai dan kiji daɗi"
Gwiwoyinta ta kai ƙasa tare da faɗin "Uncle na gode, ka biyani Uncle Allah ya saka maka da alkhairi"
"Amin Ablah""Nagode sosai Allah ya biyaka" Saratu ta faɗa cikin kuka.
"Amin karki damu. Yanzu dai ku tashi na mayar daku gida ko?"
Miƙewa tayi jikinta a sanyaye, Saratu ma ta miƙe suka fita.**** **** ****
Suna zaune kan kujerun da suka yiwa parlourn ƙawanya. Fahad ya kalleshi ya ce "Ai na faɗa maka ba lallai mu ganta ba, ba fa ɓata tayi ba tafiya tayi da kanta"
"Amma kana nufin waccan almajirar ta fi ni muhimmanci a gurin Ablah?"
"Irfan, dole ne mu bi komai a hankali, saboda ka ga ita waccan ɗin bamu san alaqarsu ba, na faɗa maka mun fito daga restaurant fa tana cikin almajirai amma haka Ablah ta rungumeta, ai a haka yanzu tana ganuwa akan farkon haɗuwarmu, da ace kaine kenan ba zama iya bari ta shiga motarka a wannan lokacin ba"
"Amma ko wacece ai bai kamata har ta guji mahaifinta a kan wata ba, tunda ai ba ita ta kawota duniya"
"Irfan baka san alaqar dake tsakaninsu ba, yarinyar nan tana samun matsi daga Nabiha ma data kasance ƙanwar mahaifiyarta, tunda kuwa ka ga ta rungumi wannan matar tabbas akwai alkhairin data mata."
"Gaskiya zan ɗauki Ablah kawai mu tafi, ba lallai na iya zaman Nigeria ba, ma riƙa zuwa lokaci zuwa lokaci"
"Dama fa ni na san sai ka faɗi haka, n san yanzu ba lallai ka iya zaman ƙasarnan ba."Sallamar su Ablah ce ta saka su yin shiru, ganinsu kuma da Affan ya saka suka miƙe tsaye. Ƙarasawa ya yi ya miƙa musu hannu suka yi musabaha. Juyawa ya yi ya kalli Ablah ta sauke kanta ƙasa da sauri, fuskarnan a haɗe sosai.
"Bismillah" Fahad ya faɗa yana nuna masa kujera. Affan da Fahad har suka zauna amma Irfan bai zauna ba. Ya ƙurawa Ablah ido.
"Ablah" Affan ya kira sunan cikin raɗa, ɗagowa tayi ta kalleshi, ya mata sign da ka, a sanyaye ta nufi gurin Irfan, tana ƙoƙarin kai gwiwoyinta ƙasa ya yi saurin ɗagota tare da rungumeta, wani sanyi yaji ya ratsa shi gashi yau rungume da jininsa 'yar daya haifa.
"Abba kayi haƙuri" Ta furta tare da fashewa da kuka.
"Ya isa haka, na haƙura kin ji, kema kiyi haƙuri ban jidaɗin abinda nayi ba ki yafe min"
Hannu ya saka ya share mata hawaye.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...