*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 30
Shiru Affan ya yi ya rasa abinda zai ce ma. "Amma sai nake ganin kamar ba hujja ace dan ina da mata ka hanani auren Ablah"
"Ba wai dan kana da mata bane, hujjata itace Ablah ba zata iya kishi ba, saboda bata da lafiya kai kanka ka san matsalarta.
"Na sani amma jira da nemanta nayi na tsawon shekaru bakwai, na daɗe ina sonta tun tana ƙaramar yarinya"
"Yanzu dai abinda za ai shi ne, ka bari nayi magana da uwar riƙonta da ita kanta Ablah, duk abinda muka tattauna zaka ji"
"To shi kenan, amma dan Allah kar matata ta zama hujja, saboda ba gida ɗaya zan ajiye su ba"
"Shi kenan, zan saka maka number ɗina tunda kace kayi missing"
Wayarsa ya karɓa ya saka masa number sannan ya ce "Bari na kira maka ita ku gaisa ko?"
"To nagode sosai"Yana fita Jalil ya kalli Affan ya ce "Ni fa gani nake ba zasu baka ita ba, bayan suma daga sama suka sameta"
"Shi ne, yarinyar har sai da tayi wayo ta zama mutum sannan suka sameta, kuma abinda zai baka mamaki shi da yake zaƙewa ba shi ne ɗan uwan nata ba, mijin ƙanwar mahaifiyarta ne"
"Au wai da shi ne alaqar tasu amma yake faɗin wai ba zai bayar da ita ba, to ai ko aure ta tashi ba shi ne waliyyinta ba"
"Eh mana kawai gadara ce"
Shigowar Ablah ce ta saka suka yi shiru. Kallo ɗaya za kai mata ka gane tana da damuwa kuma bata cikin yanyi mai daɗi."Ina yini" Shi ne abinda ta faɗa tare da zama kan kujerar, tana sanye da abaya maroon, tayi rolling mayafin ta manna pin, Abayar ta rufe hannun ta yadda ba a ganosu. Tunda ta shigo Jalil ke jinjina kyau irin nata ga wani sassanyan ƙamshi dake tashi, da yake Ablah macece mai son ƙamshi shiyasa kabbasar da take har ta gama haɗe jikinta.
"Ablah"
"Na'am" Ta furta kanta a ƙasa.
"Ya kike ya jikin naki"
"Alhamdulillah na warware"
"Allah ya ƙara miki lafiya"
"Amin ya rabbi"Shiru ne ya biyo baya kafin ya sake cewa "Wannan abokina ne, ku san zan iya cewa amini ma, sunanshi Jalil"
"Allah sarki" Ta furta a sanyaye.
"Jalil ga Ablah da nake yawan baka labari tun tana ƙarama muka rabu"
"Masha Allah shiyasa ka ruɗe ashe haka take kamar baturiya ko ince 'yr india"
Murmushi kawai tayi kanta a ƙasa dan bata iya zolaya ba, bata taso da wani wanda zai tsokaneta bare har ta iya.Affan ne ya ce "To ya isa haka, ni ne kaɗai ya dace na yabi kayata. Ablah ya karatu, yanzu a wane mataki kike?"
"Tun bayan dana gama secondary school ban cigaba da karatu ba, sai dai har yanzu ina zuwa islamiyya"
"Amma meyasa kika dakata da karatun bokon?"
"Kawai saboda larurar da nake da ita, a wasu lokutan na kan fuskanci ƙalubale daga ɗalibai ko mutanen gari ma, saboda kaga ita makaranta ba zan saka hijab haka har ƙasa ba, ko da hijab ya ɗan rufe hanayena akwai masu tsokanta wasu ma har ƙomarin fuzgewa suke, ga kuma matsalar idanuna shiyasa kawai na haƙura"
"Amma ban so kika tsaya da karatun ba domin yana da amfani"
"Na kasa jurewa ne, gani nake kamar na bambanta da sauran mutane"
"Ko kaɗan, kema kamar kowa kike wasu ma kin fisu, kuma hannunki ai haka Allah yake son ya ganki kuma hakan bai ɓoye kyawu da baiwar da Allah ya miki ba"
"Kai ne ka fahimci haka Uncle amma ni na san matsalar da nake fuskanta a rayuwata"
"Hakan ne ya saka kikayi yunƙurin kashe kanki?"
Murmushi tayi sai kuma ta fashe da kuka.
Kallon Jalil ya yi, sannan ya miƙe ya ƙarasa inda take.
"Babu wanda yake sona Yayana, Abba ne kaɗai ke ƙaunata ko a gidan nan, tunda na dawo nake fuskantar haka har zuwa yanzu, Uncle taya ba zan sha abinda zan mutu ba bayan mahaifiyata na ƙasa amma bata daina shan zagi da aibatawa ba, ba zan manta lokacin da kake cewa indai faɗin na taso a gidan karuwai amma a gidan nan gani ake kamar nayi karuwancin ma, Abba ne kaɗai ke nuna min kulawa"
"Abba kiyi haƙuri kamar yadda na faɗa zan share miki hawaye kuma zan zamo gatanki, fatana dai idan Abba ya tambayeki a game dani ki amince ki aure ni."
Shashsheƙa kawai take bata ce komai ba.
"Dan Allah ki share hawayenki kin ji"

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
HistoryczneƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...